Baibul a cikin shekara guda Mayu 291 Sarakuna 5:1-181. Sa’ad da Hiram sarkin Taya ya ji an shafe Solomon sarki yă gāji mahaifinsa Dawuda, sai ya aika da jakadunsa zuwa wurin Solomon, gama shi da Dawuda abokai ne sosai dukan kwanakinsa.2. Solomon ya mayar da wannan saƙo ga Hiram ya ce,3. “Ka san cewa saboda yaƙe-yaƙen da abokan gāba suka yi da mahaifina a kowane gefe, ya sa bai iya gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahnsa ba, sai da Ubangiji ya sa abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.4. Amma yanzu Ubangiji Allahna ya ba ni hutu a kowane gefe, babu kuma gāba ko masifa.5. Ina niyya in gina haikali domin Sunan Ubangiji Allahna, yadda Ubangiji ya faɗa wa mahaifina Dawuda, sa’ad da ya ce, ‘Ɗanka wanda zai gāje ka, shi zai gina haikali domin Sunana.’6. “Don haka, ka ba da umarni a yanka mini itatuwan al’ul na ƙasar Lebanon. Ma’aikatana za su haɗa hannu da ma’aikatanka, ni kuwa zan biya ka albashin ma’aikatanka kamar yadda ka faɗa. Gama ka san cewa babu wani a cikinmu da ya iya yanka itacen katako kamar Sidoniyawa.”7. Da Hiram ya ji saƙon Solomon, sai ya ji daɗi ƙwarai, ya kuma ce, “Yabo ga Ubangiji a yau, gama ya ba wa Dawuda ɗa mai hikima yă yi mulki a bisa wannan al’umma mai girma.”8. Sai Hiram ya aike wa Solomon da kalmomin nan, “Na sami saƙon da ka aika mini, zan kuma yi duk abin da kake so ta wurin tanada katakan al’ul da na fir.9. Ma’aikatana za su gangara da su daga Lebanon zuwa bakin teku. Zan sa a ɗaɗɗaura su su bi ruwan teku daga Lebanon zuwa bakin Bahar Rum da za ka nuna mini. A can zan kunce maka su, sa’an nan ka kwashe. Kai kuma za ka biya bukatata ta wurin tanadin abinci wa gidana.”10. A haka Hiram ya ci gaba da aika wa Solomon al’ul da kuma fir da yake bukata.11. Solomon kuma ya ba wa Hiram mudu gari dubu ashirin na alkama a matsayin abinci domin gidansa, ya ƙara da garwa dubu ashirin na tataccen man zaitun. Solomon ya ci gaba da yin haka ga Hiram, shekara-shekara.12. Ubangiji ya ba wa Solomon hikima, kamar yadda ya yi masa alkawari. Dangantakar zaman lafiya ta kasance tsakanin Hiram da Solomon, su biyun suka yi yarjejjeniya.13. Sarki Solomon ya ɗebi ma’aikata daga dukan Isra’ila, su dubu talatin.14. Ya riƙa aika su dubu goma-goma zuwa Lebanon kowane wata, saboda su yi wata ɗaya a Lebanon, watanni biyu kuma a gida. Adoniram ne ya lura da aikin gandun.15. Solomon ya kasance da ’yan ɗauko guda dubu saba’in da masu yankan duwatsu guda dubu tamanin a cikin tuddai,16. ya kuma kasance da shugabanni dubu uku da ɗari uku waɗanda suke lura da aikin, su ne kuma suke bi da ma’aikatan.17. Bisa ga umarnin sarki sai suka cire manyan duwatsu masu kyau don a tanada tushen duwatsun da aka gyara domin haikalin daga wurin haƙar duwatsun.18. Gwanayen Solomon da na Hiram da kuma mutanen Gebal, su suka yanka, suka kuma shirya katako da dutse don ginin haikali.1 Sarakuna 6:1-381. A shekara ta ɗari huɗu da tamani bayan fitowar Isra’ilawa daga Masar, a shekara ta huɗu ta mulkin Solomon a bisa Isra’ila, a watan Zif, wata na biyu, Solomon ya fara gina haikalin Ubangiji.2. Haikalin da Sarki Solomon ya gina wa Ubangiji, tsawonsa kamu sittin, fāɗinsa kamu ashirin, tsayinsa kuma kamu talatin ne.3. Shirayin da yake a gaban ainihin zauren haikalin, ya ƙara faɗin haikalin da kamu ashirin, ya kuma nausa daga gaban haikalin kamu goma.4. Ya yi tagogin da suka fi fāɗi daga ciki fiye da waje a haikalin.5. A jikin bangayen babban zaure da kuma cikin wuri mai tsarki, ya gina ɗakuna kewaye da ginin, inda akwai ɗakuna a gefe.6. Fāɗin ɗakunan ƙasa, kamu biyar ne, fāɗin ɗakunan tsakiya, kamu shida ne, fāɗin ɗakunan hawa na uku kuwa, kamu bakwai ne. Ya yi bangaye kewaye a waje da haikalin don kada a sa wani abu a bangayen haikali.7. A yin ginin haikalin, duwatsun da aka fafe ne kaɗai daga wurin fafe duwatsu aka yi amfani da su, ba a ji karar guduma ko gizago, ko wani abin da aka yi da ƙarfe a wurin ginin haikali yayinda ake gina shi ba.8. Ƙofar zuwa ɗakunan ƙasa tana gefen kudu na haikalin; akwai matakai da suka bi zuwa hawa na tsakiya, daga can kuma matakan sun wuce zuwa hawa na uku.9. A haka ya gina haikalin ya kuma gama shi, ya jinƙe shi da manyan katakai da kuma katakan al’ul.10. Ya kuma gina ɗakunan gefe duka a gefen haikalin. Tsayin kowanne, kamu biyar ne, aka haɗa su da haikalin da manyan katakan al’ul.11. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Solomon ta ce,12. “Game da wannan haikalin da kake ginawa, in ka bi ƙa’idodina, ka cika farillaina, ka kiyaye dukan umarnaina, ka kuma yi biyayya da su, zan cika alkawarin da na yi wa mahaifinka Dawuda ta wurinka.13. Zan kuma zauna a cikin Isra’ilawa, ba kuwa zan taɓa rabuwa da su ba.”14. Saboda haka Solomon ya gina haikalin ya kuma gama shi.15. Ya rufe bangon ciki da katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama, ya kuma rufe daɓen da katakan itacen fir.16. Ya gina Wuri Mafi Tsarki na can ciki, ya gina shi a can ƙuryar haikalin. Tsayinsa kamu ashirin ne, an manne masa katakan itacen al’ul tun daga ƙasa har zuwa sama.17. Tsawon babban zaure a gaban wannan ɗaki, kamu arba’in ne.18. An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.19. Ya shirya wuri mai tsarki na ciki can cikin haikali don yă sa akwatin alkawarin Ubangiji a can.20. Tsawon wuri mai tsarki na ciki kamu ashirin, fāɗin kamu ashirin, tsayin kuma kamu ashirin. Ya dalaye cikin da zinariya zalla, ya kuma dalaye bagade al’ul ɗin.21. Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya.22. Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya.23. A wuri mai tsarki na can ciki, ya yi kerubobi biyu na itacen zaitun, kowanne mai tsayi kamu goma.24. Fiffike ɗaya na kerub na fari tsawonsa kamu biyar ne, ɗayan fiffike kuma kamu biyar, kamu goma daga ƙarshen fiffike zuwa ƙarshen fiffike.25. Kerub na biyun shi ma kamu goma ne, gama kerubobi biyun sun yi kama da juna a girma da kuma siffa.26. Tsayin kowane kerub kamu goma ne.27. Ya ajiye kerubobin a ɗaki na can cikin haikalin, da fikafikansu a buɗe. Fiffiken kerub ɗaya ya taɓa bango guda, yayinda fiffiken ɗayan ya taɓa ɗayan bangon, kuma fikafikansu sun taɓa juna a tsakiyar ɗakin.28. Ya dalaye kerubobin da zinariya.29. A bangaye kewaye da haikali, a ɗakuna ciki da waje, ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da furanni buɗaɗɗu.30. Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya.31. Don ƙofar shiga wuri mai tsarki na ciki kuwa, ya yi ƙofofin katakon zaitun da madogarai masu gefe biyar.32. A kan ƙofofin katakan zaitun kuwa ya zāzzāna kerubobi, itatuwa dabino, da furanni buɗaɗɗu, ya kuma dalaye kerubobin, da kuma itatuwan dabinon da zinariya.33. Haka ma ya yi madogarai masu gefe huɗu na katakon zaitun don ƙofar shiga zuwa babban zaure.34. Ya yi ƙofofi biyu na itacen fir, kowanne yana da shafi biyu da suke juyewa a maɗaurai.35. Ya zāzzāna kerubobi, itatuwan dabino, da kuma furanni buɗaɗɗu a kansu, ya kuma dalaye su da zinariyar da aka buga daidai a kan sassaƙa.36. Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.37. An kafa tushen haikalin Ubangiji a shekara ta huɗu, a watan Zif.38. A shekara ta goma sha ɗaya, a watan Bul, wata na takwas ke nan, aka gama haikalin daidai yadda aka tsara shi bisa ga fasalinsa. Solomon ya ɗauki shekara bakwai yana ginin haikalin.Zabura 68:21-2721. Tabbatacce Allah zai murƙushe kawunan abokan gābansa, rawanin gashi na waɗanda suke ci gaba cikin zunubansa.22. Ubangiji ya ce, “Zan kawo su daga Bashan; zan kawo su daga zurfafan teku,23. don ku wanke ƙafafunku a cikin jinin maƙiyanku, yayinda harsunan karnukanku su sami rabonsu.”24. Jerin gwanonka ya zo a bayyane, ya Allah, jerin gwanon Allahna da Sarkina zuwa cikin wuri mai tsarki.25. A gaba akwai mawaƙa, a bayansu akwai makaɗa; tare da su akwai ’yan mata suna bugan ganguna.26. Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.27. Ga ƙaramar kabilar Benyamin, suna jagorance su, ga babbar ƙungiya shugabannin Yahuda, ga kuma shugabannin Zebulun da na Naftali.Karin Magana 17:13-1513. In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.14. Farawar faɗa tana kamar ɓarkewa madatsar ruwa ne, saboda haka ka bar batun kafin faɗa ta ɓarke.15. Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.Yohanna 10:24-4224. sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”25. Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.26. Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.27. Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.28. Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.29. Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.30. Da ni da Uba ɗaya ne.”31. Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi,32. amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”33. Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”34. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’?35. Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’36. to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’37. In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni.38. Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.”39. Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.40. Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna41. mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”42. A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.