Baibul a cikin shekara guda Mayu 101 Samaʼila 22:1-231. Dawuda ya bar Gat, ya tsere zuwa kogon Adullam. Da ’yan’uwansa da kuma iyalan mahaifinsa suka ji labari, sai suka tafi can wurinsa.2. Dukan mutanen da suke cikin wahala, da waɗanda ake binsu bashi, da masu damuwoyi, suka tattaru a wurin Dawuda. Shi kuwa ya zama shugabansu. Yawansu ya kai ɗari huɗu.3. Daga can Dawuda ya tafi Mizfa a Mowab. Ya ce wa sarkin Mowab, “Za ka yarda mahaifina da mahaifiyata su zo su zauna a wurinka kafin in san abin da Allah zai yi da ni?”4. Saboda haka ya bar su a wurin sarkin Mowab, suka zauna da shi duk tsawon lokacin da Dawuda yake ta ɓuya a kogwannin duwatsu.5. Amma annabin nan Gad ya ce wa Dawuda, “Kada ka zauna a nan, maza ka tashi ka shiga ƙasar Yahuda”. Sai Dawuda ya tashi ya tafi jejin Heret.6. Sai Shawulu ya sami labari cewa an ga Dawuda da mutanensa. Shawulu kuwa yana zaune da māshinsa kusa a ƙarƙashin itacen tsamiya a tudun Gibeya, tare da dukan ma’aikatansa kewaye da shi.7. Ya ce musu, “Mutanen Benyamin, ku saurara; ɗan Yesse zai iya ba dukanku filaye da gonakin inabi ne? Zai ba dukanku shugabanci na dubbai ko shugabanci na ɗari-ɗari?8. Abin da ya sa dukanku kuka gama baki a kaina? Ba wanda ya gaya mini lokacin da ɗana ya yi yarjejjeniya da ɗan Yesse, ba wanda ya kulla da ni, ko ya gaya mini cewa ɗana ya sa bawana yă tayar mini, yana fakona kamar yadda yake a yau.”9. Amma Doyeg mutumin Edom da yake tsaye tare da fadawan Shawulu ya ce, “Na ga ɗan Yesse ya zo wurin Ahimelek ɗan Ahitub a Nob.10. Ahimelek ya roƙi Ubangiji saboda shi, ya kuma ba shi guzuri da takobin Goliyat Bafilistin.”11. Sai sarki ya aika aka kira masa Ahimelek firist ɗan Ahitub da dukan iyalin mahaifinsa. Dukansu suka zo wurin sarki.12. Shawulu ya ce, “Ka saurara yanzu, ɗan Ahitub.” Ya amsa ya ce, “Ina saurara, ranka yă daɗe.”13. Shawulu ya ce masa, “Don me ka gama baki da ɗan Yesse a kaina har ka ba shi burodi da takobin (Goliyat), ka kuma roƙi Allah don yă tayar mini, yă kuma yi fakona kamar yadda yake yi yau?”14. Ahimelek ya ce wa sarki, “A cikin bayinka duka, wa ke da aminci iri na Dawuda, surukin sarki, shugaban jarumanka wanda ake girmamawa da gaske a gidanka?15. A wannan rana ce da na fara roƙon Allah saboda shi? Kada sarki yă zargi bawansa ko wani daga iyalin mahaifinsa, gama bawanka bai san kome a kan dukan waɗannan al’amura ba.”16. Amma sarki ya ce, “Lalle Ahimelek za ka mutu, da kai da dukan iyalin mahaifinka.”17. Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.” Amma ma’aikatan sarki ba su yarda su sa hannu su kashe firistocin Ubangiji ba.18. Sai sarki ya umarce Doyeg ya ce, “Ka juya ka kakkashe firistocin.” Doyeg mutumin Edom ya juya ya kakkashe firistocin. A ranar kuwa ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke sanye da efod na lilin.19. Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakuna, da kuma tumaki.20. Amma Abiyatar ɗan Ahimelek jikan Ahitub ya tsere, ya gudu zuwa wurin Dawuda.21. Abiyatar gaya wa Dawuda cewa, “Shawulu ya hallaka firistocin Ubangiji.”22. Dawuda ya ce wa Abiyatar, “Lalle a wancan ranar, sa’ad da na ga Doyeg mutumin Edom a can, na san tabbatacce zai gaya wa sarki. Ni ne sanadin mutuwar dukan iyalin mahaifinka.23. Ka zauna tare da ni, kada ka ji tsoro mutumin da yake neman ranka, yana nema raina ma. Ka zauna lafiya tare da ni.”1 Samaʼila 23:1-291. Sa’ad da aka ce wa Dawuda, “Duba ga Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Keyila, suna kwashe musu hatsi a masussukai.”2. Sai Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya ce, “In tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Jeka ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci Keyila.”3. Amma mutanen Dawuda suka ce masa, “Ga shi, a nan ma a Yahuda muna jin tsoro, balle mu tafi Keyila mu yi yaƙi da sojojin Filistiyawa!”4. Dawuda ya sāke nemi nufin Ubangiji, sai Ubangiji ya ce masa, “Tashi ka gangara zuwa Keyila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”5. Sa’an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Keyila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kwashe musu shanunsu, suka jijji wa Filistiyawa ƙwarai, suka cece mutanen Keyila daga hannunsu.6. (Abiyatar ɗan Ahimelek ya zo da efod sa’ad da ya gudo zuwa wurin Dawuda a Keyila.)7. Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya tafi Keyila, sai ya ce, “Allah ya bashe shi a hannuna, domin Dawuda ya kulle kansa ke nan da ya shiga birnin da yake da ƙofofin da ake kulle da ƙarafa.”8. Shawulu ya kira dukan sojojinsa don yaƙi, su gangaro zuwa Keyila su mamaye Dawuda da mutanensa.9. Da Dawuda ya ji labari Shawulu yana shirya hanyar da zai kashe shi, sai ya ce wa Abiyatar firist, “Kawo mini efod a nan.”10. Dawuda ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bawanka ya sami labari cewa tabbatacce Shawulu yana shirin zuwa Keyila yă hallaka garin saboda ni.11. Mutanen Keyila za su bashe ni a gare shi? Shawulu zai gangaro nan kamar yadda bawanka ya sami labari? Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka gaya wa bawanka.” Ubangiji ya ce, “Zai zo.”12. Dawuda ya sāke cewa, “Mutanen Keyila za su bashe ni da mutanena ga Shawulu?” Ubangiji ya ce, “Za su yi.”13. Saboda haka Dawuda da mutanensa wajen mutum ɗari shida suka bar Keyila, suka yi ta tafiya daga wannan wuri zuwa wancan. Sa’ad da aka gaya wa Shawulu cewa Dawuda ya tsere daga Keyila, sai ya fasa tafiya can.14. Dawuda ya zauna a jeji cikin kogunan duwatsu da kuma tuddan jejin Zif. Kowace rana Shawulu ya yi ta neman Dawuda amma Allah bai bashe Dawuda a hannunsa ba.15. A lokacin da Dawuda yana zaune a Horesh cikin jejin Zif, ya sami labari cewa Shawulu ya fito don yă kashe shi.16. Yonatan ɗan Shawulu kuwa ya tafi wurin Dawuda a Horesh, ya ƙarfafa shi yă dogara ga Allah.17. Ya ce, “Kada ka ji tsoro, mahaifina Shawulu ba zai taɓa sa hannu a kanka ba. Za ka zama sarki a Isra’ila, ni kuma in zama na biyu gare ka. Kai, ko mahaifina Shawulu ma ya san da haka.”18. Su biyunsu kuwa suka ɗaura yarjejjeniya a gaban Ubangiji. Sai Yonatan ya koma gida amma Dawuda ya zauna Horesh.19. Zifawa suka tafi wurin Shawulu a Gibeya suka ce masa, “Ashe, ba Dawuda ne yake ɓuya a cikinmu a kogwannin duwatsu a Horesh a bisan tudun Hakila, kudu da Yeshimon ba?20. Yanzu, ya sarki, ka gangaro, ka zo a duk lokacin da ka ga ya yi maka, ka zo mu kuma hakkinmu ne mu bashe shi a hannun sarki.”21. Shawulu ya ce, “ Ubangiji ya yi muku albarka, gama kun damu da ni.22. Ku tafi ku ƙara shiri. Ku san inda yakan tafi, wane ne kuma ya gan shi a can. An gaya mini cewa shi mai wayo ne sosai.23. Ku binciko duk wuraren da yakan ɓuya, sai ku dawo ku gaya mini tabbataccen labari. Sa’an nan zan tafi tare da ku in yana can. Zan nemi shi ko’ina cikin dukan kabilar Yahuda.”24. Sai suka tashi suka koma Zif, suka sha gaban Shawulu. Dawuda da mutanensa kuwa suna jejin Mawon cikin Araba, kudu da Yeshimon.25. Shawulu da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya gangara cikin duwatsu ya zauna a cikin jejin Mawon. Sa’ad da Shawulu ya ji haka, sai ya tafi jejin Mawon yana fafaran Dawuda.26. Shawulu yana tafiya a gefe ɗaya na dutsen, Dawuda da mutanensa kuma suna a wancan gefe, suna hanzari su ɓace wa Shawulu. Sa’ad da Shawulu da sojojinsa suka kusa cimma Dawuda da mutanensa don su kama su,27. sai wani manzo ya zo wurin Shawulu yana cewa, “Ka koma da sauri, Filistiyawa sun kawo wa ƙasar hari.”28. Shawulu kuwa ya janye daga fafaran Dawuda, ya tafi yă ƙara da Filistiyawa. Dalilin ke nan da ake kiran wannan wuri Sela Hammalekot, wato, dutsen tserewa.29. Dawuda kuwa ya haura daga can ya zauna a kogwannin duwatsun En Gedi.Zabura 59:6-176. Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.7. Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”8. Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a.9. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,10. Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.11. Amma kada ka kashe su, ya Ubangiji garkuwarmu, in ba haka mutanena za su manta. Cikin ikonka ka sa su yi ta yawo barkatai, ka kuma kawar da su.12. Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,13. ka cinye su da hasala, ka cinye su sarai. Sa’an nan za a sani a iyakar duniya cewa Allah yana mulki a bisa Yaƙub.14. Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.15. Suna ta yawo neman abinci su kuwa yi haushi in ba su ƙoshi ba.16. Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala.17. Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.Karin Magana 16:1-21. Ga mutum ne shirye-shiryen zuciya suke, amma daga Ubangiji ne amshin harshe kan zo.2. Dukan hanyoyin mutum sukan yi kamar marar laifi ne gare shi, amma Ubangiji yakan auna manufofi.Yohanna 1:1-281. Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne.2. Yana nan tare da Allah tun farar farawa.3. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.4. A cikinsa rai ya kasance, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.5. Hasken yana haskakawa cikin duhu, amma duhun bai rinjaye shi ba.6. Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.7. Ya zo a matsayin mai shaida domin yă ba da shaida game da wannan haske, don ta wurinsa dukan mutane su ba da gaskiya.8. Shi kansa ba shi ne hasken ba; sai dai ya zo a matsayin shaida ne kaɗai ga hasken.9. Haske na gaskiya da yake ba da haske ga kowane mutum mai shigowa duniya.10. Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.11. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.12. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah13. ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.14. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.15. (Yohanna ya ba da shaida game da shi. Ya ɗaga murya yana cewa, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya fi ni girma domin yana nan kafin ni.’ ”)16. Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.17. Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.18. Ba wanda ya taɓa ganin Allah, sai dai Allah da yake Ɗaya da kuma Makaɗaici wanda yake a gefen Uba, shi ne ya bayyana shi.19. To, ga shaidar Yohanna sa’ad da Yahudawan Urushalima suka aiki firistoci da Lawiyawa su tambaye shi ko shi wane ne.20. Bai yi mūsu ba, amma ya shaida a fili cewa, “Ba ni ne Kiristi ba.”21. Sai suka tambaye shi suka ce, “To, wane ne kai? Kai ne Iliya?” Ya ce, “A’a, ni ba shi ba ne.” “Kai ne Annabin nan?” Ya amsa ya ce, “A’a.”22. A ƙarshe suka ce, “Wane ne kai? Ka ba mu amsa don mu mayar wa waɗanda suka aike mu. Me kake ce da kanka?”23. Yohanna ya amsa da kalmomin annabi Ishaya, “Ni murya ne mai kira a hamada, ‘Ku miƙe hanya domin Ubangiji.’ ”24. To, waɗansu Farisiyawan da aka aika25. suka tambaye shi suka ce, “Don me kake yin baftisma in kai ba Kiristi ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”26. Yohanna ya amsa ya ce, “Ni dai ina baftisma da ruwa ne, amma a cikinku akwai wani tsaye da ba ku sani ba.27. Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”28. Wannan duk ya faru ne a Betani a ƙetaren Urdun, inda Yohanna yake yin baftisma. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.