Baibul a cikin shekara guda Mayu 262 Samaʼila 23:1-381. Waɗannan su ne kalmomin Dawuda na ƙarshe. “Abubuwan da Dawuda ɗan Yesse ya yi magana a kai, abubuwan da mutumin da Mafi Ɗaukaka ya girmama. Mutumin da Allah na Yaƙub ya zaɓa yă zama sarki, wanda kuma yake mawaƙi waƙoƙin Isra’ila.2. “Ruhun Ubangiji ya yi magana ta wurina; maganarsa tana a harshena.3. Allah na Isra’ila ya yi magana, Dutsen Isra’ila ya ce mini, ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci, sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,4. yana kama da hasken safiya a safiya marar girgije, kamar haske bayan ruwan sama da yakan sa ciyawa ta tsiro daga ƙasa.’5. “Ashe, gidana bai daidaita da Allah ba? Ashe, Allah bai yi madawwamiyar yarjejjeniya da ni shiryayye da ɗaurarre a kowane sashi ba? Ba zai kawo ga cikar cetona yă kuma biya duk bukatuna ba?6. Amma za a jefar da masu mugunta duka kamar ƙayayyuwan da ba a tattara da hannu.7. Duk wanda ya taɓa ƙaya yakan yi amfani da wani ƙarfe ne ko sandar māshi; akan ƙone su inda suke a zube.”8. Waɗannan su ne sunayen jarumawan Dawuda. Yosheb-Basshebet, mutumin Takemon ɗaya daga cikin shugabanni Uku; ya ɗaga māshinsa ya kashe mutum ɗari takwas a lokaci guda.9. Na biye da shi a matsayi cikin jarumawa ukun nan, shi ne Eleyazar ɗan Dodo, mutumin Aho. Eleyazar ya kasance tare da Dawuda sa’ad da suka fuskanci Filistiyawa waɗanda suka taru a Fas Dammim don yaƙi. Mutanen Isra’ila suka gudu,10. amma ya yi tsayi daka, ya bugi Filistiyawa sai da hannunsa ya gaji har ya liƙe wa māshinsa. Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara a ranar. Sauran sojoji suka komo wurin Eleyazar, don kawai su washe ganima.11. Na biye da Agiyi a matsayi, shi ne Shamma ɗan Agi, mutumin Harar. Sa’ad da Filistiyawa suka taru a wani wurin da take gona cike da waken barewa, sai rundunar Isra’ila suka gudu daga Filistiyawa.12. Amma Shamma ya yi tsayi daka a tsakiyar gonar. Ya kāre ta, ya kuma bugi Filistiyawa, Ubangiji kuwa ya sa aka yi babban nasara.13. A lokacin girbi, uku daga cikin shugabanni talatin suka gangaro zuwa wurin Dawuda a kogon Adullam. A lokacin kuwa sojojin Filistiyawa sun kafa sansani a Kwarin Refayim.14. Dawuda kuwa yana a mafaka. Wata ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuma suna Betlehem.15. Dawuda ya ji ƙishirwa, sai ya ce, “Kash, da a ce wani yă samo mini ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem mana!”16. Sai jarumawa ukun nan suka yi kukan ƙura, suka sheƙa a guje suka ratsa cikin sansanin Filistiyawa, suka ɗebo ruwa daga rijiyar da take kusa da bakin ƙofar Betlehem, suka kawo wa Dawuda. Amma Dawuda ya ƙi yă sha; a maimako sai ya zuba shi a gaban Ubangiji.17. Sai ya ce, “ Ubangiji yă sawwaƙe, in yi sha! Ba jinin mutanen da suka tafi a bakin ransu ba ne?” Dawuda kuwa bai sha ruwan ba. Irin abubuwan da jarumawa ukun nan suka yi ke nan.18. Abishai, ɗan’uwan Yowab, ɗan Zeruhiya shi shugaban Ukun nan. Ya ɗauki māshinsa ya kashe mutane ɗari uku, ta haka ya zama sananne kamar Ukun nan.19. Ashe, ba a girmama shi fiye da Ukun ba? Ya zama komandansu, ko da yake ba a haɗa shi a cikinsu ba.20. Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.21. Ya kuma buge wani jibgaggen mutumin Masar. Duk da māshin da mutumin Masar yana riƙe a hannunsa, Benahiya ya kai masa hari da kulki. Ya ƙwace māshin daga hannunsa, ya kuma kashe shi da māshin.22. Irin nasarorin da Benahiya ɗan Yehohiyada ya yi ke nan; shi ma jarumi ne sosai kamar jarumawan nan uku.23. Aka fi ba shi girma fiye da talatin ɗin nan, amma ba ya cikin ukun. Dawuda ya sa shi yă zama ɗaya daga cikin masu tsaron lafiyarsa.24. Cikin talatin ɗin kuwa akwai, Asahel, ɗan’uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo mutumin Betlehem,25. Shamma, mutumin Harod, Elika, mutumin Harod,26. Helez, mutumin Falti, Ira, ɗan Ikkesh mutumin Tekowa,27. Abiyezer, mutumin Anatot, da Mebunnai, mutumin Husha,28. Zalmon, mutumin Aho, da Maharai, mutumin Netofa,29. Heleb, ɗan Ba’ana daga Netofa, Ittai, ɗan Ribai mutumin Gibeya a Benyamin,30. Benahiya, mutumin Firaton, da Hiddai, daga rafuffukan Ga’ash,31. Abi-Albon, mutumin Arba, da Azmawet, mutumin Bahurim,32. Eliyaba, mutumin Sha’albo, ’Ya’yan Yashen, Yonatan,33. ɗan Shamma mutumin Harar, da Ahiyam, ɗan Sharar mutumin Harod.34. Elifelet, ɗan Ahasbai mutumin Ma’aka, Eliyam, ɗan Ahitofel mutumin Gilo,35. Hezro, mutumin Karmel, Fa’arai, mutumin Arbi,36. Igal, ɗan Natan mutumin Zoba, ɗan Hagiri,37. Zelek, mutumin Ammon Naharai, mutumin Beyerot mai ɗaukan wa Yowab, ɗan Zeruhiya makamai,38. Ira, mutumin Itra. Gareb, mutumin Itra,2 Samaʼila 24:1-251. Fushin Ubangiji ya sāke ƙuna a kan Isra’ila, sai ya zuga Dawuda, yana cewa, “Je ka ƙidaya Isra’ila da Yahuda.”2. Saboda haka sarki ya ce wa Yowab da komandodin da suke tare da shi, “Tafi cikin dukan kabilan Isra’ila, daga Dan har zuwa Beyersheba, ku ƙidaya mayaƙa don in san yawansu.”3. Amma Yowab ya ce wa sarki, “ Ubangiji Allahnka ya sa mayaƙan su ƙaru sau ɗari fiye da yadda suke, har ranka yă daɗe, sarki yă gani da idonsa. Me ya sa ranka yă daɗe, sarki yake so yă yi abu haka?”4. Duk da haka, maganar sarki ya rinjayi Yowab da komandodin soja, sai suka tashi daga gaban sarki, suka tafi su ƙirga mayaƙan Isra’ila.5. Bayan suka ƙetare Urdun, sai suka yi sansani kusa da Arower, kudu da garin da yake cikin kwari, sa’an nan suka ratsa ta wajen Gad, suka ci gaba zuwa Yazer.6. Suka tafi Gileyad ta yankin Tatim Hodshi, sa’an nan suka tafi Dan Ya’an, suka kuma yi wajen kewaye Sidon.7. Sa’an nan suka yi ta wajen kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa da Kan’aniyawa. A ƙarshe, suka ci gaba zuwa Beyersheba a Negeb na Yahuda.8. Bayan suka ratsa dukan ƙasashen, a ƙarshe suka koma Urushalima, bayan wata tara da kwana ashirin.9. Yowab ya ba wa sarki jimillar yawan mayaƙan. A Isra’ila akwai mutum dubu ɗari takwas da za su iya riƙe takobi. A Yahuda kuwa mutum dubu ɗari biyar.10. Bayan Dawuda ya ƙidaya mayaƙan, lamirinsa ya kāshe shi, sai ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji na yi laifi ƙwarai a kan abin da na yi. Ina roƙonka ka gafarta wa bawanka. Na yi wauta ƙwarai.”11. Kafin Dawuda yă tashi da safe kashegari, maganar Ubangiji ta riga ta zo wa annabin nan Gad, mai duban nan na Dawuda. Ubangiji ya ce,12. “Je ka faɗa wa Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, ina ba ka zaɓi uku. Ka zaɓi ɗaya daga cikinsu don in aikata maka shi.’ ”13. Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gābanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu, sai ka yi tunani, ka yanke shawarar game da amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”14. Dawuda ya ce wa Gad, “Na shiga uku. Gara mu fāɗa a hannuwan Ubangiji gama alherinsa da girma yake. Amma fa kada ka bar ni in fāɗa a hannun mutane.”15. Saboda haka Ubangiji ya aika da annoba a kan Isra’ila tun daga safe har zuwa lokacin da aka ƙayyade, mutum dubu saba’in kuwa daga Dan zuwa Beyersheba suka mutu.16. Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus.17. Da Dawuda ya ga mala’ikan da ya bubbugi mutane, sai ya ce wa Ubangiji, “Ni ne na yi zunubi, na kuma yi abin da ba daidai ba. Waɗannan tumaki ne kawai. Me suka yi? Bari hukuncinka yă sauko a kaina da iyalina.”18. A ranar, Gad ya koma wurin Dawuda ya ce, “Ka tashi, ka tafi ka gina wa Ubangiji bagade a masussukar Arauna, mutumin Yebus.”19. Saboda haka Dawuda ya haura, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Gad.20. Da Arauna ya hangi Dawuda da mutanensa suna zuwa wajensa, sai ya fita a guje, ya je ya rusuna a gaban sarki.21. Arauna ya ce, “Me ya sa ranka yă daɗe, sarki ya zo wajen bawansa?” Dawuda ya ce, “Don in saya masussukarka, saboda in gina wa Ubangiji bagade don a tsayar da annoban da suke a bisa mutane.”22. Arauna ya ce wa Dawuda, “Bari ranka yă daɗe, sarki yă ɗauki duk abin da ya ga dama yă miƙa shi. Ga shanu, don hadaya ta ƙonawa, ga kuma kayan masussuka da itacen shanu, don itace.”23. Dukan wannan, ranka yă daɗe, Arauna ya ba wa sarki. Arauna ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahnka yă karɓa.”24. Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa.25. Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.Zabura 68:7-107. Sa’ad da ka fito a gaban mutanenka, ya Allah, sa’ad da ka taka ta cikin ƙasar da take wofi,8. duniya ta girgiza, sammai suka zuba ruwan sama, a gaban Allah, wanda ya bayyana a Sinai, a gaban Allah, Allah na Isra’ila.9. Ka ba da yayyafi a yalwace, ya Allah; ka rayar da gādonka da ya gāji.10. Mutanenka suka zauna a cikinsa, kuma daga yalwarka, ya Allah, ka tanada wa matalauta.Karin Magana 17:5-65. Duk wanda yake wa matalauta ba’a yana zagin Mahaliccinsu ne; duk wanda ya yi murna akan masifar da ta sami wani za a hukunta shi.6. Jikoki rawanin tsofaffi ne, kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.Yohanna 9:1-231. Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho.2. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?”3. Sai Yesu ya ce, “Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.4. Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.5. Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”6. Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin.7. Ya ce masa, “Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam” (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.8. Maƙwabta da waɗanda suka saba ganinsa dā yana bara, suka ce, “Kai, ba wannan mutum ne ya saba zama yana bara ba?”9. Waɗansu suka ce shi mana. Waɗansu kuwa suka ce, “A’a, ya dai yi kama da shi.” Amma shi ɗin ya ce, “Ƙwarai kuwa ni ne.”10. Sai suka ce, “To, yaya aka yi idanunka suka buɗe?”11. Ya amsa ya ce, “Mutumin da ake kira Yesu ne ya kwaɓa laka ya shafa mini a idanu. Ya ce mini in je Silowam in wanke. Na kuwa tafi, na wanke, sai na sami ganin gari.”12. Suka tambaye shi suka ce, “Ina mutumin yake?” Ya ce, “Ban sani ba.”13. Sai suka kawo mutumin da dā yake makaho wurin Farisiyawa.14. To, a ranar da Yesu ya kwaɓa laka ya buɗe idanun mutumin ranar Asabbaci ce.15. Saboda haka Farisiyawa suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Mutumin ya amsa, “Ya shafa laka a idanuna, sai na wanke, ina kuwa gani.”16. Sai waɗansu daga cikin Farisiyawa suka ce, “Mutumin nan ba daga Allah yake ba, don ba ya kiyaye ranar Asabbaci.” Amma waɗansu suka yi tambaya suka ce, “Yaya mutum mai zunubi zai yi irin abubuwan banmamaki haka?” Sai ra’ayinsu ya sha bamban.17. A ƙarshe suka sāke koma ga makahon suka ce, “Kai fa, me ka gani game da shi? Idanunka ne fa ya buɗe.” Sai mutumin ya ce, “Tab, ai, shi annabi ne.”18. Yahudawa dai ba su yarda cewa dā shi makaho ne ya kuma sami ganin gari ba, sai da suka kira iyayen mutumin.19. Suka tambaye su, “Wannan ɗanku ne? Shi ne wanda kuka ce an haife shi makaho? To, ta yaya yake gani yanzu?”20. Iyayen suka amsa suka ce, “Mun dai san shi ɗanmu ne, mun kuma san cewa an haife shi makaho.21. Sai dai yadda yake gani yanzu, ko kuma wa ya buɗe idanunsa, ba mu sani ba. Ku tambaye shi. Ai, shi ba yaro ba ne, zai faɗa da bakinsa.”22. Iyayensa sun faɗa haka ne saboda suna tsoron Yahudawa, gama Yahudawa sun riga sun yanke shawara cewa duk wanda ya yarda cewa Yesu shi ne Kiristi, za a kore shi daga majami’a.23. Shi ya sa iyayensa suka ce, “Ai, shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.