Baibul a cikin shekara guda Afrilu 7Yoshuwa 3:1-171. Kashegari Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Shittim suka nufi Urdun inda suka sauka kafin su haye.2. Bayan kwana uku sai shugabannin suka zazzaga sansani, suna3. ba da umarni ga mutane, suna cewa, “Lokacin da kuka ga akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku, da firistoci waɗanda su ne Lawiyawa, suna ɗauke da shi, sai ku tashi daga inda kuke, ku bi shi.4. A ta haka za ku san inda za ku bi, gama ba ku taɓa bin hanyar ba. Sai dai ku ɗan ba da rata wajen yadi ɗari tara tsakaninku da akwatin alkawari, kada ku kusace shi.”5. Yoshuwa ya ce wa mutane, “Ku tsarkake kanku, gama gobe Ubangiji zai yi abubuwan al’ajabi a cikinku.”6. Yoshuwa ya ce wa firistoci, “Ku ɗauki akwatin alkawari ku sha gaba.” Sai suka ɗauki akwatin alkawari suka wuce gaban sauran jama’a.7. Ubangiji kuwa ya ce wa Yoshuwa, “Yau, zan fara ɗaukaka ka a gaban Isra’ilawa duka don su sani cewa ina tare da kai kamar yadda na kasance tare da Musa.8. Ka ce wa firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawari, ‘Sa’ad da kuka kai bakin Urdun, ku shiga cikin ruwan ku tsaya.’ ”9. Yoshuwa ya ce wa Isra’ilawa, “Ku zo nan ku ji maganar Ubangiji Allahnku.10. Ta haka ne za ku san cewa Allah mai rai yana tare da ku, kuma ba shakka a gabanku za ku gani zai kore Kan’aniyawa, Hittiyawa, Hiwiyawa, Ferizziyawa, Girgashiyawa, Amoriyawa da Yebusiyawa.11. Ku duba, akwatin alkawarin Ubangiji na dukan duniya zai yi gaba cikin Urdun kafin ku.12. Yanzu sai ku zaɓi mutum goma sha biyu daga kabilan Isra’ila, ɗaya daga kowace kabila.13. Kuma da firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji, Ubangiji dukan duniya, sun sa ƙafa cikin ruwan kogin Urdun, ruwan da yake gudu a rafin zai tsaya cik yă taru a wuri ɗaya.”14. Saboda haka sa’ad da mutanen suka tashi don su ƙetare Urdun, firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawarin suka sha gaba.15. Da kaka Urdun yakan cika makil da ruwa. Duk da haka da zarar firistoci masu ɗauke da akwatin alkawari suka tsoma ƙafafunsu a gefen ruwa,16. sai ruwan da yake gangarowa ya tsaya, ya tattaru a wuri ɗaya ya yi tudu daga nan har zuwa wani garin da ake kira Adam kusa da Zaretan, ruwan da yake gangarowa zuwa Tekun Araba (Tekun Gishiri) kuma ya yanke gaba ɗaya. Sai mutane suka ƙetare kusa da Yeriko.17. Firistocin kuwa da suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya daram a kan busasshiyar ƙasa a tsakiyar Urdun a lokacin da Isra’ilawa suka ƙetarewa, har sai da dukan mutane suka gama ƙetarewa.Yoshuwa 4:1-241. Da al’umma gaba ɗaya suka ƙetare Urdun, Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,2. “Ka zaɓi mutum goma sha biyu daga cikin mutane, ɗaya daga kowace kabila,3. ka ce musu kowa yă ɗauki dutse ɗaya daga tsakiyar Urdun daidai inda firistoci suka tsaya, ku kai su, ku ajiye a inda za ku sauka yau.”4. Sai Yoshuwa ya kira mutum goma sha biyu da ya zaɓa daga cikin Isra’ilawa, ɗaya daga kowace kabila5. ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,6. yă zama muku alama. Nan gaba in yaranku suka tambaye ku suka ce, ‘Mece ce ma’anar kasancewar duwatsun nan a nan?’7. Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”8. Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.9. Yoshuwa ya ɗora duwatsu goma sha biyun a tsakiyar Urdun daidai inda firistoci waɗanda suke ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji suka tsaya. Suna nan a can har wa yau.10. Firistocin da suke ɗauke da akwatin alkawari suka tsaya a tsakiyar Urdun, har aka gama dukan abin da Ubangiji ya umarci Yoshuwa yă gaya wa mutane, kamar yadda Musa ya ce Yoshuwa yă yi. Mutanen suka wuce da sauri.11. Sai da dukan mutanen suka wuce sa’an nan akwatin alkawari da firistoci suka sha gaba.12. Mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse suka ƙetare da shirin yaƙi, suka wuce gaban Isra’ila kamar yadda Musa ya ce su yi.13. Wajen mutum dubu arba’in shirye domin yaƙi, suka wuce a gaban Ubangiji zuwa filayen Yeriko.14. A ranan nan Ubangiji ya ɗaukaka Yoshuwa a gaban Isra’ilawa; suka kuma ba shi girma dukan kwanakin ransa, kamar yadda suka girmama Musa.15. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa,16. “Ka umarci firistocin da suke ɗauke da akwatin Shaida su fito daga cikin Urdun.”17. Sai Yoshuwa ya umarci firistoci ya ce, “Ku fito daga cikin Urdun.”18. Firistocin kuwa suka fito daga kogin ɗauke da akwatin alkawarin Ubangiji. Nan da nan da ƙafafunsu suka taɓa busasshiyar ƙasa, sai ruwan Urdun ya gangaro ya cika kogin kamar yadda yake a dā.19. A rana ta goma ga wata na farko, mutane suka haura daga Urdun suka sauka a Gilgal a gabashin iyakar Yeriko.20. Sai Yoshuwa ya kafa duwatsu goma sha biyun nan da suka ɗauko daga Urdun.21. Ya ce wa Isra’ilawa, “Nan gaba in yaranku suka tambayi iyayensu suka ce, ‘Mece ce ma’anar waɗannan duwatsun?’22. Ku ce musu, ‘Isra’ilawa sun ƙetare kogin Urdun a kan busasshiyar ƙasa.’23. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruwan Urdun ya yanke a gabanku, har sai da kuka gama wucewa, kamar yadda ya yi a Jan Teku, a lokacin da ya busar da shi a gabanmu har sai da muka gama wucewa.24. Ya yi wannan ne domin dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji mai iko ne, domin kuma ku zama masu tsoron Ubangiji Allahnku.”Zabura 42:1-51. Kamar yadda barewa take marmarin ruwan rafuffuka, haka raina yake marmarinka, ya Allah.2. Raina yana ƙishin Allah, Allah mai rai. Yaushe zan tafi in sadu da Allah ne?3. Hawayena ne sun zama abincina dare da rana, yayinda mutane suke ce da ni dukan yini, “Ina Allahnka ɗin?”4. Waɗannan abubuwa ne nakan tuna sa’ad da nake faɗin abin da yake a raina, yadda dā nakan tafi tare da taron jama’a, ina bishe su a jere zuwa gidan Allah, da sowa ta farin ciki da kuma godiya a cikin taron biki.5. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna.Karin Magana 13:17-1817. Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.18. Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.Luka 9:1-171. Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka.2. Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.3. Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu.4. Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin.5. In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”6. Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.7. Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu,8. waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi.9. Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.10. Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida.11. Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.12. Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.”13. Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.” Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.”14. Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar. Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.”15. Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna.16. Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen.17. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.