Baibul a cikin shekara guda Yuni 112 Sarakuna 9:1-371. Sai Elisha ya kira wani daga cikin ƙungiyar annabawa, ya ce masa, “Ka sha ɗamara, ka ɗauki wannan kwalabar mai ka je Ramot Gileyad.2. Da ka isa can, ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi. Ka je wurinsa, ka ja shi gefe daga abokansa, ka shiga da shi ɗaki na ciki.3. Sa’an nan ka ɗauki kwalabar man ka zuba a kansa, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa, na naɗa ka sarkin Isra’ila.’ Sa’an nan ka buɗe ƙofa ka ruga a guje; kada ka ɓata lokaci!”4. Sai saurayin nan, annabi, ya tafi Ramot Gileyad.5. Da ya isa can, sai ya tarar da hafsoshin soji zaune a wuri guda. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka komanda.” Sai Yehu ya ce, “Wanne a cikinmu?” Sai ce, “Dominka, komanda.”6. Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida. Sa’an nan annabin ya zuba wa Yehu mai a kā, ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na naɗa ka sarki a bisa jama’ar Ubangiji, wato, Isra’ila.7. Za aka hallaka gidan Ahab maigidanka, zan kuma ɗauki fansar jinin bayina annabawa da kuma jinin dukan bayin Ubangiji da Yezebel ta zub da.8. Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan ’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko ’yantattu.9. Zan mai da gidan Ahab kamar gidan Yerobowam ɗan Nebat da kuma kamar gidan Ba’asha ɗan Ahiya.10. Game da Yezebel kuwa, karnuka za su cinye ta a fili a Yezireyel, ba kuwa wanda zai binne ta.’ ” Sa’an nan ya buɗe ƙofa ya ruga a guje.11. Da Yehu ya koma wurin sauran hafsoshin sai ɗaya daga cikinsu ya tambaye shi, “Lafiya? Me ya kawo wannan mahaukaci a wurinka?” Sai Yehu ya ce, “Ka san mahaukacin nan da irin maganganunsa.”12. Suka ce masa, “Ba gaskiya ba ne, ka dai faɗa mana.” Yehu ya ce, “Ga abin da ya ce mini, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce, na naɗa ka sarki a bisa Isra’ila.’ ”13. Sai suka yi sauri suka ɗauki rigunansu suka shimfiɗa a ƙasa, suka busa kakaki, suka yi ihu, suka ce, “Yehu ne sarki.”14. Saboda haka, Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi, ya ƙulla wa Yoram maƙarƙashiya (To, Yoram da dukan Isra’ila suna kāre Ramot Gileyad daga Hazayel sarkin Aram,15. amma Sarki Yoram ya koma Yezireyel don yă farfaɗo daga raunukan da Arameyawa suka ji masa a wata gabzawar da ya yi da Hazayel sarkin Aram.) Yehu ya ce, “In haka kuke ji, kada ku bar wani yă sulluɓe daga birnin yă kai labarin Yezireyel.”16. Sai ya tashi ya ɗauki keken yaƙinsa ya tafi Yezireyel gama Yoram yana hutawa a can. Ga kuma Ahaziya sarkin Yahuda ya je don yă gan shi.17. Mai tsaro kuwa yana tsaye a kan hasumiya a Yezireyel, sai ya hangi rundunar Yehu sa’ad da yake zuwa. Ya ce, “Na ga wata runduna.” Sai Yoram ya umarta, “Nemi mahayin doki a aike shi yă tarye su, yă kuma tambaye su, ‘Lafiya?’ ”18. Sai mahayin dokin ya hau, ya ruga, ya taryi Yehu, ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Sai Yehu ya ce masa, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.” Sai mai tsaron ya ce wa sarki, “Ɗan saƙon ya kai wurinsu, amma ba ya dawowa.”19. Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”20. Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.”21. Yoram ya umarta, “Haɗa mini keken yaƙi!” Da aka haɗa, sai Yoram sarkin Isra’ila, da Ahaziya sarkin Yahuda, suka hau suka tafi, kowa a keken yaƙinsa, don su taryi Yehu. Suka sadu da shi a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel.22. Sa’ad da Yoram ya ga Yehu sai ya tambaye shi, “Lafiya kuwa ka zo, Yehu?” Yehu ya ce, “Ina kuwa lafiya, da yake dukan bautar gumaka da bokancin mahaifiyarka Yezebel sun bazu ko’ina?”23. Yoram ya juya, ya gudu, yana ce wa Ahaziya, “Cin amana, Ahaziya!”24. Sai Yehu ya ja bakansa ya harbi Yoram a tsakanin kafaɗunsa. Kibiyar ta same shi a zuciyarsa sai ya fāɗi a cikin keken yaƙinsa.25. Yehu ya ce wa Bidkar, hafsan keken yaƙinsa, “Ka ɗauke shi ka jefar a filin da yake na Nabot mutumin Yezireyel. Ka tuna yadda ni da kai muke a kekunan yaƙi a bayan Ahab mahaifinsa sa’ad da Ubangiji ya yi wannan annabci game da shi,26. ‘Jiya na ga jinin Nabot da jinin ’ya’yansa, in ji Ubangiji, kuma ba shakka zan ɗauki fansa a wannan fili, in ji Ubangiji.’ Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar da shi a bisa wannan fegi, bisa ga faɗin Ubangiji. Saboda haka, ka ɗauke shi ka jefar a filin, in ji Ubangiji.”27. Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.28. Barorinsa suka ɗauke shi cikin keken yaƙi zuwa Urushalima suka binne shi a kabarinsa tare da kakanninsa a birnin Dawuda.29. (A shekara ta goma sha ɗaya ta Yoram ɗan Ahab, Ahaziya ya zama sarkin Yahuda.)30. Sa’an nan Yehu ya je Yezireyel. Sa’ad da Yezebel ta sami labari, sai ta sha kwalliya ta gyara gashin kanta, ta zauna tana kallo daga taga.31. Yayinda Yehu ya shiga ƙofa, sai ta ce, “Lafiya, kai Zimri, mai kashe maigidansa?”32. Sai ya ɗaga ido ya dubi tagan ya ce, “Wa yake gefena? Wane ne?” Sai bābānni biyu ko uku suka leƙo suka dube shi.33. Yehu ya ce musu, “Ku jefa ta ƙasa!” Sai suka jefar da ita, jininta ya fantsama a jikin bango da kuma a jikin dawakai yayinda suke tattaka ta.34. Yehu ya shiga ya ci, ya kuma sha. Ya ce, “Ku san yadda za ku yi da la’ananniyan nan, ku binne ta, gama ’yar sarki ce.”35. Amma sa’ad da suka je don su binne ta, ba su sami kome ba sai ƙoƙon kanta, ƙafafunta da kuma hannuwanta.36. Suka komo suka faɗa wa Yehu, wanda ya ce, “Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa Iliya mutumin Tishbe. A fili, a Yezireyel, karnuka za su cinye naman Yezebel.37. Gawar Yezebel zai zama kamar juji a ƙasa, a fili, a Yezireyel, har ba wanda zai iya cewa, ‘Wannan Yezebel ce.’ ”2 Sarakuna 10:1-361. To, akwai ’ya’ya maza saba’in na gidan Ahab a Samariya. Saboda haka Yehu ya rubuta wasiƙu, ya aika su Samariya, zuwa ga shugabannin Yezireyel, da kuma ga masu lura da ’ya’yan Ahab. Ya ce,2. “Da zarar wasiƙan nan ta sadu da ku, da yake ’ya’yan maigidanku suna tare da ku, kuna kuma da kekunan yaƙi da dawakai, da birni mai katanga da makamai,3. sai ku zaɓi mafi cancanta a cikin ’ya’yan maigidanku ku sa shi a kan kursiyin mahaifinsa. Sa’an nan ku yi yaƙi don gidan maigidanku.”4. Amma suka razana suka ce, “Idan sarakuna biyu ba su iya yin tsayayya da shi ba, wane mu?”5. Saboda haka sarkin fada, da gwamnan birnin, da dattawa, da kuma masu lura da ’ya’yan suka aika da saƙo ga Yehu, cewa, “Mu bayinka ne, za mu kuma yi duk abin da ka ce. Ba za mu naɗa kowa sarki ba; sai ka yi abin da ka ga ya fi kyau.”6. Sai Yehu ya sāke rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “In a gefena kuke, to, sai ku yi biyayya da ni, ku fille kawunan ’ya’yan maigidanku, ku kawo mini a Yezireyel war haka gobe.” To, ’ya’yan sarki, su saba’in, suna tare da manyan birni waɗanda suke lura da su.7. Sa’ad da wasiƙar ta iso, sai mutanen nan suka ɗauki dukan ’ya’yan sarkin nan saba’in, suka kashe su, suka sa kawunansu cikin kwanduna, suka aika wa Yehu a Yezireyel.8. Da ɗan saƙon ya iso, sai aka ce wa Yehu, “Sun kawo kawunan ’ya’yan sarki.” Sai Yehu ya ce, “Ku ajiye su kashi biyu a ƙofar gari har safiya.”9. Da gari ya waye, sai Yehu ya fita ya tsaya a gaban dukan jama’a ya ce, “Ba ku da laifi. Ni ne na ƙulla wa maigidana maƙarƙashiya, na kuma kashe shi, amma wa ya karkashe dukan waɗannan?10. Ku sani fa, ba kalmar da Ubangiji ya faɗa game da gidan Ahab da ba za tă cika ba. Ubangiji ya yi abin da ya alkawarta ta bakin bawansa Iliya.”11. Saboda haka Yehu ya kashe duk waɗanda suka rage na iyalin Ahab a Yezireyel, tare da dukan fadawansa da aminansa da firistocinsa, ba a bar masa kowa ba.12. Sa’an nan Yehu ya nufi Samariya. Da ya kai Bet-Eked na Makiyaya,13. sai ya gamu da waɗansu daga dangin Ahaziya sarkin Yahuda, sai ya tambaye su, ya ce, “Ku, su wane ne?” Suka ce, “Mu dangin Ahaziya ne, mun kuma zo ne mu gai da iyalan sarki da kuma mahaifiyar sarauniya.”14. Sai ya umarta ya ce, “A kama su da rai!” Aka kuwa kama su aka yayyanka kusa da rijiyar Bet-Eked, su arba’in da biyu. Ba a bar wani da rai ba.15. Bayan ya bar wurin, sai ya gamu da Yehonadab ɗan Rekab wanda yake kan hanyarsa don yă sadu da shi. Sai Yehu ya gaishe shi, ya ce, “Ka amince da ni yadda na amince da kai?” Yehonadab ya ce, “I.” Yehu ya ce, “To, in haka ne ka ba ni hannunka.” Sai ya miƙa masa, Yehu kuwa ya ja shi cikin keken yaƙin.16. Yehu ya ce, “Zo tare da ni ka ga himmata saboda Ubangiji.” Sa’an nan ya sa suka tafi tare cikin keken yaƙinsa.17. Da Yehu ya isa Samariya, sai ya karkashe dukan sauran iyalin Ahab, ya hallaka su, bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.18. Sa’an nan Yehu ya tattara dukan jama’a ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan ne kawai; amma Yehu zai bauta masa sosai.19. Yanzu sai ku kira dukan annabawan Ba’al, dukan masu yin masa hidima da kuma dukan firistocinsa. Ku tabbata ba a manta da wani ba, gama zan yi wa Ba’al babbar hadaya. Duk wanda bai zo ba, a bakin ransa.” Amma Yehu yana wayo ne domin yă hallaka masu yi wa Ba’al sujada.20. Yehu ya ce, “Ku kira jama’a don a girmama Ba’al.” Saboda haka suka yi shela.21. Sa’an nan ya aika saƙo ko’ina a Isra’ila, dukan masu yi wa Ba’al hidima kuwa suka tattaru, ba mutumin da bai zo ba. Suka yi cincirindo a haikalin Ba’al har sai da ya cika makil.22. Sai Yehu ya ce wa mai ajiyar tufafi, “Ka kawo riguna domin dukan masu yi wa Ba’al hidima.” Sai ya fito musu da riguna.23. Sa’an nan Yehu da Yehonadab ɗan Rekab, suka shiga haikalin Ba’al. Yehu ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku dudduba ku tabbatar cewa babu wani bawan Ubangiji a nan tare da ku, sai masu hidimar Ba’al kawai.”24. Saboda haka suka shiga don su miƙa hadayu da kuma hadaya ta ƙonawa. To, Yehu ya riga ya ba wa mutane takwas wannan kashedi a waje cewa, “In waninku ya bar ɗaya daga cikin mutanen nan da nake danƙa a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”25. Nan da nan sa’ad da Yehu ya gama yin hadayar, sai ya umarci masu gadin da hafsoshi, “Ku shiga ku karkashe su; kada ku bar wani yă tsere.” Saboda haka suka karkashe su da takobi. Masu gadin da hafsoshin suka wuwwurga gawawwakinsu waje, suka kuma shiga ciki cikin haikalin Ba’al ɗin,26. suka fitar da dutsen tsafi daga haikalin Ba’al, suka kuma ƙone shi.27. Suka farfasa dutsen tsafin Ba’al, suka kuma rushe haikalin, mutane suka mai da wurin salga har yă zuwa yau.28. Ta haka Yehu ya hallaka butar Ba’al a Isra’ila.29. Duk da haka, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba, wato, yin sujada ga siffofin maruƙa na zinariya a Betel da kuma Dan.30. Ubangiji ya ce wa Yehu, “Tun da yake ka aikata abin da yake mai kyau a idanuna, ka kuma yi wa gidan Ahab dukan abin da yake a zuciyata, ina yin maka alkawari cewa zuriyarka za su yi mulkin Isra’ila har tsara ta huɗu.”31. Duk da haka, Yehu bai mai da hankali ya kiyaye dokokin Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa ba. Bai rabu da zunubin Yerobowam, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.32. A kwanakin sai Ubangiji ya fara rage girman Isra’ila, Hazayel ya yi nasara a bisa Isra’ila a ko’ina a yankinsu33. gabas da Urdun, cikin dukan ƙasar Gileyad (yankin Gad, da na Ruben, da na Manasse), daga Arower wajen Kwarin Arnon ya ratsa Gileyad zuwa Bashan.34. Game da sauran ayyukan mulkin Yehu, da dukan abin da ya yi, a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.35. Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa.36. Yehu ya yi sarautar Isra’ila a Samariya shekara ashirin da takwas.Zabura 72:17-2017. Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.18. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah, Allah na Isra’ila, wanda shi kaɗai ya aikata abubuwa masu banmamaki.19. Yabo ya tabbata ga sunansa mai ɗaukaka har abada; bari dukan duniya ta cika da ɗaukakarsa. Amin kuma Amin.20. Wannan ya kammala addu’o’in Dawuda ɗan Yesse.Karin Magana 18:14-1514. Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.15. Zuciya mai la’akari kan nemi sani; kunnuwan mai hikima kan bincika don yă koya.Yohanna 19:1-221. Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.2. Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya.3. Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.4. Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, “Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba.”5. Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, “Ga mutumin!”6. Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”7. Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”8. Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi,9. sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba.10. Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?”11. Yesu ya amsa ya ce, “Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”12. Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”13. Da Bilatus ya ji haka, sai ya fito da Yesu, ya kuma zauna a kujerar shari’ar da ake ce da shi Daɓen Dutse (wanda a harshen Arameyik ana ce da shi Gabbata).14. Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.”15. Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”16. A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Saboda haka sojoji suka tafi da Yesu.17. Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota).18. Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.19. Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa.20. Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik.21. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.”22. Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.