Baibul a cikin shekara guda Mayu 91 Samaʼila 20:1-421. Sai Dawuda ya gudu daga Nayiwot a Rama ya je wurin Yonatan ya ce, “Me na yi? Wane laifi ne na yi? Ta wace hanya ce na yi wa mahaifinka laifi har da yake neman yă kashe ni?”2. Yonatan ya ce, “Faufau, ba za ka mutu ba! Ka ji nan, mahaifina ba ya yin kome ba tare da ya shawarce da ni ba. Me ya sa ya ɓoye mini wannan? Ba zai yiwu ba.”3. Sai Dawuda ya rantse ya ce, “Mahaifinka ya san cewa, na sami tagomashi a gare ka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada yă baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji, da kai kuma, taki ɗaya kaɗai ya rage tsakanina da mutuwa.”4. Sai Yonatan ya ce, “Duk abin da kake so in yi maka zan yi.”5. Dawuda ya ce, “Gobe fa shi ne Bikin Sabon Wata, ya kamata in ci tare da sarki amma bari in tafi fili in ɓuya har jibi da yamma.6. In mahaifinka bai gan ni ba, ka gaya masa cewa, ‘Dawuda ya nemi izinina domin yă hanzarta yă tafi garinsa a Betlehem saboda ana hadaya ta shekara-shekara don dukan zuriyarsa.’7. In ya yi na’am, to, bawanka ya tsira. Amma in ka ga ya damu, to, ka tabbata ya yi niyya yă kashe ni.8. Kai kuma, ka nuna alheri ga bawanka, gama ka riga ka yi yarjejjeniya da ni a gaban Ubangiji, in kuwa na yi laifi ne sai ka kashe ni da kanka. Don me za ka bashe ni ga mahaifinka?”9. Yonatan ya ce, “Labudda! In na ji ƙishin-ƙishin, cewa mahaifina yana neman yă kashe ka ashe, ba zan gaya maka ba?”10. Dawuda ya ce, “Wa zai gaya mini idan mahaifinka ya amsa maka da amsa marar daɗi?”11. Yonatan ya ce, “Zo mu fita zuwa fili.” Sai suka tafi tare.12. Sai Yonatan ya ce wa Dawuda, “Na yi rantse da Ubangiji, Allah na Isra’ila cewa war haka jibi, zan yi ƙoƙari in ji daga mahaifina, idan ya yi magana mai kyau game da kai, zan gaya maka.13. Amma in mahaifina ya sa zuciya yă cuce ka, Ubangiji yă hukunta ni da hukunci mai tsanani in ban gaya maka ba, in kuma sa ka ka tafi lafiya. Ubangiji yă kasance tare da kai kamar yadda ya kasance da mahaifina.14. Amma ka nuna mini alheri marar ƙarewa iri ta Ubangiji dukan rayuwata don kada a kashe ni.15. Kada kuma ka yanke alherinka ga iyalina ko da Ubangiji ya hallaka dukan maƙiyin Dawuda a duniya.”16. Saboda haka Yonatan ya yi yarjejjeniya da gidan Dawuda cewa Ubangiji yă kawo dukan maƙiyin Dawuda ga mutuwa.17. Yonatan kuwa ya sa Dawuda ya sāke tabbatar masa rantsuwansa game da abokantakarsa da shi, gama yana ƙaunar Dawuda kamar ransa.18. Sai Yonatan ya gaya wa Dawuda cewa, “Gobe ne Bikin Sabon Wata, za a rasa ka, da yake kujerarka za tă kasance ba kowa a kai.19. Jibi wajajen yamma, ka tafi wurin da ka ɓuya lokacin da wannan matsala ta fara, ka tsaya kusa da dutsen Etsel.20. Zan harbi kibiya uku ta wajen, sai ka ce dai ina harbin baka.21. Sa’an nan zan aiki yaro in ce masa, ‘Je ka nemo kibiyoyin.’ In na ce masa, ‘Duba, kibiyoyin suna wannan gefen da kake, kawo su,’ sai ka fito, wato, tabbatacce muddin Ubangiji yana raye, ka tsira, ba wani hatsari.22. Amma in na ce wa yaron, ‘Duba, kibiyoyin suna gaba da kai,’ sai ka tafi, gama Ubangiji ya sallame ka.23. Game da al’amarin da muka tattauna da ni da kai kuwa, ka tuna fa Ubangiji ne shaida tsakanina da kai har abada.”24. Dawuda ya tafi ya ɓuya a fili. Sa’ad da ranar Bikin Sabon Wata ta zo, sarki ya zauna don yă ci.25. Ya zauna a kujeransa inda ya saba zama kusa da bango yana fuskantar Yonatan, Abner kuma ya zauna kusa da sarki. Amma kujeran Dawuda ba kowa.26. Shawulu bai ce kome ba a ranar domin ya yi tsammani wataƙila wani abu ya faru da Dawuda ya mai da shi marar tsarki, tabbatacce ba shi da tsarki.27. Amma kashegari, rana ta biyu ga wata, kujeran Dawuda kuma ba kowa, sai Shawulu ya ce wa ɗansa Yonatan, “Me ya sa ɗan Yesse bai zo cin abinci, jiya da yau ba?”28. Yonatan ya ce, “Dawuda ya nemi izinina don yă tafi Betlehem.29. Ya ce, ‘Bari in tafi gama iyalinmu suna miƙa hadaya a gari, ’yan’uwana kuwa sun gayyace ni in kasance a can. In na sami yardarka, bari in tafi in ga ’yan’uwana.’ Dalilin ke nan da bai zo ci da sarki ba.”30. Fushin Shawulu ya ƙuna a kan Yonatan, sai ya ce masa, “Kai shege ne, haihuwar banzan mace; ai, na san kana goyon bayan ɗan Yesse don ka wulaƙantar da kanka da mahaifinka.31. Muddin ɗan Yesse yana da rai a duniya, ba za ka kahu ba. Sarautarka kuma ba za tă kahu ba. Yanzu sai ka je ka kawo mini shi. Dole yă mutu.”32. Yonatan ya ce wa mahaifinsa, “Me ya sa zai mutu? Me ya yi?”33. Amma Shawulu ya jefe shi da māshi don yă kashe shi. A nan ne Yonatan ya san lalle mahaifinsa ya yi niyya yă kashe Dawuda.34. Yonatan ya tashi daga tebur cin abincin da fushi. A rana ta biyun kuwa bai ci abinci ba, gama yana baƙin ciki game da rashin kunyar mahaifinsa game da Dawuda.35. Da safe Yonatan ya tafi domin yă sadu da Dawuda a fili. Ya tafi tare da wani ƙaramin yaro.36. Ya ce wa yaron, “Yi ruga da gudu ka nemo kibiyoyin da na harba.” Da yaron ya ruga sai ya harba kibiya a gaba da shi.37. Da yaron ya isa wurin da kibiyan Yonatan ya fāɗi, Yonatan ya kira shi ya ce, “Kibiyan na gabanka fa.”38. Sai ya tā da murya ya ce, “Maza, yi sauri kada ka tsaya.” Yaron ya ɗauko kibiya ya kawo wa maigidansa.39. (Yaron kuwa bai san kome game da wannan abu ba, sai Yonatan da Dawuda kawai.)40. Yonatan ya ba wa yaron makaman ya ce, “Ka ɗauka ka koma gari.”41. Da yaron ya tafi, sai Dawuda ya tashi daga inda ya ɓuya kusa da tarin duwatsu, ya rusuna har sau uku. Sa’an nan suka sumbaci juna, suka yi kuka, Dawuda kuwa ya yi kuka sosai.42. Yonatan ya ce wa Dawuda, “Sauka lafiya, mun riga mun yi rantsuwar abokantaka da juna a cikin sunan Ubangiji cewa, ‘Ubangiji ne shaida tsakanina da kai, tsakanin zuriyarka da zuriyata har abada.’ ” Sai Dawuda ya tafi, Yonatan kuwa ya koma gari.1 Samaʼila 21:1-151. Dawuda ya tafi Nob a wurin Ahimelek firist. Da Ahimelek ya gan shi sai ya firgita ya ce, “Me ya sa kai kaɗai ne? Me ya sa ba wani tare da kai?”2. Dawuda ya ce wa Ahimelek firist, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya sa in yi. Na faɗa wa mutanena inda za su same ni.3. Yanzu, me kake da shi a hannu? Ka ba ni burodi guda biyar, ko wani abu da kake da shi a nan.”4. Amma firist ya ce wa Dawuda, “Ba ni da burodi iri na kowa da kowa, sai dai akwai burodin da aka tsarkake. Za ka iya ɗauka ku ci idan mutanenka ba su kwana da mata ba.”5. Dawuda ya ce, “Lalle ne a keɓe muke daga mata. Mutanena sukan keɓe kansu a koyaushe suka tashi ’yar tafiya, balle fa a yau!”6. Don haka firist ya ba shi keɓaɓɓen burodi, tun da yake babu wani burodi a can sai dai burodin Kasancewa da aka cire daga gaban Ubangiji, aka sa burodi mai zafi a maimakon wanda aka cire a ranar.7. A ranar kuwa, ɗaya daga cikin bayin Shawulu yana can, a tsare a gaban Ubangiji, sunansa Doyeg, mutumin Edom, shugaban makiyayan Shawulu.8. Dawuda ya ce wa Ahimelek, “Ba ka da māshi ko takobi a nan? Ban kawo māshina ko wani makami ba gama saƙon sarki ya zo mini da gaggawa.”9. Sai firist ya ce, “Takobin Goliyat Bafilistin nan wanda ka kashe a Kwarin Ela yana nan. An naɗe shi da ƙyallen aka ajiye a bayan Efod, in kana so, sai ka ɗauka. Ba wani takobi kuma sai wancan.” Dawuda ya ce, “Ba ni shi, ai, ba wani kamar sa.”10. A ranar, Dawuda ya gudu daga wajen Shawulu ya tafi wuri Akish sarkin Gat.11. Amma bayin Akish suka ce masa, “Wannan ba shi ne Dawuda sarkin ƙasar ba? Ashe, ba shi ne aka yi ta yin waƙoƙi a kansa, ana raye-raye, ana cewa, “Shawulu ya kashe dubbai, Dawuda kuwa ya kashe dubun dubbai?”12. Dawuda ya riƙe waɗannan kalmomi a zuciyarsa, ya kuma ji tsoron Akish sarkin Gat sosai.13. Don haka sai ya yi kamar ya taɓu a gabansu. A duk lokacin da yake tare da su, sai yă yi kamar ya haukace. Ya yi ta zāne-zāne a ƙofofi, ya bar miyau yana ta bin gemunsa.14. Akish ya ce wa bayinsa, “Duba, wannan mutum yana hauka. Me ya sa kuka kawo shi a wurina?15. Na rasa masu hauka ne da za ku kawo mini wannan mutum yă yi ta hauka a gabana? Dole ne wannan mutum yă shiga gidana?”Zabura 59:1-51. Ka cece ni daga abokan gābana, ya Allah; ka tsare ni daga waɗanda suka tayar mini.2. Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa.3. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.4. Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!5. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, ka tashi ka hukunta dukan al’ummai; kada ka nuna jinƙai ga mugaye maciya amana.Karin Magana 15:31-3331. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.32. Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.33. Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.Luka 24:36-5336. Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”37. Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.38. Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?39. Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”40. Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.41. Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?”42. Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,43. ya karɓa ya ci a gabansu.44. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”45. Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.46. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.47. Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.48. Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.49. Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”50. Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.51. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.52. Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.53. Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.