Baibul a cikin shekara guda Mayu 172 Samaʼila 5:1-251. Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne.2. A dā da Shawulu yake sarauta a bisanmu, kai ne kake bi Isra’ilawa zuwa yaƙe-yaƙensu. Ubangiji kuwa ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayi mutanena Isra’ila, za ka kuma zama sarkinsu.’ ”3. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka zo wurin Sarki Dawuda a Hebron, sarki ya yi yarjejjeniya da su a gaban Ubangiji, suka kuwa naɗa Dawuda sarki bisa Isra’ila.4. Dawuda yana da shekara talatin ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara arba’in.5. A Hebron ya yi mulki a bisa Yahuda shekara bakwai da wata shida, a Urushalima kuma ya yi mulki a bisa Isra’ila da Yahuda shekara talatin da uku.6. Sarki da mutanensa suka tafi Urushalima don su kai wa Yebusiyawan da suke zaune a can hari, Yebusiyawa suka ce wa Dawuda, “Ba za ka shiga nan ba; ko makafi da guragu kaɗai ma za su kore ka.” Suka yi tsammani suna cewa, “Dawuda ba zai iya shiga can ba.”7. Duk da haka, Dawuda ya kame kagarar Sihiyona, wadda ta zama Birnin Dawuda.8. A ranar, Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kame Yebusiyawa, dole yă yi amfani da wuriyar ruwa don yă kai ga waɗannan ‘guragu da makafi’ waɗanda suke abokan gāban Dawuda.” Shi ya sa suka ce, “ ‘Makafi da guragu’ ba za su shiga fadan sarki ba.”9. Sai Dawuda ya zauna a kagarar, ya kuma kira ta Birnin Dawuda. Ya gina wuraren da suke kewaye da ita, tun daga madogaran gini zuwa ciki.10. Ya yi ta ƙara ƙarfi, gama Ubangiji Allah Maɗaukaki yana tare da shi.11. To, Hiram sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda tare da gumaguman itacen al’ul, da kafintoci, da kuma maginan duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda fada.12. Dawuda kuwa ya gane Ubangiji ya naɗa shi sarki bisa Isra’ila, ya kuma ɗaukaka masarautarsa saboda mutanensa Isra’ila.13. Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa ’ya’ya maza da mata.14. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan da aka haifa masa a can. Shammuwa, Shobab, Natan, Solomon,15. Ibhar, Elishuwa, Nefeg, Yafiya,16. Elishama, Eliyada da Elifelet.17. Da Filistiyawa suka ji labari an shafe Dawuda sarki a bisa Isra’ila, sai suka haura da ƙarfi sosai don su nema shi, amma Dawuda ya ji labarin sai ya gangara zuwa mafaka.18. To, fa, Filistiyawa suka zo suka baje ko’ina a cikin Kwarin Refayim;19. saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.”20. Saboda haka Dawuda ya tafi Ba’al-Ferazim, a can ya ci su da yaƙi. Sai ya ce, “Kamar yadda ruwa yakan fasu, haka Ubangiji ya kakkarya abokan gābana a gabana.” Saboda haka aka kira wurin Ba’al-Ferazim.21. Filistiyawa suka bar gumakansu a can, Dawuda da mutanensa kuwa suka kwashe su.22. Har yanzu Filistiyawa suka sāke haurawa suka bazu a Kwarin Refayim;23. saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji, ya kuwa ce, “Kada ka haura kai tsaye, amma ka kewaya ta bayansu ka fāɗa musu a gaban itatuwan balsam.24. Da zarar ka ji tafiya kamar na takawar sojoji tana a bisan itatuwan balsam, sai ka yi maza, gama wannan alama ce cewa Ubangiji ya sha gabanka don yă karkashe sojojin Filistiyawa.”25. Saboda haka Dawuda ya aikata yadda Ubangiji ya umarce shi, ya kuma karkashe Filistiyawa tun daga Geba har zuwa Gezer.2 Samaʼila 6:1-231. Dawuda ya sāke tattara zaɓaɓɓun mutanen Isra’ila, dubu talatin.2. Shi, da dukan mutanensa suka tashi daga Ba’ala-Yahuda don su hauro da akwatin alkawarin Allah, wanda ake kira da Sunan Ubangiji Maɗaukaki, wanda yake zama a tsakanin kerubobin da suke a kan akwatin alkawarin.3. Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabuwar keken yaƙi, suka kawo shi daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Uzza da Ahiyo, ’ya’yan Abinadab maza, suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki suka bi da keken yaƙin4. da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab.5. Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.6. Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.7. Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah.8. Ran Dawuda ya ɓace gama fushin Ubangiji ya ɓarke a kan Uzza. Shi ya sa har wa yau ana kira wurin Ferez Uzza.9. Dawuda ya ji tsoron Ubangiji a ranar, sai ya ce, “Yaya akwatin alkawarin Ubangiji zai iya zuwa wurina?”10. Bai so yă ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji yă kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka sai ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat.11. Akwatin Alkawarin Ubangiji ya kasance a gidan Obed-Edom mutumin Gat har tsawon wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkace shi da dukan iyalinsa.12. To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “ Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki.13. Sa’ad da waɗanda suke ɗaukan akwatin alkawarin Ubangiji suka yi tafiya taki shida, sai yă yi hadayar bijimi da saniya mai ƙiba.14. Dawuda, sanye da efod lilin, ya yi ta rawa a gaban Ubangiji da dukan ƙarfinsa,15. yayinda shi da dukan gidan Isra’ila suka hauro da akwatin alkawarin Ubangiji da sowa da kuma busar ƙahoni.16. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.17. Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, aka ajiye shi a inda aka shirya masa a cikin tentin da Dawuda ya shirya dominsa. Dawuda kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama a gaban Ubangiji.18. Bayan ya gama yin hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji Maɗaukaki.19. Sa’an nan ya rarraba abinci, da ƙosai, dabino, da waina ga kowane mutum a cikin dukan jama’ar Isra’ila, maza da mata. Dukan mutane kuwa suka watse zuwa gidajensu.20. Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”21. Dawuda ya ce wa Mikal, “Na yi rawana domin in girmama Ubangiji ne, wanda ya zaɓe ni a maimakon mahaifinki ko wani daga cikin dukan gidansa, shi ne kuma ya sa ni sarki a kan Isra’ila, mutanen Ubangiji, zan yi biki a gaban Ubangiji.22. Zan ma mai da kaina abin reni fiye da haka, za a kuma zama abin reni a gare ki. Amma waɗannan bayi ’yan matan da kika yi magana a kai, za su gan ni da martaba.”23. Mikal ’yar Shawulu kuwa ba tă haifi ɗa ba har mutuwarta.Zabura 63:1-111. Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa.2. Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka.3. Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.4. Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.5. Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.6. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.7. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka.8. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.9. Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.10. Za a bayar da su ga takobi su kuma zama abincin karnukan jeji.11. Amma sarki zai yi farin ciki ga Allah; dukan waɗanda suke rantse da sunan Allah za su yabe shi, amma za a rufe bakunan maƙaryata.Karin Magana 16:16-1716. Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!17. Buɗaɗɗiyar hanyar masu aikata gaskiya kan guje wa mugunta; duk wanda yake lura da hanyarsa yakan lura da ransa.Yohanna 5:1-231. Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa.2. To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda an kuma kewaye shi da shirayi biyar.3. A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.