Baibul a cikin shekara guda Mayu 111 Samaʼila 24:1-221. Bayan da Shawulu ya komo daga fafaran Filistiyawa, sai aka gaya masa cewa, “Dawuda yana can a Jejin En Gedi.”2. Saboda haka Shawulu ya zaɓi mutum dubu uku daga cikin dukan Isra’ila, suka fita neman Dawuda da mutanensa kusa da Duwatsun Awakin Jeji.3. Da Shawulu ya isa inda ake ajiye garken tumaki a bakin hanya inda akwai kogo, sai ya shiga ciki kogon don yă yi bayan gari. Dawuda da mutanensa kuwa suna can zaune a ƙurewar kogon.4. Mutanen Dawuda suka ce, wannan rana ce Ubangiji ya yi magana ya ce maka, “Zan ba da maƙiyinka a hannunka domin ka yi abin da ka ga dama da shi.” Sai Dawuda ya tashi a hankali ya je ya yanke shafin rigar Shawulu.5. Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu.6. Ya ce wa mutanensa, “ Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.”7. Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa.8. Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.9. Ya ce wa Shawulu, “Me ya sa kake saurari mutanen da suke cewa, ‘Dawuda ya dāge yă cuce ka’?10. Yau ka ga da idonka yadda Ubangiji ya bashe ka a hannuna a cikin kogon nan. Waɗansu sun ce mini in kashe ka, amma na bar ka, na ce, ‘Ba zan sa hannuna a kan shugabana ba, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.’11. Babana, duba, ga shafin rigarka a hannuna, na yanke shafin rigarka amma ban kashe ka ba. Yanzu ka gane ka kuma sani cewa ba ni da laifin aikata kome ko tayarwa, ban yi maka laifi ba, amma kana farautar raina.12. Ubangiji zai shari’anta tsakanina da kai. Ubangiji zai sāka mini laifin da ka yi mini, amma ni kam ba zan taɓa ka ba.13. Kamar yadda karin maganan nan na dā ya ce, ‘Daga cikin masu mugunta, mugunta ke fitowa,’ hannuna dai ba zai taɓa ka ba.14. “Wane ne sarkin Isra’ila, ka fito kake bi? Wa kake kora? Kana bin mataccen kare ko kuɗin cizo?15. Ubangiji yă zama alƙali, yă yi shari’a tsakanina da kai, bari Ubangiji yă duba, yă tsaya mini, yă nuna ba ni da laifi.”16. Da Dawuda ya gama wannan magana, sai Shawulu ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Sai ya fasa da kuka.17. Ya ce, “Ka fi ni gaskiya, ka yi mini alheri, ni kuwa na yi maka mugunta.18. Ga shi yanzu ka faɗa mini alherin da ka yi mini. Ubangiji ya bashe ni a hannunka amma ba ka kashe ni ba.19. In mutum ya sami maƙiyinsa, zai bar shi yă tafi lafiya ba tare da yin masa rauni ba? Ubangiji yă sāka maka, gama ka nuna mini alheri a yau.20. Na sani tabbatacce za ka zama sarki. Masarautar Isra’ila za tă kahu a hannunka.21. Yanzu ka rantse mini da Ubangiji cewa ba za ka hallaka zuriyarta ko ka share sunana daga iyalin mahaifina ba.”22. Sai Dawuda ya rantse wa Shawulu. Sa’an nan Shawulu ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka haura zuwa wurin ɓuya.1 Samaʼila 25:1-441. Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.2. A Mawon, akwai wani mutum wanda yake da dukiya a Karmel, mutumin mai arziki ne ƙwarai. Yana da awaki dubu ɗaya, da tumaki dubu uku waɗanda yake wa aski a Karmel.3. Ana ce da shi Nabal, sunan matarsa kuwa Abigiyel. Tana da hikima ga ta kuma kyakkyawa, amma mijinta mai rowa ne marar mutunci. Shi daga kabilar Kaleb ne.4. Lokacin da Dawuda yake a jeji, ya ji labari cewa Nabal yana askin tumaki.5. Sai ya zaɓi samari goma ya aike su wurin Nabal a Karmel su gaishe shi a madadinsa,6. su ce masa, “Ranka yă daɗe, ina maka fatan alheri, kai da gidanka da dukan abin da kake da shi!7. “Na ji cewa, yanzu lokacin askin tumaki ne. Sa’ad da makiyayanka suke tare da mu, ba mu cuce su ba, kuma duk zamansu a Karmel ba abin da yake nasu da ya ɓata.8. Ka tambayi bayinka za su kuwa gaya maka. Saboda haka ka yi wa mutanena kirki, gama yau ranar biki ce. Ina roƙonka ka ba wa samarina, wato, bayinka, da ni ɗanka Dawuda, duk abin da kake iya ba su.”9. Da mutanen Dawuda suka isa wurin Nabal, suka ba wa Nabal wannan saƙo a sunan Dawuda, sai suka jira.10. Nabal ya ce wa mutanen Dawuda, “Wane ne wannan Dawuda? Wane ne wannan ɗan Yesse? Yawancin bayi suna tayar wa iyayengijinsu a kwanakin nan.11. Don me zan ɗauki burodina da ruwana, da kuma naman da na yanka saboda masu yin wa tumakina aski in ba mutanen da ban ma san inda suka fito ba?”12. Mutanen Dawuda suka juya suka koma. Da suka iso sai suka faɗa wa Dawuda abin da Nabal ya ce.13. Dawuda ya ce wa mutanensa, “Kowa yă rataya takobinsa.” Sai duk suka yi haka. Dawuda kuma ya rataya nasa. Mutum wajen ɗari huɗu suka tafi tare da Dawuda, mutum ɗari biyu kuwa suka zauna suna gadin kayansu.14. Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.15. Waɗannan mutane kuwa sun yi mana kirki ƙwarai, ba su ba mu wata wahala ba. Babu abu guda da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su.16. Dare da rana sun zama mana katanga kewaya da mu, a duk tsawon lokacin da muke kiwon tumakinmu kusa da su.17. Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.”18. Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.19. Sai ta ce wa bawanta, “Yi gaba, zan bi ka”. Amma ba tă gaya wa Nabal, mijinta ba.20. Da tana tafiya a kan jaki, ta kai gindin wani dutse ke nan, sai ga Dawuda da mutanensa suna gangarowa zuwa wajen da take. Sai ta tafi, ta sadu da su.21. Bai daɗe ba da Dawuda ya ce a ransa, “Ashe, a banza ne na yi ta lura da dukan abin da yake na mutumin nan a jeji, har ba abinsa da ya ɓace. Ga shi, ya rama mini alheri da mugunta.22. Bari Allah yă yi duk abin da ya ga dama da ni in na bar ko ɗaya daga mazan da suke da tare shi, gobe da safe.”23. Da Abigiyel ta ga Dawuda, sai ta gaggauta ta sauka daga kan jaki, ta rusuna a gaban Dawuda da fuskarta har ƙasa.24. Ta fāɗi a ƙafafunsa ta ce, “Bari laifin yă zama nawa, ranka yă daɗe. Ina roƙonka ka bar baiwarka ta yi magana, ka ji abin da baiwarka za tă ce.25. Kada ranka yă daɗe, yă kula da Nabal, mugun mutumin nan. Shi dai kamar sunansa ne, sunansa Wawa ne, kuma wawanci yana cikinsa. Amma ni baiwarka, ban ga mutanen da ranka yă daɗe ya aika ba.26. Da yake yanzu, ya mai girma, Ubangiji ya hana ka zubar da jini da kuma ɗaukan wa kanka fansa, muddin Ubangiji yana raye, kai kuma kana a raye, bari maƙiyinka da dukan waɗanda suke niyya su cuci shugabana su zama kamar Nabal.27. Bari kuma ka karɓi wannan kyautar da baiwarka ta kawo don samarin da suke binka.28. Ina roƙonka ka gafarta wa baiwarka laifinta gama tabbatacce Ubangiji zai ba shugabana dawwammamiyar sarauta, gama kana yin yaƙin Ubangiji ne. Kuma ba wani mugun abin da zai same ka muddin kana a raye.29. Ko da yake wani mutum yana fafaranka domin yă kashe ka, Ubangiji Allahnka zai kiyaye ranka. Amma za a wurgar da rayukan maƙiyanka kamar yadda ake wurga dutsen majajjawa.30. Sa’ad da Ubangiji ya cika kowane alherinsa da ya yi wa shugabana alkawari, ya kuma keɓe shi sarki a bisa Isra’ila,31. kada yă zama cewa zuciyarka ta ba ka laifi ko ka damu cewa kana da alhakin jini, kada ka yi ramuwa da kanka. Sa’ad da Ubangiji ya nuna maka alheri, ka tuna da ni, baiwarka.”32. Dawuda ya ce wa Abigiyel, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya aiko ki don ki same ni yau.33. Bari Allah yă albarkace ki saboda hikima yanke hukuncinki da kuma hana ni zubar da jini da ɗauka wa kaina fansa da hannuna a wannan rana.34. Ubangiji, ya hana ni in yi miki ɓarna. Da ba don kin zo kin sadu da ni ba, na rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila Mai Rai, babu ko ɗaya daga cikin mazan gidan Nabal da zai rage gobe da safe.”35. Sa’an nan Dawuda ya karɓi abin da ta kawo masa daga hannunta, ya kuma ce mata, “Ki koma gida kada ki damu, na ji koke-kokenki, zan kuma biya miki bukatarki.”36. Da Abigiyel ta kai gida sai ta sami Nabal cikin gida yana ta fama biki iri na sarakuna. Yana ji wa ransa daɗi, ya kuma bugu tilis, saboda haka ba tă ce masa kome ba sai da gari ya waye.37. Da safe sa’ad da Nabal ya natsu, sai matarsa ta gaya masa dukan abin da ya faru. Sai zuciyarsa ta tsinke, ya zama kamar dutse.38. Bayan kusan kwana goma, Ubangiji ya bugi Nabal, sai ya mutu.39. Da Dawuda ya sami labarin mutuwar Nabal, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya sāka mini a kan irin renin da Nabal ya yi mini. Ya hana bawansa yin mugunta, ga shi ya ɗora wa Nabal muguntar da ya yi.” Sai Dawuda ya aika wa Abigiyel cewa tă zama matarsa.40. Bayin Dawuda suka tafi Karmel suka ce wa Abigiyel, “Dawuda ya aike mu gare ki, mu zo mu ɗauke ki ki zama matarsa.”41. Sai ta rusuna da fuskarta har ƙasa ta ce, “Ni baranyarka ce, na shirya in bauta maka in kuma wanke ƙafafun bayin shugabana.”42. Abigiyel ta tashi da sauri ta hau jaki, ta kuma sa ’yan mata biyar da suke mata hidima su bi ta, suka tafi tare da ’yan saƙon Dawuda. Ta kuwa zama matarsa.43. Dawuda a lokacin ya riga ya auri Ahinowam daga Yezireyel, dukansu suka zama matansa.44. Amma Shawulu ya aurar da Mikal, ’yarsa, matar Dawuda, ga Falti ɗan Layish wanda yake daga Gallim.Zabura 60:1-51. Ka ki mu, ya Allah, ka kuma fashe kāriyarmu; ka yi fushi da mu, yanzu ka mai da mu!2. Ka girgiza ƙasar ka kuma tsaga ta; ka daure karayarta, gama tana rawa.3. Ka nuna wa mutanenka lokutan wahala; ka ba mu ruwan inabin da ya sa muka bugu.4. Amma ga waɗanda suke tsoronka, ka ɗaga tuta don a buɗe gāba da baka.5. Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.Karin Magana 16:3-33. Ka miƙa wa Ubangiji dukan abin da kake yi, shirye-shiryenka kuwa za su yi nasara.Yohanna 1:29-5129. Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!30. Wannan shi ne wanda nake nufi sa’ad da na ce, ‘Mutum mai zuwa bayana ya fi ni girma, domin yana nan kafin ni.’31. Ko ni ma dā ban san shi ba, sai dai abin da ya sa na zo ina baftisma da ruwa shi ne domin a bayyana shi ga Isra’ila.”32. Sai Yohanna ya ba da wannan shaida, “Na ga Ruhu ya sauko kamar kurciya daga sama ya zauna a kansa.33. Dā ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa ya gaya mini cewa, ‘Mutumin da ka ga Ruhu ya sauko ya kuma zauna a kansa shi ne wanda zai yi baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’34. Na gani na kuma shaida cewa wannan Ɗan Allah ne.”35. Kashegari kuma Yohanna yana can tare da biyu daga cikin almajiransa.36. Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”37. Da almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.38. Da juyewa, sai Yesu ya ga suna bin sa, sai ya tambaye, su ya ce, “Me kuke nema?” Suka ce, “Rabbi” (wato, “Malam”), “ina kake da zama?”39. Ya amsa musu ya ce, “Ku zo, za ku kuma gani.” Saboda haka suka je suka ga inda yake da zama, suka kuma zauna a can tare da shi. Wajen sa’a ta goma ce kuwa.40. Andarawus ɗan’uwan Siman Bitrus, yana ɗaya daga cikin biyun nan da suka bi Yesu bayan da suka ji maganar Yohanna a kan Yesu.41. Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi).42. Ya kuma kawo shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi ya ce, “Kai ne Siman ɗan Yohanna. Za a ce da kai Kefas” (in an fassara, Bitrus ke nan).43. Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, “Bi ni.”44. Filibus, kamar Andarawus da Bitrus shi ma daga garin Betsaida ne.45. Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”46. Natanayel ya ce, “A Nazaret! Wani abin kirki zai iya fito daga can?” Filibus ya ce, “Zo ka gani.”47. Da Yesu ya ga Natanayel yana zuwa, sai ya yi magana game da shi cewa, “Ga mutumin Isra’ila na gaske wanda ba shi da ha’inci.”48. Natanayel ya yi tambaya ya ce, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa ya ce, “Na gan ka yayinda kake a gindin itacen ɓaure, kafin Filibus yă kira ka.”49. Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”50. Yesu ya ce, “Ka gaskata domin na ce maka na gan ka a gindin itacen ɓaure. Za ka ga abubuwan da suka fi haka.”51. Sai ya ƙara da cewa, “Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.