Baibul a cikin shekara guda Mayu 162 Samaʼila 3:1-391. Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi.2. An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron. Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;3. na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;4. na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;5. na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda. An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.6. Sa’ad da ake yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda, sai Abner ya yi ta ƙarfafa matsayinsa a gidan Shawulu.7. To, Shawulu yana da ƙwarƙwarar da ake kira Rizfa, ’yar Aiya. Sai Ish-Boshet ya ce wa Abner, “Don me kake kwana da ƙwarƙwarar mahaifina?”8. Abner ya husata saboda abin da Ish-Boshet ya ce, sai ya ce, “Kana tsammani ni mai cin amana ne? Kana zato ni mai goyon bayan Yahuda ne? Tun farko na nuna aminci ga gidan babanka Shawulu, da ’yan’uwansa, da abokansa! Ban kuwa ba da kai a hannun Dawuda ba. Ga shi yanzu a kan mace za ka ga laifina?9. Allah yă yi wa Abner hukunci mai tsanani, in ban goyi bayan Dawuda ya sami abin da Ubangiji ya yi masa alkawari da rantsuwa ba.10. Zan kuma mayar wa Dawuda sarautar gidan Shawulu, in kafa kursiyin Dawuda a kan Isra’ila, da kan Yahuda tun daga Dan har zuwa Beyersheba.”11. Ish-Boshet bai ƙara yin karambanin ce wa Abner kome ba, gama yana tsoronsa.12. Sai Abner ya aiki manzanni a madadinsa wurin Dawuda su ce masa, “Ƙasar ta wane ne? Ka yi yarjejjeniya da ni, zan kuwa taimake ka, in juye dukan Isra’ila zuwa ɓangarenka.”13. Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”14. Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”15. Sai Ish-Boshet ya ba da umarni, aka kuwa ɗauke ta daga gidan mijinta Faltiyel ɗan Layish.16. Amma mijin ya raka ta, yana tafe yana kuka, ya bi ta har Bahurim. Sai Abner ya ce masa, “Koma gida!” Sai ya koma.17. Abner ya tattauna da dattawan Isra’ila ya ce, “An daɗe kuna nema ku naɗa Dawuda sarkinku.18. To, yanzu sai ku yi haka! Gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta wurin bawana Dawuda zan ceci mutanena Isra’ila daga hannun Filistiyawa, da kuma hannun dukan abokan gābansu.’ ”19. Abner kuma ya yi magana da mutane Benyamin da kansa. Sa’an nan ya tafi Hebron yă gaya wa Dawuda ko mene ne Isra’ila da kuma dukan gidan Benyamin suke so su yi.20. Sa’ad da Abner wanda yake tare da mutane ashirin suka zo wurin Dawuda a Hebron, Dawuda ya shirya masa liyafa tare da mutanensa.21. Sai Abner ya ce wa Dawuda, “Bari in tafi nan da nan in tattara dukan Isra’ila wa ranka yă daɗe, sarki, saboda su yi alkawari da kai, ka kuma ka yi mulki bisa dukansu yadda ranka yake so.” Saboda haka Dawuda ya sallami Abner, ya kuwa tafi lafiya.22. Ba a jima ba sai mutanen Dawuda da Yowab suka dawo daga hari. Suka kawo ganima da yawa tare da su. Abner kuwa ya riga ya bar Dawuda a Hebron, domin Dawuda ya sallame shi, shi kuma ya tafi lafiya.23. Sa’ad da Yowab da dukan sojoji suka dawo, aka gaya masa cewa Abner ɗan Ner ya zo wurin sarki, sarki kuwa ya sallame shi, ya kuma tafi lafiya.24. Sai Yowab ya je wurin sarki ya ce, “Me ke nan ka yi? Abner ya zo wurinka. Don me ka ƙyale shi yă tafi? Ga shi kuwa ya tafi!25. Ka san Abner ɗan Ner ya zo ne yă ruɗe ka, yă ga fitarka da shigarka, yă kuma binciki kome da kake yi.”26. Yowab ya tashi daga gaban Dawuda ya tafi ya aika manzanni su bi Abner. Suka same shi a rijiyar Sira suka komo da shi, Dawuda kuwa bai sani ba.27. To, da Abner ya komo Hebron, Yowab ya ratse da shi zuwa hanyar shigar gari kamar zai gana da shi a kaɗaice. Amma a can ya soki Abner a ciki, ya kashe shi don yă rama mutuwar ɗan’uwansa Asahel.28. Daga baya, Dawuda ya ji labarin sai ya ce, “Ni da masarautata har abada ba mu da laifi a gaban Ubangiji game da jinin Abner ɗan Ner.29. Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”30. (Yowab da ɗan’uwansa Abishai suka kashe Abner don yă kashe ɗan’uwansu Asahel a yaƙin Gibeyon.)31. Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.32. Suka binne Abner a Hebron, sarki kuwa ya ɗaga murya ya yi kuka a kabarin Abner.33. Sarki ya kuma yi wannan waƙar makoki domin Abner ya ce, “Daidai ne Abner yă mutu, kamar yadda marasa bin doka suke mutuwa?34. Hannuwanka ba a daure suke ba, ƙafafunka ba a tabaibaye suke ba. Ka mutu kamar waɗanda suke mutuwa a hannun mugaye.” Sai dukan mutane suka sāke fashe da kuka saboda shi.35. Sa’an nan duk suka zo suka roƙi Dawuda yă ci wani abu tun rana ba tă fāɗi ba; amma Dawuda ya rantse ya ce, “Bari Allah yă hukunta ni, in na ɗanɗana abinci ko wani abu kafin rana ta fāɗi!”36. Dukan mutane suka lura suka kuma ji daɗi ƙwarai, tabbatacce kome da sarki ya yi, ya gamshe su.37. Saboda haka a ranar dukan mutane da dukan Isra’ila suka gane sarki ba shi da hannu a kisan Abner ɗan Ner.38. Sa’an nan sarki ya ce wa mutanensa, “Ba ku gane cewa ɗan sarki kuma babban mutum ya mutu a ƙasar Isra’ila a yau ba?39. A yau, ko da yake ni naɗaɗɗen sarki ne, duk da haka na raunana, kuma waɗannan ’ya’yan Zeruhiya sun fi ƙarfina. Ubangiji yă sāka wa mai aikata mugunta da muguntar da ya aikata!”2 Samaʼila 4:1-121. Sa’ad da Ish-Boshet ya ji labari cewa Abner ya mutu a Hebron, sai ya karaya, sai dukan hankalin Isra’ila ya tashi.2. To, ɗan Shawulu yana da ’ya’ya maza biyu da suke shugabannin ’yan hari. Ana kiran ɗaya Ba’ana, ɗayan kuma Rekab. Su ’ya’yan Rimmon mutumin Benyamin ne daga Beyerot, an lissafta Beyerot a ɓangaren Benyamin,3. domin mutanen Beyerot sun gudu zuwa Gittayim inda suke zaman baƙunci har wa yau.4. (Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)5. To, Rekab da Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, suka tafi gidan Ish-Boshet, suka isa can da tsakar rana yayinda yake hutun tsakar rana.6. Suka shiga sashe na cikin gida sai ka ce suna so su ɗibo alkama ne, suka soke shi a ciki. Sa’an nan Rekab da Ba’ana ɗan’uwansa suka zame suka ɓace.7. Sun shiga gidan yayinda yake kwance a gado a ɗakin barcinsa. Bayan sun soke shi sai suka kashe shi, suka kuma datse kansa. Suka ɗauke shi, suka yi tafiya dukan dare suka bi ta Araba.8. Suka kawo kan Ish-Boshet wa Dawuda a Hebron, suka ce wa sarki, “Ga kan Ish-Boshet ɗan Shawulu, maƙiyinka, wanda ya nemi yă kashe ka. A yau Ubangiji ya rama wa ranka yă daɗe sarki, a kan Shawulu da zuriyarsa.”9. Dawuda ya ce wa Rekab da ɗan’uwansa Ba’ana, ’ya’yan Rimmon mutumin Beyerot, “Muddin Ubangiji yana a raye, wanda ya kuɓutar da ni daga wahala,10. sa’ad da wani mutum ya ce mini, ‘Shawulu ya mutu,’ yana tsammani ya kawo labari mai daɗi ne, na kama shi na kashe a Ziklag. Ladar da na ba shi ke nan saboda labarinsa!11. Balle fa, sa’ad da mugayen mutane suka kashe marar laifi a gidansa, a bisa gadonsa, ashe, ba zan nemi jininsa daga hannunku in kawar da ku a duniya ba!”12. Saboda haka Dawuda ya umarci mutanensa, suka kuwa kashe su. Suka yayyanka hannuwansu da ƙafafunsu, suka kuma rataye jikunansu kusa da tafki a Hebron. Amma suka ɗauki kan Ish-Boshet suka binne a kabarin Abner a Hebron.Zabura 62:5-125. Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne.6. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.7. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata.8. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu.9. Talakawa dai kamar shaƙar iska suke, Attajirai dai kamar shirim suke; in aka auna a ma’auni, su ba wani abu ba ne; dukansu dai kamar shaƙar iska ne kawai.10. Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.11. Abu guda Allah ya ce, abubuwa biyu na ji, “Cewa kai, ya Allah, kake mai ƙarfi,12. kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”Karin Magana 16:13-1513. Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya.14. Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai.15. Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.Yohanna 4:31-5431. Ana cikin haka, sai almajiransa suka roƙe shi suka ce, “Rabbi, ci abinci mana.”32. Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku san kome a kai ba.”33. Sai almajiran suka ce wa juna, “Shin, ko wani ya kawo masa abinci ne?”34. Yesu ya ce, “Abincina shi ne, in aikata nufin wannan da ya aiko ni, in kuma gama aikinsa.35. Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi.36. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.37. Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’38. Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”39. Samariyawa da yawa daga wannan gari suka gaskata da shi saboda shaidar macen da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”40. To, da Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roƙe shi yă zauna da su, ya kuwa zauna kwana biyu.41. Saboda kalmominsa kuwa da yawa suka gaskata.42. Sai suka ce wa macen, “Yanzu kam mun gaskata, ba don abin da kika faɗa kawai ba; yanzu mun ji da kanmu, mun kuwa san cewa wannan mutum tabbatacce shi ne Mai Ceton duniya.”43. Bayan kwana biyun nan sai ya bar can zuwa Galili.44. (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.)45. Da ya isa Galili, sai mutanen Galili suka marabce shi. Sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin Bikin Ƙetarewa, gama su ma sun kasance a can.46. Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum.47. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa.48. Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”49. Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.”50. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ka tafi. Ɗanka zai rayu.” Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi.51. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa.52. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.”53. Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, “Ɗanka zai rayu.” Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.54. Wannan ce abin banmamaki ta biyu da Yesu ya yi, bayan zuwansa daga Yahudiya zuwa Galili. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.