Baibul a cikin shekara guda Yuni 152 Sarakuna 17:1-411. A shekara ta goma sha biyu ta mulkin Ahaz sarkin Yahuda, Hosheya ɗan Ela ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki na shekara tara.2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar na sarakunan Isra’ilan da suka riga shi ba.3. Shalmaneser sarkin Assuriya ya kawo wa Hosheya wanda dā abokin tarayyarsa ne, hari har Hosheya ya biya shi haraji.4. Amma sarkin Assuriya ya gane cewa Hosheya mai cin amana ne, gama ya aika da wakilai wurin So sarkin Masar, ya kuma daina aika wa sarkin Assuriya haraji yadda ya saba yi kowace shekara. Saboda haka Shalmaneser ya kama shi ya sa a kurkuku.5. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku.6. A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, sarkin Assuriya ya ci Samariya da yaƙi ya kuma kwashe Isra’ilawa zuwa Assuriya. Ya tsugunar da su a Hala, da a Gozan a bakin Kogin Habor da kuma a garuruwan Medes.7. Duk wannan ya faru ne saboda Isra’ilawa sun yi wa Ubangiji Allahnsu zunubi, shi wanda ya fitar da su daga Masar daga ƙarƙashin ikon Fir’auna sarkin Masar. Sun yi wa waɗansu alloli sujada8. suka kuma bi gurbin al’umman da Ubangiji ya kora a gabansu, da kuma ayyukan da sarakuna Isra’ila suka gabatar.9. Isra’ilawa a ɓoye sun aikata abubuwan da ba daidai ba ga Ubangiji Allahnsu. Tun daga hasumiyoyi har zuwa birane masu katanga, sun gina wa kansu wuraren sujada na tudu a dukan garuruwansu.10. Suka kafa keɓaɓɓun duwatsu da kuma ginshiƙan Ashera a kowane tudu mai tsayi da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.11. Suka ƙona turare a kan kowane tudu, kamar dai yadda al’umman da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka yi muguntan da ya sa Ubangiji ya yi fushi.12. Suka bauta wa gumaka, ko da yake Ubangiji ya ce, “Ba za ku yi wannan ba.”13. Ubangiji ya yi wa Isra’ila da Yahuda kashedi ta bakin dukan annabawansa da kuma masu duba, cewa, “Ku juyo daga mugayen ayyukanku. Ku yi biyayya da umarnai da farillaina, bisa ga dukan Dokar da na dokaci kakanninku su bi, waɗanda na kuma bayar ta wurin bayina, annabawa.”14. Amma ba su saurare ni ba don sun kangare kamar kakanninsu, waɗanda ba su amince da Ubangiji Allahnsu ba.15. Suka yi watsi da farillansa da yarjejjeniyar da ya ƙulla da kakanninsu, da kuma kashedin da ya yi musu. Suka bi gumaka marasa amfani, wannan ya sa su ma kansu suka zama marasa amfani. Suka kwaikwayi sauran ƙasashen da suke kewaye da su, ko da yake Ubangiji ya umarce su cewa, “Kada ku yi rayuwa irin tasu,” suka kuwa yi abin da Ubangiji ya hana su.16. Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada.17. Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.18. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari,19. ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo.20. Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.21. Sa’ad da ya ware Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat sarki a kansu. Yerobowam ya rinjayi Isra’ila daga ƙin Ubangiji, ya sa suka aikata babban zunubi.22. Isra’ila suka nace cikin dukan zunuban Yerobowam, ba su kuwa rabu da su ba23. har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can.24. Sarkin Assuriya ya kawo mutane daga Babilon, Kuta, Afa, Hamat da Sefarfayim ya zaunar da su a garuruwan Samariya don su maya gurbin Isra’ilawa. Suka mallaki Samariya suka kuma zauna a garuruwansu.25. Sa’ad da suka fara zama a can, ba su bauta wa Ubangiji ba; saboda haka ya aika da zakoki a tsakaninsu suka karkashe waɗansu mutane.26. Sai aka faɗa wa sarkin Assuriya cewa, “Mutanen da ka kwashe ka zaunar a garuruwan Samariya fa ba su san abin da allahn ƙasar yake bukata ba. Saboda haka allahn ƙasar ya tura zakoki a cikinsu, waɗanda suke karkashe su, domin mutanen ba su san abin da yake bukata ba.”27. Sai sarkin Assuriya ya ba da umarni cewa, “A sami wani daga cikin firistocin da aka kwaso zuwa bauta daga Samariya, yă koma yă zauna a can, yă koya wa mutanen abin da allahn ƙasar yake bukata.”28. Saboda haka ɗaya daga cikin firistocin da aka kawo bauta daga Samariya ya dawo ya zauna a Betel, ya koya musu yadda za su yi sujada ga Ubangiji.29. Duk da haka, jama’ar kowace ƙasa, suka ƙera tasu alloli a garuruwa masu yawa inda suke zaune, suka sa su a masujadan da mutanen Samariya suka gina a kan tuddai.30. Mutane daga Babilon suka ƙera Sukkot Benot, mutane daga Kut suka ƙera Nergal, mutane daga Hamat suka ƙera Ashima;31. Awwiyawa suka ƙera Nibhaz da Tartak, Sefarfayawa kuwa suka ƙone ’ya’yansu a wuta a matsayi hadayu ga Adrammelek da Anammelek allolin Sefarfayim.32. Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma suka zaɓi mutanensu su yi musu hidima a matsayin firistoci a masujadan da suke kan tuddai.33. Sun yi wa Ubangiji sujada, amma kuma sun bauta wa allolinsu bisa ga al’adun ƙasashen da suka fito.34. Har yă zuwa yau, sun nace da ayyukansu na dā. Ba sa yin wa Ubangiji sujada, ba sa kuma bin dokoki da farillansa, dokoki da umarnan da Ubangiji ya ba wa zuriyar Yaƙub, wadda ya ba wa suna Isra’ila.35. Da Ubangiji ya ƙulla alkawari da Isra’ilawa, ya dokace su cewa, “Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada ko ku durƙusa a gabansu ku bauta musu, ko ku miƙa musu hadaya.36. Amma Ubangiji wanda ya fito da ku daga Masar da iko mai girma da hannu mai ƙarfi, shi ne za ku yi masa sujada. Gare shi za ku durƙusa ku kuma miƙa masa hadayu.37. Dole kullum ku mai da hankali ga kiyaye ƙa’idodi da farillan, dokoki da umarnan da ya rubuta muku. Kada ku yi wa waɗansu alloli sujada.38. Kada ku manta da alkawarin da na ƙulla da ku, kada ku yi sujada ga waɗansu alloli.39. Maimakon haka, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada; shi ne zai cece ku daga hannun abokan gābanku.”40. Amma ba su saurara ba, suka nace da ayyukansu na dā.41. Ko ma yayinda mutanen nan suke yi wa Ubangiji sujada, ba su daina bauta wa gumakansu ba. Har yă zuwa yau, ’ya’yansu da jikokinsu sun ci gaba da bin gurbin kakanninsu.2 Sarakuna 18:1-371. A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki.2. Yana da shekara ashirin da biyar da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Abiya ’yar Zakariya.3. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda kakansa Dawuda ya yi.4. Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.)5. Hezekiya ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Ba a yi wani kamar sa ba cikin dukan sarakunan Yahuda; ko kafin shi, ko kuma bayansa.6. Ya manne wa Ubangiji, bai fasa binsa ba; ya yi biyayya da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa.7. Ubangiji kuma ya kasance tare da shi, ya yi nasara a duk abin da ya sa hannu. Ya yi tawaye ga sarkin Assuriya, ya ƙi yă bauta masa.8. Daga hasumiya zuwa birni mai katanga, ya ci Filistiyawa da yaƙi, har zuwa Gaza da kewaye.9. A shekara ta huɗu ta Hezekiya, wato, shekara ta bakwai ke nan ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila; Shalmaneser Sarkin Assuriya ya tasam ma Samariya da yaƙi; ya kewaye ta.10. A ƙarshen shekara ta uku, Assuriyawa suka ci Samariya da yaƙi. An ci Samariya da yaƙi a shekara ta shida ta mulki Hezekiya, wanda ya zo daidai da shekara ta tara ta mulkin Hosheya sarkin Isra’ila.11. Sarkin Assuriya ya kwashe Isra’ila zuwa Assuriya ya zaunar da su a Hala, da Gozan a kogin Habor da kuma garuruwan Medes.12. Wannan ya faru ne domin ba su yi biyayya ga Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsu; da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su saurari umarnin ba, balle su kiyaye su.13. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su.14. Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda.15. Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki.16. A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.17. Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.18. Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.19. Jagoran dogarawan sarkin Assuriya ya ce musu, “Ku ce wa Hezekiya, “ ‘Ga abin da babban sarkin Assuriya ya ce, da wa kake taƙama?20. Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye?21. Na sani kana dogara da Masar, wadda take kamar karar masara, wadda in ka jingina a kai, za tă karye tă soki hannunka. Haka Fir’auna sarkin Masar yake ga dukan wanda ya dogara da shi.22. Sai ya ci gaba da cewa, in kuma ka ce mini “Muna dogara ga Ubangiji Allahnmu ne,” ba masujadansa da bagadansa ne Hezekiya ya ciccire, yana ce wa Urushalima da Yahuda, “Dole ku yi sujada a gaban wannan bagade a Urushalima”?23. “ ‘Yanzu, ka zo ku shirya da shugabana, sarkin Assuriya. Zan ba ka dawakai dubu biyu, in za ka sami mahayansu!24. Yaya za ka yi tsayayya da mafi ƙanƙantan hafsan shugabana, ko da kana dogara da Masar don kekunan yaƙi da mahaya dawakai?25. Ban da haka ma, kana gani cewa na zo in hallaka wannan wuri ne ba tare da na ji daga Ubangiji ba? Ubangiji da kansa ne ya ce da ni in kawo wa wannan ƙasa hari in hallaka ta.’ ”26. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”27. Amma shugaban sojojin ya ce, “Ai, ba gare ku da sarkinku kaɗai ne shugabana ya aike ni ba. Amma har ga mutanen da suke zaune a kan katangar birnin, waɗanda za su ci kashinsu, su sha fitsarinsu!”28. Sai shugaban sojojin ya yi kira da Yahudanci ya ce, “Ku ji muryar babban sarki, sarkin Assuriya!29. Ga abin da sarki ya faɗa; kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku. Ba zai iya cetonku daga hannuna ba.30. Kada ku yarda Hezekiya yă rinjaye ku cewa ku dogara ga Allah, sa’ad da ya ce da ku, ‘Ba shakka Ubangiji zai cece mu; yana ce da ku birnin nan ba zai faɗa a hannun sarkin Assuriya ba.’31. “Kada ku saurari Hezekiya. Ga abin da sarkin Assuriya ya ce, ku shirya zaman lafiya da ni, ku fito zuwa wurina. Kowane ɗayanku kuwa zai ci ’ya’yan inabinsa da ’ya’yan ɓaurensa, yă kuma sha ruwa daga randarsa,32. har lokacin da zan zo in kwashe ku, in kai ku wata ƙasa mai kama da taku, ƙasa mai yalwar hatsi, da ruwan inabi, da abinci, da gonakin inabi, da itatuwan zaitun, da zuma, don ku rayu, kada ku mutu! “Kada ku saurari Hezekiya, don karya yake muku, sa’ad da ya ce, ‘Ubangiji zai cece mu.’33. Akwai allahn wata al’ummar da ya taɓa ceton ƙasarsa daga hannun sarkin Assuriya?34. Ina allolin Hamat da na Arfad? Ina allolin Sefarfayim, da na Hena, da na Iffa? Sun cece Samariya daga hannuna?35. Wanne a cikin dukan allolin ƙasashen nan ya iya ceton ƙasarsa da gare ni? Shugaban sojojin ya kuma ci gaba da cewa, ta yaya Ubangiji zai ceci Urushalima daga hannuna?”36. Amma mutane suka yi shiru ba su amsa masa ba, domin sarki ya umarta cewa, “Kada ku amsa masa.”37. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf, marubuci, suka je wurin Hezekiya da tufafinsu a kece, suka faɗa masa abin da shugaban sojojin ya faɗa.Zabura 74:1-81. Me ya sa ka ƙi mu har abada, ya Allah? Me ya sa fushinka yake a kan tumakin kiwonka?2. Ka tuna da mutanen da ka saya tun da daɗewa, kabilar gādonka, wadda ka fansa, Dutsen Sihiyona, inda ka zauna.3. Ka juye sawunka wajen waɗannan madawwamin kufai, dukan wannan hallakar da abokin gāba ya yi wa wuri mai tsarki.4. Maƙiyanka sun yi ruri a inda ka sadu da mu; suka kakkafa tutotinsu a matsayin alamu.5. Sun yi kamar mutane masu wāshin gatura don yanka itatuwa a kurmi.6. Sun ragargaje dukan sassaƙar katako da gatura da kuma gudumarsu.7. Suka ƙone wurinka mai tsarki ƙurmus; suka ƙazantar da mazaunin Sunanka.8. Suna cewa a zukatansu, “Za mu murƙushe su sarai!” Suka ƙone ko’ina aka yi wa Allah sujada a ƙasar.Karin Magana 18:22-2422. Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.23. Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.24. Mutum mai abokai masu yawa kan lalace, amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.Ayyukan Manzanni 1:1-261. A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar2. har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.3. Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.4. A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai.5. Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”6. Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”7. Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa.8. Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”9. Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.10. Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su.11. Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”12. Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin.13. Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.14. Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.15. A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin)16. ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu17. dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”18. (Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo.19. Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)20. Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’21. Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu,22. farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”23. Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas.24. Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa25. ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.”26. Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.