Baibul a cikin shekara guda Mayu 192 Samaʼila 9:1-131. Wata rana Dawuda ya yi tambaya ya ce, “Akwai wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu wanda zan nuna masa alheri saboda Yonatan?”2. To, akwai wani bawa na gidan Shawulu mai suna Ziba. Sai aka kira shi yă bayyana a gaban Dawuda, sarki ya ce masa, “Kai ne Ziba?” Sai ya ce, “I, ni ne, ranka yă daɗe.”3. Sa’an nan sarki ya yi tambaya ya ce, “Babu wani har yanzu da ya rage a gidan Shawulu don in nuna masa alherin Allah?” Ziba ya ce wa sarki, “Har yanzu akwai ɗan Yonatan da ya rage, sai dai shi gurgu ne a dukan ƙafafu.”4. Sarki ya ce, “Ina yake?” Ziba ya ce, “Yana a gidan Makir ɗan Ammiyel a Lo Debar.”5. Saboda haka Sarki Dawuda ya umarta aka kawo shi daga gidan Makir ɗan Ammiyel, daga Lo Debar.6. Sa’ad da Mefiboshet ɗan Yonatan, ɗan Shawulu, ya zo wurin Dawuda, sai ya rusuna har ƙasa ya yi gaisuwar bangirma. Dawuda ya ce, “Mefiboshet!” Shi kuwa ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, ga ni, bawanka.”7. Dawuda ya ce, “Kada ka ji tsoro, gama tabbatacce zan nuna maka alheri saboda mahaifinka Yonatan. Zan mayar maka da dukan ƙasar da take ta kakanka Shawulu, kullum kuma za ka ci a teburina.”8. Mefiboshet ya rusuna ya ce, “Ni ne wa har da za ka kula da ni? Ai! Ni bawanka ne da bai ma fi mataccen kare daraja ba.”9. Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa10. Kai da ’ya’yanka maza da bayinka za ku riƙa yin masa noma, ku kuma kawo hatsin, don jikan maigidanka yă sami abinci. Mefiboshet kuma, jikan maigidanka, zai riƙa ci a teburina.” (Ziba kuwa yana da ’ya’ya maza goma sha biyar da kuma bayi ashirin.)11. Sai Ziba ya ce wa sarki, “Bawanka zai aikata dukan abin da ranka yă daɗe sarki, ya umarce shi.” Saboda haka Mefiboshet ya riƙa ci a teburin Dawuda kamar sauran ’ya’yan sarki.12. Mefiboshet yana da wani ƙaramin ɗa sunansa Mika, dukan iyalin gidan Ziba kuwa bayin Mefiboshet ne.13. Mefiboshet ya zauna a Urushalima, gama kullum yana ci a teburin sarki, shi kuwa gurgu ne a dukan ƙafafu.2 Samaʼila 10:1-191. Ana nan sai sarkin Ammonawa ya rasu, ɗansa Hanun kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.2. Dawuda ya yi tunani a ransa ya ce, “Zan yi wa Hanun ɗan Nahash alheri kamar yadda mahaifinsa ya yi mini.” Saboda haka sai Dawuda ya aiki jakadu su yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka isa ƙasar Ammonawa,3. sai manyan mutanen Ammonawa suka ce wa Hanun shugabansu, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aiko da jakadu su kawo maka ta’aziyya? Ai, wayo ya yi don yă ga asirin birninmu, yă san ƙarfinmu, yă kuma ci mu da yaƙi.”4. Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda ya aske rabin gemun kowannensu, ya yayyage rigunarsu daidai ɗuwawu, sa’an nan ya sallame su.5. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda game da wannan, sai ya aiki manzanni su taryi waɗannan mutanen da aka ci mutuncinsu, gama an wulaƙanta su ƙwarai. Sai sarki ya ce musu, “Ku dakata a Yeriko har sai gemunku ya sāke girma, sa’an nan ku dawo.”6. Da Ammonawa suka gane cewa Dawuda ya ji fushi da su sosai saboda abin da suka yi, sai suka yi hayar sojojin ƙasar Arameyawa dubu ashirin daga Bet Rehob da Aram-Zoba, suka kuma yi hayar sarkin Ma’aka tare da mutum dubu ɗaya, suka kuma yi hayar maza dubu goma sha biyu daga Tob.7. Da jin haka, Dawuda ya tura Yowab da dukan sojojin yaƙi.8. Ammonawa suka fita suka ja dāgār yaƙi a ƙofar shiga birninsu, yayinda Aram-Zoba, da na Rehob, da mutane Tob, da kuma na Ma’aka, suka ja tasu dāgār a karkara.9. Yowab ya ga cewa an ja masa dāgār yaƙi gaba da baya; saboda haka sai ya zaɓi waɗansu shahararrun sojoji cikin Isra’ila, ya sa su gabza da Arameyawa.10. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin Abishai ɗan’uwansa, ya sa su gabza da Ammonawa.11. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ƙarfina, sai ku kawo mini gudummawa; amma in Ammonawa suka fi ƙarfinku, sai mu kawo muku gudummawa.12. Ku yi ƙarfin hali, mu kuma yi yaƙi da ƙarfin zuciya saboda mutanenmu da kuma birane Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da yake da kyau a idanunsa.”13. Sa’an nan Yowab da rundunar da take tare da shi suka ci gaba don su gabza da Arameyawa, Arameyawa kuwa suka gudu a gabansa.14. Da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka ruga da gudu a gaban Abishai, suka shiga cikin birni. Sa’an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙin da ya yi da Ammonawa.15. Bayan Arameyawa suka ga Isra’ila ta ci su da yaƙi, sai suka sāke tattara kansu.16. Hadadezer sarkin Zoba ya aika a kawo Arameyawan da suke ƙetaren Kogin Yuferites. Suka iso Helam a ƙarƙashin shugabancin Shobak, shugaban dukan sojojin Hadadezer.17. Da aka gaya wa Dawuda wannan, sai ya tattara dukan Isra’ila, ya ƙetare Urdun, ya je Helam. Arameyawa suka ja dāgār yaƙinsu, suka kara da Dawuda.18. Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, Dawuda kuwa ya kashe mahayan keken yaƙinsu ɗari bakwai, da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya bugi Shobak, shugaban ƙungiyar sojansu ya kuwa mutu a can.19. Sa’ad da dukan sarakuna waɗanda suke abokan tarayya na Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka yi sulhu da Isra’ilawa, suka kuma zama bayinsu. Wannan ya sa Arameyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudummawa.Zabura 65:1-81. Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu2. Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo.3. Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu.4. Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki.5. Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa,6. wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi,7. wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai.8. Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki.Karin Magana 16:20-2120. Duk wanda ya mai da hankali ga umarni yakan yi nasara, kuma mai albarka ne wanda yake dogara ga Ubangiji.21. Akan ce da masu hikima a zuciya hazikai, kuma kalmomi masu daɗi kan inganta umarni.Yohanna 6:1-211. Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),2. sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.3. Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.4. Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.5. Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”6. Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.7. Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”8. Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,9. “Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”10. Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.11. Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.12. Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”13. Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.14. Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”15. Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.16. Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,17. inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.18. Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.19. Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.20. Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”21. Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.