Baibul a cikin shekara guda Mayu 41 Samaʼila 10:1-271. Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “ Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa.2. Sa’ad da ka rabu da ni yau, za ka sadu da mutum biyu kusa da kabarin Rahila a Zelza, a yankin Benyamin. Za su ce maka, ‘An sami jakunan da ka fita nema, yanzu haka mahaifinka ya bar damuwa kan jakunan ya koma damuwa a kanka, yana cewa, yaya zan gan ɗana?’3. “Sa’an nan za ka ci gaba daga nan sai ka kai wajen babban itace na Tabor. Waɗansu mutum uku za su sadu da kai a hanyarsu zuwa wurin yin wa Allah sujada a Betel. Ɗaya yana ɗauke da ’yan awaki uku, ɗaya yana ɗauke da burodi uku, ɗayan kuma yana ɗauke da salkar ruwan inabi.4. Za su gaishe ka, su ba ka burodi biyu, kai kuwa sai ka karɓa.5. “Bayan wannan, za ka tafi Gebiya ta Allah, inda sansanin Filistiyawa yake. Kana shiga garin, za ka sadu da jerin gwanon annabawa suna gangarowa daga tudu, ana kaɗa garaya, ana bugan ganguna, ana hura sarewa, ana kuma bugan molo, a gabansu, su kuma za su yi ta annabci.6. Ruhun Ubangiji zai sauko a kanka da iko, za ka kuma yi annabci tare da su. Za a canja ka ka zama dabam.7. Da zarar waɗannan alamu sun cika, sai ka aikata duk abin da kana iya yi gama Allah yana tare da kai.8. “Ka sha gabana zuwa Gilgal. Lalle zan gangara wurinka domin in miƙa hadaya ta ƙonawa da hadayu na salama. Sai ka jira ni kwana bakwai sai na zo wurinka na kuma gaya maka abin da za ka yi.”9. Da Shawulu ya juya zai bar Sama’ila, sai Allah ya canja wa Shawulu zuciya, alamun nan kuwa suka cika a ranar.10. Da suka iso Gibeya, jerin gwanon annabawa suka sadu da shi Ruhun Allah kuma ya sauko a kansa da iko, sai ya shiga yin annabci tare da su.11. Sa’ad da dukan waɗanda suka san shi a dā suka gan shi yana annabci tare da annabawa, sai suka tambayi juna, suka ce, “Me ya faru da ɗan Kish? Shawulu ma yana cikin annabawa ne?”12. Wani mutumin da yake zama a can ya ce, “Wane ne kuma mahaifinsu?” Ta haka sai wannan ya zama karin magana cewa, “Shawulu ma yana cikin annabawa?”13. Bayan da Shawulu ya gama annabci sai ya haura ya tafi tudu.14. Sai ɗan’uwan mahaifin Shawulu ya tambaye shi da baransa ya ce, “Ina kuka je?” Shawulu ya ce, “Mun tafi neman jakuna, amma da ba mu same su ba sai muka tafi wurin Sama’ila.”15. Ɗan’uwan mahaifin Shawulu ya ce, “Faɗa mini abin da Sama’ila ya ce maka.”16. Shawulu ya ce, “Ya tabbatar mana cewa an riga an sami jakuna.” Amma bai gaya wa ɗan’uwan mahaifinsa abin da Sama’ila ya ce game da sarauta ba.17. Sama’ila ta tattara mutanen Isra’ila a gaban Ubangiji a Mizfa18. ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na fito da Isra’ila daga Masar, na kuma cece ku daga hannun Masarawa da dukan mulkokin da suka wahalshe ku.’19. Amma yanzu kun ƙi Allahnku wanda ya cece ku daga dukan masifu da wahaloli. Kuka ce, ‘Sam, a naɗa mana sarki.’ Saboda haka yanzu sai ku zo gaban Ubangiji kabila-kabila da iyali-iyali.”20. Sa’ad da Sama’ila ya kawo dukan Isra’ila gaba, kabila-kabila, sai aka zaɓi kabilar Benyamin ta wurin jefa ƙuri’a.21. Sai ya kawo kabilar Benyamin gaba, iyali-iyali, aka zaɓi iyalin Matri. A ƙarshe aka zaɓi Shawulu ɗan Kish. Amma da aka neme shi sai ba a same shi ba.22. Suka ƙara nemi bayani daga Ubangiji suka ce, “Mutumin ya zo nan kuwa?” Ubangiji ya ce, “I, ga shi can, ya ɓuya cikin kayayyaki.”23. Suka ruga suka kawo shi. Da ya tsaya cikin mutane, sai ya fi kowa tsayi.24. Sama’ila ya ce wa dukan mutane, “Kun ga wanda Ubangiji ya zaɓa ko? Ba wani kamar sa a cikin dukan mutane.” Sai mutane suka tā da murya suka ce, “Ran sarki yă daɗe.”25. Sama’ila kuwa ya bayyana wa mutane ƙa’idodin sarauta. Ya rubuta su cikin littafi ya ajiye a gaban Ubangiji. Sa’an nan ya sallame mutane, kowa ya koma gidansa.26. Shawulu ma ya tafi gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawan da Allah ya taɓa zuciyarsu.27. Amma waɗansu ’yan iska suka ce, “Yaya wannan mutum zai iya cetonmu?” Suka rena shi suka ƙi su kawo masa kyautai. Amma Shawulu bai ce uffam ba.1 Samaʼila 11:1-151. Nahash mutumin Ammon ya haura ya kewaye Yabesh Gileyad da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”2. Amma Nahash ya ce, “Zan ƙulla amana da ku kawai a kan sharaɗin cewa zan ƙwaƙulo idon dama na kowannenku, ta haka za a kunyata Isra’ila.”3. Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.”4. Da manzannin suka zo Gibeya garin Shawulu, suka gaya wa mutane wannan sharaɗin, suka yi kuka mai zafi.5. A daidai wannan lokacin kuwa Shawulu yana dawowa daga gona tare da shanunsa na noma, sai ya ce, “Me ya faru, mutane suna kuka haka?” Sai suka faɗa masa abin da mutanen Yabesh suka faɗa musu.6. Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai.7. Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.8. Mutanen Isra’ila sun kai dubu ɗari uku. Mutanen Yahuda kuma dubu talatin, sa’ad da Shawulu ya tara su a Bezek.9. Suka ce wa ’yan aikan da suka zo, “Ku faɗa wa mutanen Yabesh Gileyad, ‘Gobe, kafin rana tă yi zafi, za ku sami ceto.’ ” Sa’ad da ’yan aikan suka tafi, suka ba da saƙon nan ga mutanen Yabesh, sai suka farin ciki.10. Suka ce wa Ammonawa, “Gobe za mu miƙa wuya gare ku, ku kuma yi duk abin da kuka ga dama.”11. Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare.12. Sai mutane suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce, ‘Shawulu zai yi mulkinmu?’ A kawo mana su mu kashe.”13. Shawulu ya ce, “Ba wanda zai mutu yau, gama Ubangiji ya kuɓutar da Isra’ila a wannan rana.”14. Sai Sama’ila ya ce wa mutane, “Ku zo mu tafi Gilgal, a can za a yi wankan sarauta.”15. Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa.Zabura 55:16-2316. Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.17. Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.18. Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.19. Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.20. Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa.21. Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.22. Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.23. Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka.Karin Magana 15:18-2018. Mutum mai zafin rai kan kawo faɗa, amma mutum mai haƙuri kan kwantar da faɗa.19. An tare hanyar rago da ƙayayyuwa, amma hanyar mai aikata gaskiya buɗaɗɗiyar hanya ce.20. Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa, amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.Luka 22:24-4624. Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.25. Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.26. Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima.27. Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.28. Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.29. Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku.30. Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.31. “Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka kamar alkama.32. Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”33. Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”34. Yesu ya ce, “Ina gaya maka Bitrus, kafin zakara ya yi cara yau, za ka yi mūsun sanina sau uku.”35. Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, “Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?” Suka amsa, “Babu.”36. Ya ce musu, “Amma yanzu, in kuna da jakar kuɗi, ko jaka, ku ɗauka. In kuma ba ku da takobi, ku sayar da rigarku, ku saya.37. A rubuce yake cewa, ‘An lissafta shi tare da masu zunubi.’ Ina kuwa gaya muku, dole wannan ya cika a kaina. I, abin da aka rubuta a kaina yana kusan cikawa.”38. Almajiran suka ce, “Duba Ubangiji, ga takuba biyu.” Yesu ya ce, “Ya isa.”39. Yesu ya fita zuwa Dutsen Zaitun kamar yadda ya saba, almajiransa kuma suka bi shi.40. Da ya kai wurin, sai ya ce musu, “Ku yi addu’a don kada ku fāɗi cikin jarraba.”41. Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi addu’a,42. “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.”43. Wani mala’ika daga sama ya bayyana gare shi, ya ƙarfafa shi.44. Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.45. Da ya tashi daga addu’a, ya koma inda almajiransa suke, sai ya iske su suna barci, daga gajiyar baƙin ciki.46. Ya tambaye su, “Don me kuke barci? Ku tashi ku yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.