Baibul a cikin shekara guda Mayu 121 Samaʼila 26:1-251. Zifawa suka je wurin Shawulu a Gibeya suka ce, “Ashe, ba Dawuda ne ya ɓuya a tudun Hakila da yake fuskantar Yeshimon ba?”2. Sai Shawulu ya tashi ya gangara zuwa Jejin Zif, tare da zaɓaɓɓun mutane dubu uku na Isra’ila. Suka fita neman Dawuda a can.3. Shawulu ya yi sansani a bakin hanyar zuwa tudun Hakila mai fuskantar Yeshimon. Amma Dawuda yana zaune a jeji. Sa’ad da ya ga Shawulu ya biyo shi har zuwa can,4. sai ya aiki ’yan leƙen asiri su tabbata lalle Shawulu ya iso can.5. Sai Dawuda ya kintsa ya tafi inda Shawulu ya yi sansani. Ya ga inda Shawulu da Abner ɗan Ner shugaban ƙungiyar soja suka kwanta. Shawulu yana kwance a cikin sansani tare da sojoji kewaye da shi.6. Sai Dawuda ya ce wa Ahimelek mutumin Hitti da Abishai ɗan Zeruhiya ɗan’uwan Yowab, “Wa zai gangara tare da ni zuwa sansanin Shawulu?” Sai Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”7. Saboda haka Dawuda da Abishai suka gangara zuwa wurin rundunar da dare, sai ga Shawulu kwance yana barci a cikin sansani da māshinsa a kafe a ƙasa kusa da kansa. Abner kuwa tare da sojoji suna kwance kewaye da shi.8. Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Allah ya ba da maƙiyinka a hannunka. Bari in kafe shi da ƙasa da māshina, zan soke shi da māshi sau ɗaya tak, ba na bukata in soke shi sau biyu.”9. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira?10. Muddin Ubangiji yana a raye, Ubangiji da kansa zai buge shi, ko yă mutu a lokacinsa, ko kuma yă mutu a wurin yaƙi.11. Amma Allah yă sawwaƙa in sa hannu a shafaffen Ubangiji, ka ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da kansa mu tafi.”12. Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su.13. Sa’an nan Dawuda ya haye zuwa wancan gefen kwarin, ya hau kan wani tudu mai ɗan nisa inda Shawulu tare da mutanensa suke. Akwai babban fili tsakaninsu.14. Sai Dawuda ya kira sojojin Shawulu da kuma Abner ɗan Ner ya ce, “Abner ba za ka amsa mini ba?” Abner ya ce, “Wane ne yake kira yana damun sarki haka?”15. Dawuda ya ce wa Abner, “Wane irin mutum ne kai? Ba kai ne soja mafi iya yaƙi a Isra’ila ba? Don me ba ka yi gadin ranka yă daɗe, sarki da kyau ba? Ɗazu wani ya shiga tsakiyarku don yă kashe ranka yă daɗe, sarki.16. Abin da ka yi bai yi kyau ba. Muddin Ubangiji yana a raye kai da mutanenka kun cancanci mutuwa, domin ba ku lura da maigidanku shafaffe na Ubangiji ba. Ka duba kewaye da kai, ina māshi da kuma butar ruwan da suke kusa da kansa?”17. Shawulu ya gane muryar Dawuda, sai ya ce, “Muryarka ke nan ɗana Dawuda?” Dawuda ya ce, “I, muryata ce ya ranka yă daɗe, sarki.”18. Ya ƙara da cewa, “Don me ranka yă daɗe, yake fafarata? Mene ne na yi? Wane abu ne aka same ni da laifi a kai?19. To, bari ranka yă daɗe, sarkina yă kasa kunne yă ji abin da zan faɗa. Idan Ubangiji ne ya sa ka yi fushi da ni, bari yă karɓi hadaya ta hatsi. Amma idan mutane ne suka sa ka, bari a la’anta su, Ubangiji ne shaidata. Gama sun kore ni don kada in sami rabo cikin gādon Ubangiji, suna cewa, ‘Ka je ka bauta wa waɗansu alloli.’20. Kada ka yarda jinina yă zuba a ƙasa nesa da gaban Ubangiji. Sarkin Isra’ila ya fito yă nemi kuɗin cizo kamar mai farautar kazan duwatsu.”21. Sai Shawulu ya ce, “Na yi zunubi ka dawo Dawuda ɗana. Ba zan yi maka kome ba, domin ka darajarta raina yau. Lalle na yi wawanci! Na yi babban kuskure.”22. Dawuda ya ce, “Ga māshin sarki, ka aiko wani saurayi yă zo yă karɓa.23. Ubangiji yakan sāka wa kowa bisa ga adalcinsa da amincinsa. Ubangiji ya bashe ka a hannuna yau, amma ba zan sa hannuna a kan shafaffe na Ubangiji ba.24. Kamar yadda na ga darajar ranka yau. Haka ma bari Ubangiji yă ga darajar raina, yă cece ni daga dukan wahala.”25. Sai Shawulu ya ce wa Dawuda, “Allah yă albarkace ka ɗana, Dawuda, za ka yi manyan abubuwa, tabbatacce kuma ka yi nasara.” Sai Dawuda ya yi tafiyarsa, Shawulu kuwa ya koma gida.1 Samaʼila 27:1-121. Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Wata rana Shawulu zai kashe ni, abu mafi kyau da zan yi shi ne in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Da haka Shawulu zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra’ila, a can kuwa zan tsira daga hannunsa.”2. Sai Dawuda tare da mutanensa, mutum ɗari shida suka tashi suka haye zuwa wurin Akish ɗan Mawok, sarkin Gat.3. Dawuda da mutanensa suka zauna a Gat tare da Akish. Kowa ya kasance tare da iyalinsa. Dawuda kuwa yana tare da matansa biyu. Ahinowam daga Yezireyel da Abigiyel matar Nabal da ya mutu daga Karmel.4. Da Shawulu ya sami labari cewa Dawuda ya gudu zuwa Gat, bai ƙara fita nemansa ba.5. Sai Dawuda ya ce wa Akish, “In na sami tagomashi a gabanka ka ba ni wani wuri a cikin biranenka in zauna a can. Don me bawanka zai kasance tare da kai a gidan sarauta?”6. A ranar Akish ya ba shi Ziklag wanda tun dā take ta sarkin Yahuda.7. Dawuda ya zauna a yankin Filistiyawa shekara ɗaya da wata huɗu.8. Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.)9. Duk lokacin da ya yaƙi wani wuri, ba ya barin namiji ko mace da rai, amma sai ya kwashe tumaki, da shanu, da jakuna, da raƙuma, da riguna, sa’an nan yă koma wurin Akish.10. Idan Akish ya ce, “Ina ka kai hari yau?” Sai Dawuda yă ce, “Na kai hari a Negeb ta Yahuda, ko Negeb ta Yerameyel, ko Negeb na Keniyawa.”11. Bai bar a kawo namiji ko mace da rai a Gat ba, gama yana tunani, “Za su ba da sanarwa a kanmu su ce, ‘Ga abin da Dawuda ya yi.’ ” Haka ya yi ta yi dukan rayuwarsa a ƙasar Filistiyawa.12. Akish ya amince da Dawuda sosai, har ya ce wa kansa, “Ga shi ya mai da kansa abin ƙi ga mutanensa Isra’ilawa, zai zama bawana har abada.”Zabura 60:6-126. Allah ya yi magana daga wurinsa mai tsarki, “Da nasara zan rarraba Shekem in kuma auna Kwarin Sukkot.7. Gileyad nawa ne, Manasse kuma nawa ne; Efraim shi ne hular kwanona, Yahuda kuma sandar mulkina.8. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”9. Wa zai kawo ni birnin katanga? Wa zai bishe ni zuwa Edom?10. Ba kai ba ne, ya Allah, kai da ka ƙi mu ba ka kuwa fita tare da mayaƙanmu?11. Ka ba mu gudummawa a kan abokin gāba, gama taimakon mutum banza ne.12. Tare da Allah za mu yi nasara, zai kuma tattake abokan gābanmu.Karin Magana 16:4-54. Ubangiji yana yin kome domin amfaninsa, har ma da mugaye domin ranar masifa.5. Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.Yohanna 2:1-251. A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can,2. aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren.3. Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”4. Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”5. Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”6. Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.7. Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.8. Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.” Suka yi haka.9. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya10. ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”11. Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.12. Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki.13. Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima.14. A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi.15. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu.16. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”17. Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”18. Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?”19. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”20. Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?”21. Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne.22. Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.23. To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa.24. Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane.25. Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.