Baibul a cikin shekara guda Mayu 31 Samaʼila 8:1-221. Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.2. Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba.3. Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.4. Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.5. Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”6. Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.7. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.8. Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka.9. Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”10. Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.11. Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa.12. Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.13. Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.14. Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa.15. Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa.16. Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki.17. Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa.18. Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”19. Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”20. Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.21. Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.22. Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”1 Samaʼila 9:1-271. An yi wani mutum, attajiri daga kabilar Benyamin, sunansa Kish, ɗan Abiyel, jikan Zeror na iyalin Bekorat daga dangin Afiya.2. Yana da ɗa mai suna Shawulu, wani kyakkyawan saurayi. A cikin mutanen Isra’ila ba wanda ya fi shi kyau, ya kuma fi kowa tsaye.3. To, ana nan sai jakunan Kish mahaifin Shawulu suka ɓace. Kish ya ce wa ɗansa, “Tashi ka tafi tare da wani daga cikin bayi, ku nemo jakunan.”4. Suka bi ta ƙasar tudu ta Efraim, suka ratsa ta ƙasar Shalisha amma ba su same su ba. Suka bi ta ƙasar Shalim, a can ma ba su same su ba sai suka bi ta ƙasar Benyamin, a can ma ba su same su ba.5. Da suka iso gunduman Zuf, sai Shawulu ya ce wa bawan da yake tare da shi, “Zo mu koma kada mahaifina yă bar damuwa a kan jakuna, yă shiga damuwa game da mu.”6. Amma bawan ya amsa ya ce, “Duba, a wannan gari akwai wani mutumin Allah, ana ganin girmansa ƙwarai kuma duk abin da ya faɗa yakan zama gaskiya. Mu tafi can wurinsa wataƙila zai gaya mana hanyar da za mu bi.”7. Shawulu ya ce wa bawan, “Idan muka isa can, me za mu ba wa mutumin? Ga shi abinci guzurinmu duk ya ƙare, ba mu da wani abin da za mu kai wa mutumin Allahn nan. Me muke da shi?”8. Bawan ya sāke ce masa, “Duba ina da kwatar azurfar da zan ba wa mutumin Allah don yă gaya mana wace hanya ce za mu bi.”9. (A dā a Isra’ila, in wani yana so yă nemi nufin Allah, mutumin yakan ce, “Zo mu tafi wajen mai duba.” Gama wanda ake ce da shi annabi a yanzu, a dā ana kiransa mai duba ne.)10. Shawulu ya ce wa bawansa, “Madalla, zo mu tafi.” Sai suka kama hanya suka nufi birnin da mutumin Allah yake.11. Sa’ad da suke haura tudun zuwa birnin, sai suka sadu da waɗansu ’yan mata sun fito za su ɗiban ruwa. Sai suka tambaye su, suka ce, “Mai duba yana nan?”12. ’Yan matan suka ce, “I, yana nan, ai, ga shi ma a gabanku, ku hanzarta. Shigowarsa ke nan a garin, domin yau mutane za su ba da sadaka a bagade a kan tudu.13. Da zarar kun shiga garin, za ku same shi kafin yă tafi cin abinci a wurin yin sadakar, can kan tudu. Gama jama’a ba za su ci ba, sai ya kai can ya sa albarka a sadakar, sa’an nan waɗanda aka gayyata su ci. Ku haura da sauri, za ku same.”14. Suka haura zuwa birnin, da shigarsu sai ga Sama’ila ya nufo su a hanyarsa ta zuwa kan tudu.15. Kafin zuwa Shawulu, Ubangiji ya riga ya bayyana wa Sama’ila ya ce,16. “Gobe war haka zan aiko maka da wani mutum daga ƙasar Benyamin. Ka keɓe shi shugaban mutanena Isra’ila. Shi zai cece mutanena daga hannun Filistiyawa. Na ga azabar mutanena gama kukansu ya hauro wurina.”17. Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.”18. Shawulu ya sami Sama’ila a hanyar shiga gari, sai ya tambaye shi ya ce, “Ina roƙonka ka nuna mini gidan mai duba?”19. Sama’ila ya ce, “Ni ne mai duban, ka yi gaba zuwa ka tudu, gama yau za ka ci tare da ni, da safe kuma in sallame ka, in gaya muku duk abin da yake a zuciyarku.20. Game da jakunan da suka ɓace kwana uku kuwa, kada ka damu, an same su. Ga wane ne Isra’ila ta sa dukan zuciya, in ba ga kai da kuma dukan iyalin mahaifinka ba?”21. Shawulu ya ce, “Ashe, ni ba mutumin Benyamin ba ne daga ƙaramar kabila ta Isra’ila? Dangina kuma ba shi ba ne mafi kakanni a cikin kabilar Benyamin ba? Yaya za ka faɗa mini irin wannan magana.”22. Sa’an nan Sama’ila ya shiga da Shawulu da baransa ya zaunar da su a gaban waɗanda aka gayyata, mutanen sun kai wajen mutum talatin.23. Sama’ila ya ce wa mai dahuwa, “Kawo naman da na ba ka, wannan da na ce ka ajiye dabam.”24. Sai mai dahuwan ya ɗauko cinya da abin da yake bisanta ya kawo ya ajiye a gaban Shawulu. Sama’ila ya ce, “Ga abin da aka ajiye dominka. Ka ci, gama an keɓe shi dominka saboda wannan hidima daga lokacin da na ce, ‘Na gayyaci baƙi.’ ” Shawulu kuwa ya ci tare da Sama’ila a ranan nan.25. Bayan suka gangaro daga tudu zuwa cikin gari, Sai Sama’ila ya yi magana da Shawulu a ɗakin samansa.26. Da asuba sai suka tashi, Sama’ila ya kira Shawulu daga ɗakin sama ya ce, “Ka shirya, zan sallame ka.” Da Shawulu ya shirya, sai Sama’ila da Shawulu suka fita waje tare.27. Suna dab da ƙarshen gari, sai Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Ka ce wa bawanka yă yi gaba, kai ka ɗan dakata a nan tukuna, domin in ba ka saƙo daga Allah.”Zabura 55:9-159. Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.10. Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta.11. Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.12. Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.13. Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,14. wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.15. Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.Karin Magana 15:15-1715. Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.16. Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala.17. Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.Luka 22:1-231. Yanzu fa, Bikin Burodi Marar Yistin da ake kira Bikin Ƙetarewa ya yi kusa,2. manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.3. Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun.4. Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.5. Suka kuwa yi murna, suka yarda su ba shi kuɗi.6. Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.7. Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa.8. Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.”9. Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?”10. Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga.11. Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’12. Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.”13. Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.14. Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.15. Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala.16. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”17. Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku.18. Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”19. Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”20. Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.21. Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.22. Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.”23. Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.