Baibul a cikin shekara guda Yuni 162 Sarakuna 19:1-371. Da sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya shiga haikalin Ubangiji.2. Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna marubuci da shugabannin firistoci, dukansu sanye da tufafin makoki, zuwa wurin annabi Ishaya ɗan Amoz.3. Suka ce masa, “Hezekiya ya ce, yau ranar wahala ce, da ta cin mutunci, da ta shan kunya, ga shi, ’ya’ya suna gab da a haife su, amma ba ƙarfin da za a yi yunƙuri a haife su.4. Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka ya ji dukan maganganun sarkin yaƙi, wanda maigidansa, sarkin Assuriya, ya aiko don yă rena Allah mai rai. Bari Ubangiji Allahnka yă tsawata masa saboda maganar da ya ji. Saboda haka ka yi addu’a domin raguwar da har yanzu suke a raye.”5. Da fadawan sarki Hezekiya suka isa wurin Ishaya,6. Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su.7. Saurara! Zan sa masa wani ruhun da zai sa yă ji wata jita-jitar da za tă sa yă koma ƙasarsa. A can zan sa a kashe shi da takobi a ƙasarsa.’ ”8. Da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye, ya kuma iske sarkin yana yaƙi da Libna.9. To, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana zuwa masa da yaƙi. Saboda haka ya sāke aika manzanni zuwa wurin Hezekiya cewa,10. “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda, kada ka bar allahn da kake dogara gare shi yă ruɗe ka cewa, ‘Urushalima ba za tă fāɗi a hannun sarkin Assuriya ba.’11. Ba shakka ka riga ka ji abin da sarkin Assuriya ya yi da dukan ƙasashe, yana hallaka su gaba ɗaya. Kai kuwa kana ji za a cece ka?12. Allolin al’umman da kakannina suka hallaka, sun cece su ne, allolin Gozan, da na Haran, da na Rezef, da kuma na mutane Eden da suke a Tel Assar?13. Ina sarkin Hamat, da sarkin Arfad, da sarkin birnin Sefarfayim, ko na Hena da kuma na Iffa?”14. Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga manzannin ya karanta. Sa’an nan ya tashi ya tafi haikalin Ubangiji ya shimfiɗa wasiƙar a gaban Ubangiji.15. Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.16. Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka ji; ka buɗe idanunka ya Ubangiji ka gani; ka saurari kalmomin da Sennakerib ya aiko don yă yi wa Allah mai rai ba’a.17. “Da gaske ne, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriya sun hallakar da waɗannan al’ummai da ƙasashensu.18. Sun jefar da allolinsu cikin wuta, suka hallaka su, gama ba alloli ba ne, katakai ne da kuma duwatsu, ayyukan hannuwan mutane.19. To, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, don dukan mulkokin duniya su san cewa kai kaɗai, ya Ubangiji ne Allah.”20. Sai Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo zuwa wurin Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, na ji addu’arka game da Sennakerib sarkin Assuriya.21. Ga abin da Ubangiji yana cewa game da shi, “ ‘Budurwar Sihiyona ta rena ka tana kuma yin maka ba’a. Diyar Urushalima ta kaɗa kanta yayinda kake gudu.22. Wane ne ka zaga, ka kuma yi masa saɓo? Wa kake gāba da shi har ka ɗaga muryarka, har ka tā da idanunka da fahariya? Kana gāba da Mai Tsarki na Isra’ila!23. Ta wurin manzanninka ka tara wa Ubangiji zagi. Ka kuma ce, “Da yawa kekunan yaƙina na haye kan ƙwanƙolin duwatsu, wurin mafi tsawo na Lebanon. Na sassare itacen al’ul nasa mafi tsawo mafi daraja na itacen fir nasa. Na ratsa har can tsakiyar kurmi, mafi kyau na kurminsa.24. Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.”25. “ ‘Ba ka taɓa ji ba? Tun da daɗewa na ƙaddara haka. Tuntuni kuwa na shirya shi; yanzu kuma na sa ya faru, cewa ka mai da birane masu katanga tarin duwatsu.26. Ƙarfin mutanensu ya tsiyaye, suka razana aka kuma kunyata su. Suna kama da tsirai a gona, kamar sabon toho kamar ciyawa mai tohuwa bisa rufin ɗaki wanda ya bushe saboda zafi, kafin yă yi girma.27. “ ‘Amma na san wurin zamanka da fitarka da shigarka da yadda kake fushi da ni.28. Domin kana fushi da ni reninka ya iso kunnuwata, zan sa ƙugiyata a hancinka da linzamina a bakinka, zan kuma sa ka koma a ta hanyar da ka zo.’29. “Wannan zai zama alama a gare ka, ya Hezekiya, “Bana, za ku ci amfanin gonar da ya tsira da kansa, baɗi kuma amfanin gonar da ya tsiro daga na bara. Amma a shekara ta uku, za ku yi shuki, ku kuma girbe, ku dasa gonakin inabi, ku kuma ci ’ya’yansa.30. Sau ɗaya kuma ragowar masarautar Yahuda za tă yi saiwoyi a ƙasa ta kuma ba da ’ya’ya a bisa.31. Gama daga Urushalima za a sami ragowa, daga Dutsen Sihiyona kuma za a sami waɗanda suka tsira. Himmar Ubangiji Maɗaukaki za tă cika wannan.32. “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba ko yă harba kibiya a nan. Ba zai kusace ta da garkuwa ko yă yi mata zoben yaƙi ba.33. Ta hanyar da ya zo ne zai koma; ba zai shiga birnin nan ba, in ji Ubangiji.34. Zan kāre birnin nan in cece ta, saboda kaina da kuma bawana Dawuda.”35. A daren nan mala’ikan Ubangiji ya fita ya kashe dakaru dubu ɗari da tamanin da biyu a sansanin Assuriyawa. Da mutane suka farka da safe, sai ga gawawwaki ko’ina.36. Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya tā da sansanin ya kuma janye. Ya koma Ninebe ya zauna a can.37. Wata rana yayinda yake sujada a haikalin Nisrok, allahnsa, sai ’ya’yansa maza, Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka gudu zuwa ƙasar Ararat. Sai Esar-Haddon ɗansa ya gāje shi.2 Sarakuna 20:1-211. A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”2. Hezekiya ya juya fuskarsa wajen bango ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce,3. “Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.4. Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa,5. “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji.6. Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’ ”7. Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.8. Hezekiya ya tambayi Ishaya, “Wace alama ce za tă nuna cewa Ubangiji zai warkar da ni, kuma cewa in tafi haikalin Ubangiji kwana uku daga yanzu?”9. Sai Ishaya ya ce, “Ga alamar Ubangiji zuwa gare ka da za tă nuna cewa Ubangiji zai cika alkawarinsa. Kana so inuwa tă yi gaba da taki goma, ko tă koma baya da taki goma?”10. “Ai, abu mai sauƙi ne inuwa tă yi gaba da taki goma.” In ji Hezekiya, “Gwamma dai tă koma baya da taki goma.”11. Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina.12. A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya.13. Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba.14. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”15. Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.”16. Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji.17. Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji.18. Za a kuma kwashe waɗansu daga cikin zuriyarka, na jiki da jininka waɗanda za a haifa maka, su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”19. Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.”20. Game da sauran ayyukan mulkin Hezekiya, dukan nasarorinsa da yadda ya yi tafki da kuma bututun ruwa inda ya kawo ruwa cikin birni, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.21. Hezekiya ya huta tare da kakanninsa. Manasse ɗansa kuma ya gāje shi.2 Sarakuna 21:1-261. Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba.2. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.3. Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada.4. Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.”5. Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari.6. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.7. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.8. Ba zan ƙara sa Isra’ilawa su fita daga ƙasar da na ba kakanninsu ba, idan dai za su kula su aikata dukan abin da na umarce su, su kuma kiyaye dukan dokokin da na ba wa bawana Musa yă umarce su.”9. Amma mutanen ba su kasa kunne ba. Manasse ya ɓad da su, har suka yi muguntar da ta fi ta al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.10. Ubangiji ya yi magana ta bakin bayinsa annabawa,11. “Manasse, sarkin Yahuda ya aikata waɗannan ƙazantattun zunubai. Ya aikata mugunta fiye da ta Amoriyawan da suka riga shi, ya kuma sa Yahuda ta bauɗe ta wurin yin zunubi saboda gumakansa.12. Saboda haka ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, zan jawo wa Urushalima da kuma Yahuda masifar da duk kunnen da ya ji, sai ya kusa suma.13. Zan auna Urushalima da ma’aunin da na yi amfani da shi a kan Samariya, zan kuma yi amfani da magwajin da na yi amfani da shi a kan gidan Ahab. Zan shafe Urushalima yadda mutum yake wanke kwano yă kife.14. Zan rabu da ragowar gādona, in kuma miƙa su ga maƙiyansu. Abokan gābansu za su washe suka kuma kwashi ganima daga gare su,15. domin sun aikata mugunta a idanuna, suka kuma tsokane ni tun daga ranar da kakanninsu suka fito daga Masar, har yă zuwa yau.”16. Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.17. Game da sauran ayyukan mulkin Manasse, da duk abin da ya yi, har da zunubin da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.18. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a lambun fadansa, lambun Uzza. Sai Amon ɗansa ya gāje shi.19. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce.20. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi.21. Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu.22. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.23. Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.24. Sai mutanen ƙasar suka kashe duk waɗanda suka ƙulla wa Sarki Amon maƙarƙashiya, sa’an nan suka naɗa ɗansa sarki a maimakonsa.25. Game da sauran ayyukan mulkin Amon, da abubuwan da ya aikata, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda.26. Aka binne shi a kabarinsa a lambun Uzza. Yosiya ɗansa kuma ya gāje shi.Zabura 74:9-179. Ba a ba mu wata alama mai banmamaki ba; ba sauran annabawan da suka ragu, kuma babu waninmu da ya sani har yaushe wannan zai ci gaba.10. Har yaushe abokan gāba za su yi mana ba’a, ya Allah? Maƙiya za su ci gaba da ɓata sunanka har abada ne?11. Me ya sa ka janye hannunka, hannunka na dama? Ka fid da shi daga rigarka ka hallaka su!12. Amma kai, ya Allah, kai ne sarki tun da daɗewa; ka kawo ceto a kan duniya.13. Kai ne ka raba teku ta wurin ikonka; ka farfashe kawunan dodo a cikin ruwaye.14. Kai ne ka murƙushe kawunan dodon ruwa ka kuma ba da shi yă zama abinci ga halittun hamada.15. Kai ne ka bubbuɗe maɓulɓulai da rafuffuka; ka busar da koguna masu ruwa.16. Yini naka ne, dare kuma naka ne; ka kafa rana da wata.17. Kai ne ka kafa dukan iyakokin duniya; ka yi rani da damina.Karin Magana 19:1-21. Gara matalauci wanda yake marar laifi da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.2. Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya.Ayyukan Manzanni 2:1-211. Da ranar Fentekos ta yi, dukansu suna tare wuri ɗaya.2. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.3. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.4. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.5. To, a Urushalima akwai Yahudawa masu tsoron Allah, daga kowace ƙasa a duniya.6. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.7. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?8. To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?9. Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,10. Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma11. (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”12. A ruɗe kuma cike da mamaki, suka tambayi junansu cewa, “Mene ne wannan yake nufi?”13. Duk da haka waɗansu suka yi musu ba’a suka ce, “Sun yi tatil da ruwan inabi ne.”14. Sai Bitrus ya miƙe tsaye tare da Sha Ɗayan nan, ya ɗaga muryarsa ya yi wa taron jawabi ya ce, “’Yan’uwana Yahudawa da dukanku da kuke zama cikin Urushalima, bari in bayyana muku wannan, ku saurara da kyau ga abin da zan faɗa.15. Waɗannan mutane ba su bugu ba, kamar yadda kuka ɗauka. Yanzu ƙarfe tara na safe ne kawai!16. A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,17. “Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe, zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, samarinku za su ga wahayoyi, dattawanku kuma za su yi mafarkai.18. Kai, har ma a kan bayina, maza da mata, zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki, za su kuwa yi annabci.19. Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama da alamu a nan ƙasa, jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.20. Za a mai da rana duhu, wata kuma ya zama jini, kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.21. Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’ Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.