Baibul a cikin shekara guda Mayu 252 Samaʼila 21:1-221. Lokacin da Dawuda yake mulki, an yi yunwa shekara uku a jere; saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji. Ubangiji ya ce, “Saboda Shawulu ne da alhakin jinin gidansa; domin ya kashe Gibeyonawa.”2. Sai sarki ya tattara Gibeyonawa ya yi musu magana. (To, Gibeyonawa ba sashen Isra’ilawa ba ne, amma mutanen Amoriyawa ne da suka ragu, waɗanda Isra’ila ta rantse za tă bari da rai, amma Shawulu cikin kishinsa don Isra’ila da Yahuda ya yi ƙoƙari yă hallaka su duka.)3. Dawuda ya ce wa Gibeyonawa, “Me zan yi muku? Yaya zan yi kafara domin ku sa wa masu gādon Ubangiji albarka?”4. Gibeyonawa suka ce, “Ba mu da ’yanci mu nemi zinariya ko azurfa daga wurin Shawulu ko gidansa, ba mu kuwa da wani ’yanci mu sa a kashe wani a Isra’ila.” Dawuda ya ce, “To, me kuke so in yi muku?”5. Suka ce wa sarki, “Mutumin da ya hallaka mu ya kuma yi mana makirci don kada mu kasance tare da Isra’ilawa ko’ina a cikin ƙauyukansu,6. a ba mu zuriyarsa maza bakwai, mu kashe su, mu kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji a Gibeya na Shawulu wannan zaɓaɓɓen Ubangiji.” Sai sarki ya ce, “Zan ba ku su.”7. Sarki ya ware Mefiboshet ɗan Yonatan jikan Shawulu, saboda rantsuwar da take tsakanin Dawuda da Yonatan, ɗan Shawulu a gaban Ubangiji.8. Amma sarki ya ɗauki Armoni da Mefiboshet, ’ya’ya biyu maza waɗanda Rizfa ’yar Aiya ta haifa wa Shawulu, tare da ’ya’ya maza biyar na Merab ’yar Shawulu, waɗanda ta haifa wa Adriyel ɗan Barzillai, mutumin Mehola.9. Ya ba da su ga Gibeyonawa, waɗanda suka kashe su, suka kuma rataye jikunansu a gaban Ubangiji. Dukan bakwai ɗin an kashe su gaba ɗaya; an kashe su a farkon kwanankin girbi, daidai lokacin fara girbin sha’ir.10. Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba.11. Da aka gaya wa Dawuda abin da Rizfa ’yar Aiya ƙwarƙwaran Shawulu ta yi,12. sai ya je ya kwashe ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga mutanen Yabesh Gileyad (Gama mutanen sun saci gawawwakin Shawulu da Yonatan daga inda Filistiyawa suka kakkafa su a kan itace a filin Bet-Shan, bayan da Filistiyawa suka kashe su a Gilbowa.)13. Dawuda ya kawo ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan daga can, a kuma aka tattara dukan ƙasusuwan waɗanda Gibeyonawan suka kashe, suka kuma rataye.14. Suka binne ƙasusuwan Shawulu da na ɗansa Yonatan a kabarin Kish, mahaifin Shawulu, a Zela a Benyamin. Suka kuma yi kome da sarki ya umarta. Bayan wannan Allah ya ji addu’arsu a madadin ƙasar.15. Har yanzu yaƙi ya sāke ɓarke tsakanin Filistiyawa da Isra’ila. Sai Dawuda ya gangara tare da mutanensa don su yaƙi Filistiyawa, gajiya ta kama shi.16. Ishbi-Benob kuwa, wani daga zuriyar Rafa, wanda nauyin kan māshinsa na tagulla ya yi shekel ɗari uku, wanda yake kuma da sabon māshi, ya ce zai kashe Dawuda.17. Amma Abishai ɗan Zeruhiya ya kawo wa Dawuda gudummawa; ya bugi Bafilistin, ya kashe shi. Sa’an nan mutanen Dawuda suka rantse masa suka ce, “Ba za ka ƙara fita tare da mu wurin yaƙi ba, don kada fitilar Isra’ila tă mutu.”18. Ana nan, sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa, a Gob. A lokacin Sibbekai mutumin Husha ya kashe Saf, wani daga zuriyar Rafa.19. Sai aka sāke yin wani yaƙin da Filistiyawa a Gob, Elhanan ɗan Ya’are-Oregim mutumin Betlehem ya kashe Goliyat mutumin Gat, wanda girmar sandan māshinsa ta yi kama da taɓarya.20. Har wa yau a wani yaƙin da aka yi a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu, da kuma yatsotsi shida a kowane ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriya Rafa ne.21. Da ya yi wa Isra’ila reni, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwa Dawuda, ya kashe shi.22. Waɗannan huɗu zuriyar Rafa ne a Gat, suka kuwa mutu ta hannu Dawuda da mutanensa.2 Samaʼila 22:1-511. Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.2. Ya ce, “ Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;3. Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni.4. “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.5. Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni; raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.6. Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini.7. “A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa.8. Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, harsashan sararin sama sun jijjigu; suka yi makyarkyata saboda yana fushi.9. Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa; harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa, garwashi mai ƙuna daga bakinsa.10. Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.11. Ya hau kerubobi, ya tashi sama; ya yi firiya a fikafikan iska.12. Ya mai da duhu abin rufuwarsa gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.13. Daga cikin hasken gabansa garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.14. Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama; aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.15. Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba, da walƙiya kuma ya sa suka gudu.16. Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.17. “Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni, ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.18. Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko, daga maƙiyina da suka fi ƙarfina.19. Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni.20. Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.21. “ Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.22. Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.23. Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.24. Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.25. Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.26. “Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,27. ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.28. Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.29. Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.30. Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.31. “Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.32. Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?33. Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.34. Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.35. Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.36. Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.37. Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.38. “Na fafari abokan gābana, na murƙushe su; ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.39. Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba, sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.40. Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.41. Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina.42. Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.43. Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura; na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.44. “Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena; ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai. Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,45. baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci; da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.46. Zukatansu ta karaya; suka fito da rawan jiki daga kagararsu.47. “ Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!48. Shi ne Allahn da yake rama mini, wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina,49. wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina. Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyina; ka kiyaye ni daga hannun mugayen mutane.50. Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai; Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka.51. “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”Zabura 68:1-61. Bari Allah yă tashi, bari a watsar da abokan gābansa; bari maƙiyansa su gudu a gabansa.2. Kamar yadda iska take hura hayaƙi, bari yă hura su haka; kamar yadda kaki kan narke a gaban wuta, bari mugaye su hallaka a gaban Allah.3. Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki.4. Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.5. Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.6. Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.Karin Magana 17:2-42. Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa.3. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.4. Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.Yohanna 8:28-5928. Saboda haka Yesu ya ce, “Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.29. Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”30. Sa’ad da yake cikin magana, da yawa suka ba da gaskiya gare shi.31. Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, “In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.32. Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”33. Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”34. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.35. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.36. Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske.37. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku.38. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”39. Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi.40. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba.41. Kuna yin abubuwan da ubanku yake yi ne.” Suka ce, “Mu fa ba shegu ba ne. Uba guda kaɗai da muke da shi, shi ne Allah kansa.”42. Yesu ya ce musu, “Da Allah ne Ubanku, da kun ƙaunace ni, gama daga Allah na fito yanzu kuma ga ni nan. Ban zo saboda kaina ba, amma shi ne ya aiko ni.43. Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi.44. Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.45. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!46. Akwai waninku da zai iya haƙaƙƙewa na taɓa yin zunubi? In kuwa gaskiya na faɗa, me ya sa ba kwa gaskata ni?47. Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”48. Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Aha, ai, gaskiyarmu da muka ce kai mutumin Samariya ne, kana kuma da aljani.”49. Yesu ya ce, “Ni ba mai aljani ba ne, ni dai ina girmama Ubana, ku kuwa ba kwa girmama ni.50. Ba na nema wa kaina ɗaukaka, amma akwai wani wanda yake neman mini, shi ne kuma alƙali.51. Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”52. Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.53. Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”54. Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.55. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa.56. Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”57. Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”58. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!”59. Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.