Baibul a cikin shekara guda Mayu 21 Samaʼila 6:1-211. Lokacin da akwatin alkawarin Ubangiji ya kai wata bakwai a ƙasar Filistiyawa.2. Filistiyawa suka kira firistoci da bokaye suka ce, “Me za mu yi da akwatin alkawarin Ubangiji? Ku gaya mana yadda za mu komar da shi inda ya fito.”3. Suka ce, in za ku komar da akwatin alkawarin Allah na Isra’ila kada ku komar da shi hannu wofi; amma ku tabbata kun aika da hadaya don laifi zuwa wurinsa. Sa’an nan za ku warke ku kuma san dalilin da ya sa bai cire hannunsa a kanku ba.4. Filistiyawa suka ce, “Wace irin hadaya don laifi za mu aika masa?” Suka ce, “Marurai biyar na zinariya da ɓeraye biyar na zinariya bisa ga yawan sarakunan Filistiyawa. Saboda annoba iri ɗaya ce ta buga ku da shugabanninku.5. Ku yi siffofin marurai da na ɓeraye da suke hallaka gari, ku ba da girma ga Allah na Isra’ila. Wataƙila zai ɗauke hukuncinsa daga gare ku da allolinku da kuma ƙasarku.6. Me ya sa kun taurare kanku kamar yadda Masarawa da Fir’auna suka yi? Da ya ba su matsanancin wahala, ba su bar Isra’ilawa suka tafi hanyarsu ba?7. “Yanzu fa ku shirya sabon keken shanu da shanu biyu masu ba wa ’ya’yansu nono, waɗanda ba a taɓa sa musu karkiya ba. Ku daure keken shanu wa shanun, amma ku tsare ’yan maruƙansu a gida.8. Ku ɗauki wani akwati ku sa siffofin zinariyan nan a ciki, waɗanda za su zama kyautai na shafen laifi, ku ajiye kusa da Akwati na UBANGIJI. Bayan haka sai ku sa keken shanun da akwatin a hanya, ku bar shi yă tafi.9. Amma ku zuba ido ku ga in ya haura zuwa yankinsa, zuwa Bet-Shemesh, to, Ubangiji ne ya kawo mana babban masifar a kanmu. Amma in bai bi ta nan ba, za mu san cewa ba shi ne ya buge mu ba, tsautsayi ne kawai.”10. Suka yi haka. Suka ɗauki shanun tatsa guda biyu suka ɗaura musu keken shanu, suka tsare ’yan maruƙansu a gida.11. Suka aza akwatin alkawarin Ubangiji a bisa keken shanun tare da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.12. Sai shanun suka miƙe zuwa Bet-Shemesh. Suka bi hanya daidai, ba su juya dama ko hagu ba. Shugabannin Filistiyawa suka bi har zuwa iyakar ƙasar Bet-Shemesh.13. A lokacin kuwa mutanen Bet-Shemesh suna girbin alkamansu a kwari da suka ɗaga ido suka hangi akwatin alkawarin Ubangiji, sai suka yi farin ciki ganinsa.14. Keken shanun ya zo filin Yoshuwa a Bet-Shemesh ya tsaya a gefen wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun suka miƙa shanun hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji.15. Lawiyawa suka saukar da akwatin alkawarin Ubangiji tare da babban akwati mai siffofin zinariya na ɓeraye da marurai suka ajiye su a kan ƙaton dutse. A wannan rana mutanen Bet-Shemesh suka miƙa hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu ga Ubangiji.16. Shugabanni biyar na Filistiyawan nan suka ga duk abin da ya faru, suka koma zuwa Ekron a ranar.17. Waɗannan su ne siffofi marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin miƙa hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.18. Filistiyawa kuma suka aika da siffofin ɓeraye biyar na zinariya. Yawan ɓerayen sun yi daidai da yawan garuruwan sarakunan nan biyar na Filistiyawa. Garuruwan sun ƙunshi waɗanda aka gina katangar birni kewaye da su, da kuma ƙauyukansu. Babban dutsen da suka ajiye akwatin alkawarin Ubangiji, ya zama shaida har wa yau a filin Yoshuwa a Bet-Shemesh.19. Amma Allah ya kashe waɗansu mutum saba’in na mutanen Bet-Shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawarin Ubangiji. Mutane kuwa suka yi makoki domin Ubangiji ya hallaka mutane da yawa.20. Mutanen Bet-Shemesh suka yi tambaya suka ce, wa zai iya tsaya a gaban Ubangiji Allah Mai Tsarki? Wurin wa akwatin alkawari zai je daga nan?21. Sai suka aiki manzanni zuwa Kiriyat Yeyarim suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawarin Ubangiji, ku zo ku ɗauka ku kai wajenku.”1 Samaʼila 7:1-171. Mutanen Kiriyat Yeyarim suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji. Suka kai a gidan Abinadab da ke kan tudu, suka keɓe Eleyazar ɗansa yă lura da akwatin alkawarin Ubangiji.2. Akwatin Alkawarin ya daɗe a Kiriyat Yeyarim ya kai shekara ashirin cif. Sai dukan mutanen Isra’ila suka yi makoki suka nemi Ubangiji.3. Saboda haka Sama’ila ya yi magana da dukan gidan Isra’ila ya ce, in har da zuciya ɗaya kuke juyowa ga Ubangiji sai ku raba kanku da baƙin alloli da gunkin nan Ashtarot, ku ba da kanku ga Ubangiji. Ku yi masa bauta shi kaɗai, zai kuɓutar da ku daga hannun Filistiyawa.4. Sai Isra’ilawa suka rabu da gumakan Ba’al da Ashtarot suka bauta wa Ubangiji kaɗai.5. Sama’ila ya ce, “Ku tattara dukan Isra’ila a Mizfa, ni kuwa zan yi addu’a ga Ubangiji dominku.”6. Sa’ad da suka taru a Mizfa, suka kawo ruwa suka zuba a gaban Ubangiji. A wannan rana suka yi azumi suka tuba, suka ce, “Mun yi wa Ubangiji zunubi!” Sama’ila kuwa ya zauna a Mizfa ya yi mulkin Isra’ilawa.7. Da Filistiyawa suka ji cewa Isra’ila sun taru a Mizfa, sai shugabanninsu suka zo don su yaƙe Isra’ila. Da Isra’ilawa suka ji labarin, sai suka tsorata saboda Filistiyawa.8. Suka ce wa Sama’ila, “Kada ka fasa kai kukanmu ga Ubangiji Allahnmu saboda mu, don yă cece mu daga hannun Filistiyawa.”9. Sama’ila ya kama ɗan rago ya miƙa shi ɗungum hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji. Ya yi roƙo ga Ubangiji a madadin Isra’ila, Ubangiji kuwa ya amsa addu’arsa.10. Lokacin da Sama’ila yana miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso kusa don su yi yaƙi da Isra’ila. A ranar Ubangiji ya sa babban tsawa ya ruɗar da Filistiyawa har suka gudu a gaban Isra’ilawa.11. Isra’ilawa suka fito a guje daga Mizfa suka fafari Filistiyawa suka yi ta karkashe su a hanya har kwarin Bet-Kar.12. Sa’an nan Sama’ila ya ɗauki dutse ya kafa tsakanin Mizfa da Shen, ya sa masa suna, Ebenezer ma’ana, “Har zuwa wannan lokaci Ubangiji ya taimake mu.”13. Ta haka Isra’ilawa suka ci Filistiyawa. Daga ranan Filistiyawa ba su ƙara yin nasara a kan Isra’ila ba. Ubangiji ya yi gāba da Filistiyawa har ƙarshen zamanin Sama’ila.14. Filistiyawa suka mayar wa Isra’ila da garuruwan da suka ƙwato, wato, daga Ekron zuwa Gat, dukan yankin ƙasarsu da yake ƙarƙashin ikon Filistiyawa. Aka kuma sami zaman lafiya tsakanin Isra’ilawa da Amoriyawa.15. Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa.16. Shekara-shekara Sama’ila yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal da Mizfa inda yakan yi musu shari’a.17. Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade.Zabura 55:1-81. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona;2. ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis3. hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina.4. Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.5. Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina.6. Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta,7. da na tafi can da nisa na zauna a hamada;8. da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.”Karin Magana 15:14-1414. Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.Luka 21:20-3820. “In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa.21. A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin.22. Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta.23. Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.24. Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika.25. “Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.26. Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.27. A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.28. Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”29. Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.30. A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa.31. Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.32. “Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika.33. Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.34. “Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.35. Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.36. Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”37. Kowace rana, Yesu yakan je haikalin ya yi koyarwa, da kowace yamma kuma, ya je ya kwana a kan tudun da ake kira Dutsen Zaitun.38. Da sassafe kuma, dukan mutanen suka zo haikalin, don su saurare shi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.