Baibul a cikin shekara guda Mayu 281 Sarakuna 3:1-281. Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.2. A lokacin dai mutane suna miƙa hadaya a wurare a bisa tuddai, domin ba a riga an gina haikali saboda Sunan Ubangiji ba.3. Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai.4. Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.5. A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.”6. Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.7. “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba.8. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta.9. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?”10. Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan.11. Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya,12. zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.13. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna.14. In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”15. Sai Solomon ya farka, ya gane ashe mafarki ne. Ya koma Urushalima, ya tsaya a gaban akwatin alkawarin Ubangiji ya miƙa hadayun ƙonawa da hadayun salama. Sa’an nan ya shirya wa fadawansa biki.16. To, ana nan sai waɗansu karuwai biyu suka zo wurin sarki, suka tsaya a gabansa.17. Sai ɗaya ta ce, “Ranka yă daɗe, wannan mata da ni muna zama a gida ɗaya. Na haifi jariri yayinda take can tare da ni.18. Kwana uku bayan haihuwar jaririna, wannan mata ma ta haifi jariri. Mu dai kaɗai ne; babu wani a gidan sai mu biyu.19. “Da dare ɗan wannan matan ya mutu domin ta kwanta a kansa.20. Saboda haka ta tashi da tsakar dare ta ɗauki ɗana daga gefena yayinda baiwarka take barci. Sai ta sa shi kusa da ƙirjinta, ta kuma sa mataccen ɗanta kusa da ƙirjina.21. Kashegari, da na farka don in shayar da ɗana, sai na tarar ya mutu! Amma sa’ad da na dube shi da kyau da safe, sai na ga ashe ba ɗan da na haifa ba ne.”22. Amma ɗaya matar ta ce, “A’a! Mai rai ɗin ne ɗana; mataccen naki ne.” Amma ta farin ta nace, “A’a! Mataccen ne naki; mai ran ne nawa.” A haka suka yi ta gardama a gaban sarki.23. Sarki ya ce, “Wannan ta ce, ‘Ɗana ne a raye, naki ne matacce,’ yayinda ɗayan tana cewa, ‘A’a! Ɗanki ne mataccen, nawa ne a raye.’ ”24. Sai sarki ya ce, “Kawo mini takobi.” Sai aka kawo takobi wa sarki.25. Ya ba da umarni ya ce, “Yanka yaron nan mai rai, gida biyu, kowacce ta ɗauki rabi.”26. Ainihin mamar ɗan da yake a raye ta cika da tausayi saboda ɗanta, sai ta ce wa sarki, “Ina roƙonka, ranka yă daɗe, kada ka kashe yaron! Ka ba ta kawai!” Amma ɗayan matar ta ce, “Kada a ba kowa daga cikinmu ɗan da rai, a ci gaba a raba shi!”27. Sai sarki ya zartar da hukuncinsa ya ce, “A ba da jariri mai ran ga mata ta fari. Kada a kashe shi; ita ce ainihin mahaifiyarsa.”28. Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.1 Sarakuna 4:1-341. Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila.2. Waɗannan su ne manyan shugabanninsa. Azariya ɗan Zadok shi ne firist;3. Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.4. Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa. Zadok da Abiyatar, su ne firistoci.5. Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki. Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara.6. Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.7. Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.8. Ga sunayensu, Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;9. Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;10. Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);11. Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);12. Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;13. Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);14. Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;15. Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);16. Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;17. Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;18. Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;19. Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.20. Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki.21. Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa.22. Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci,23. shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.24. Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe.25. A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa.26. Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu, da kuma dawakai dubu goma sha biyu27. Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba.28. Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su.29. Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku.30. Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma.31. Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye.32. Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar.33. Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi.34. Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.Zabura 68:15-2015. Duwatsun Bashan, duwatsu masu alfarma ne; duwatsun Bashan masu wuyar hawa ne.16. Don me kuke duba da kishi, ya duwatsu masu wuyan hawa, a kan dutsen da Allah ya zaɓa yă yi mulki, inda Ubangiji kansa zai zauna har abada?17. Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.18. Sa’ad da ka hau bisa, ka bi da kamammu cikin tawagarka; ka karɓi kyautai daga mutane, har ma daga ’yan tawaye, don kai, ya Ubangiji Allah, za ka zauna a can.19. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu.20. Allahnmu shi ne Allah wanda yake ceto; daga Ubangiji Mai Iko Duka kuɓuta yake zuwa daga mutuwa.Karin Magana 17:10-1210. Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.11. Mugayen mutane sukan kuta tawaye da Allah; za a aika manzo mutuwa a kansu.12. Gara a haɗu da beyar da aka ƙwace wa ’ya’ya fiye da a sadu da wawa cikin wautarsa.Yohanna 10:1-231. “Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.2. Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.3. Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje.4. Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.5. Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”6. Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.7. Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.8. Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba.9. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo.10. Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.11. “Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.12. Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.13. Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.14. “Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni,15. kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.16. Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.17. Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.18. Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”19. Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa.20. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”21. Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”22. Bikin Miƙawa a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa.23. Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon, Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.