Baibul a cikin shekara guda Yuni 191 Tarihi 1:1-541. Adamu, Set, Enosh,2. Kenan, Mahalalel, Yared,3. Enok, Metusela, Lamek, Nuhu.4. ’Ya’yan Nuhu maza su ne, Shem, Ham da Yafet.5. ’Ya’yan Yafet maza su ne, Gomer, Magog, Madai, Yaban, Tubal, Meshek da Tiras.6. ’Ya’yan Gomer maza su ne, Ashkenaz, Rifat da Togarma.7. ’Ya’yan Yaban maza su ne, Elisha, Tarshish, Kittim da Rodanim.8. ’Ya’yan Ham maza su ne, Kush, Masar Fut da Kan’ana.9. ’Ya’yan Kush maza su ne, Seba, Hawila, Sabta, Ra’ama da Sabteka. ’Ya’yan Ra’ama maza su ne, Sheba da Dedan10. Kush shi ne mahaifin Nimrod, wanda ya yi girma ya zama babban jarumi a duniya.11. Masar shi ne mahaifin Ludiyawa, Anamawa, Lehabiyawa, Neftuhawa,12. Fatrusawa, Kasluhiyawa (daga waɗanda Filistiyawa suka fito) da Kaftorawa.13. Kan’ana shi ne mahaifin Sidon ɗan farinsa, da Hittiyawa,14. Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa15. Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,16. Arbadiyawa, Zemarawa da Hamawa.17. ’Ya’yan Shem maza su ne, Elam, Asshur, Arfakshad, Lud da Aram. ’Ya’yan Aram maza su ne, Uz, Hul, Geter da Meshek.18. Arfakshad shi ne mahaifin Shela, Shela kuwa shi ne mahaifin Eber.19. Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu. Aka kira ɗaya Feleg domin a lokacinsa ne aka raba duniya; sunan ɗan’uwansa kuwa shi ne Yoktan.20. Yoktan shi ne mahaifin Almodad, Shelef, Hazarmawet, Yera21. Hadoram, Uzal, Dikla,22. Ebal, Abimayel, Sheba,23. Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.24. Shem, Arfakshad, Shela,25. Eber, Feleg, Reyu26. Serug, Nahor, Tera27. da Abram (wato, Ibrahim).28. ’Ya’yan Ibrahim maza su ne, Ishaku da Ishmayel.29. Waɗannan su ne zuriyarsu. Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,30. Mishma, Duma, Massa, Hadad, Tema31. Yetur, Nafish da Kedema. Waɗannan su ne ’ya’yan Ishmayel maza.32. ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.33. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.34. Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila.35. ’Ya’yan Isuwa maza, su ne, Elifaz, Reyuwel, Yewush, Yalam da Kora36. ’Ya’yan Elifaz maza su ne, Teman, Omar, Zefi, Gatam, Kenaz, da Timna wanda aka haifa wa Amalek.37. ’Ya’yan maza Reyuwel su ne, Nahat, Zera, Shamma da Mizza.38. ’Ya’yan Seyir maza su ne, Lotan, Shobal, Zibeyon, Ana, Dishon, Ezer da Dishan.39. ’Ya’yan Lotan maza su ne, Hori da Homam. Timna ita ce ’yar’uwar Lotan.40. ’Ya’yan Shobal maza su ne, Alwan, Manahat, Ebal, Shefo da Onam. ’Ya’yan Zibeyon maza su ne, Aiya da Ana.41. Ɗan Ana shi ne, Dishon. ’Ya’yan Dishon maza su ne, Hemdan, Eshban, Itran da Keran.42. ’Ya’yan Ezer maza su ne, Bilhan, Za’aban da Ya’akan. ’Ya’yan Dishan maza su ne, Uz da Aran.43. Waɗannan su ne sarakunan da suka yi sarauta a Edom kafin wani sarkin mutumin Isra’ila yă yi sarauta. Bela ɗan Beyor, wanda aka kira birninsa Dinhaba.44. Sa’ad da Bela ya mutu sai Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi a matsayin sarki.45. Da Yobab ya mutu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi a matsayin sarki.46. Sa’ad da Husham ya mutu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a cikin ƙasar Mowab, ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Awit.47. Da Hadad ya mutu, Samla daga Masreka ya gāje shi a matsayin sarki.48. Sa’ad da Samla ya mutu, Sha’ul daga Rehobot na kogi ya gāje shi a matsayin sarki.49. Sa’ad da Sha’ul ya mutu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi a matsayin sarki.50. Sa’ad da Ba’al-Hanan ya mutu, Hadad ya gāje shi a matsayin sarki. Aka kira birninsa Fau, sunan matarsa kuwa Mehetabel ’yar Matired, ’yar Me-Zahab.51. Hadad shi ma ya mutu. Manyan Edom su ne, Timna, Alwa, Yetet52. Oholibama, Ela, Finon53. Kenaz, Teman, Mibzar,54. Magdiyel da Iram. Waɗannan su ne manyan Edom.1 Tarihi 2:1-551. Waɗannan su ne ’ya’yan Isra’ila maza. Ruben, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Zebulun,2. Dan, Yusuf, Benyamin, Naftali, Gad da Asher.3. ’Ya’yan Yahuda maza su ne, Er, Onan da Shela. Waɗannan mutum uku Bat-shuwa mutuniyar Kan’ana ce ta haifa masa. Er, ɗan farin Yahuda mugu ne a gaban Ubangiji, saboda haka Ubangiji ya kashe shi.4. Tamar, surukar Yahuda, ta haifa masa Ferez da Zera. Yahuda ya haifi ’ya’ya maza biyar ne.5. ’Ya’yan Ferez maza su ne, Hezron da Hamul.6. ’Ya’yan Zera maza su ne, Zimri, Etan, Heman, Kalkol da Darda, su biyar ne.7. ’Ya’yan Karmi maza su ne, Akar wanda ya kawo masifa wa Isra’ila ta wurin yin abin da aka haramta.8. Ɗan Etan shi ne, Azariya.9. ’Ya’ya maza da aka haifa wa Hezron su ne, Yerameyel, Ram da Kaleb.10. Ram shi ne mahaifin Amminadab, Amminadab kuwa shi ne mahaifin Nashon, shugaban mutanen Yahuda.11. Nashon shi ne mahaifin Salma, Salma shi ne mahaifin Bowaz,12. Bowaz shi ne mahaifin Obed kuma Obed shi ne mahaifin Yesse.13. Yesse shi ne mahaifin. Eliyab ɗan farinsa, ɗansa na biyu shi ne Abinadab, na ukun Shimeya,14. na huɗun Netanel, na biyar Raddai,15. na shidan Ozem na bakwai kuma Dawuda.16. ’Yan’uwansu mata su ne Zeruhiya da Abigiyel. ’Ya’yan Zeruhiya maza guda uku su ne Abishai, Yowab da Asahel.17. Abigiyel ita ce mahaifiyar Amasa, wanda mahaifinsa shi ne Yeter mutumin Ishmayel.18. Kaleb ɗan Hezron ya haifi yara ta wurin matarsa Azuba (da kuma ta wurin Yeriyot). Waɗannan su ne ’ya’yan Azuba maza. Yesher, Shobab da Ardon.19. Da Azuba ta mutu, Kaleb ya auri Efrat, wadda ta haifa masa Hur.20. Hur shi ne mahaifin Uri, Uri kuma shi ne mahaifin Bezalel.21. Daga baya, Hezron ya kwana da ’yar Makir mahaifin Gileyad (ya aure ta sa’ad da take da shekara sittin), ta haifa masa Segub.22. Segub shi ne mahaifin Yayir, wanda ya yi mulkin garuruwa uku a Gileyad.23. (Amma Geshur da Aram suka ƙwace Hawwot Yayir da kuma Kenat tare da ƙauyukan kewayenta, garuruwa sittin.) Dukan waɗannan su ne zuriyar Makir mahaifin Gileyad.24. Bayan Hezron ya mutu a Kaleb Efrata, sai Abiya matar Hezron ta haifa masa Asshur mahaifin Tekowa.25. ’Ya’yan Yerameyel maza, ɗan farin Hezron su ne, Ram shi ne ɗan fari, sai Buna, Oren, Ozem da Ahiya.26. Yerameyel yana da wata mata, wadda sunanta Atara; ita ce mahaifiyar Onam.27. ’Ya’yan Ram maza ɗan farin Yerameyel su ne, Ma’az, Yamin da Eker.28. ’Ya’yan Onam maza su ne, Shammai da Yada. ’Ya’yan Shammai maza su ne, Nadab da Abishur.29. Sunan matar Abishur ita ce Abihayil, wadda ta haifa masa Aban da Molid.30. ’Ya’yan Nadab maza su ne, Seled da Affayim. Seled ya mutu babu yara.31. Ɗan Affayim shi ne, Ishi, wanda shi ne mahaifin Sheshan. Sheshan shi ne mahaifin Alai.32. ’Ya’yan Yada maza, ɗan’uwan Shammai su ne, Yeter da Yonatan. Yeter ya mutu babu yara.33. ’Ya’yan Yonatan maza su ne, Felet da Zaza. Waɗannan su ne zuriyar Yerameyel.34. Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha.35. Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.36. Attai shi ne mahaifin Natan, Natan shi ne mahaifin Zabad,37. Zabad shi ne mahaifin Eflal, Eflal shi ne mahaifin Obed,38. Obed shi ne mahaifin Yehu, Yehu shi ne mahaifin Azariya,39. Azariya shi ne mahaifin Helez, Helez shi ne mahaifin Eleyasa,40. Eleyasa shi ne mahaifin Sismai, Sismai shi ne mahaifin Shallum41. Shallum shi ne mahaifin Yekamiya, Yekamiya kuma shi ne mahaifin Elishama.42. ’Ya’yan Kaleb maza, ɗan’uwan Yerameyel su ne, Mesha ɗan farinsa, wanda shi ne mahaifin Zif, da ɗansa Maresha, wanda shi ne mahaifin Hebron.43. ’Ya’yan Hebron maza su ne, Kora, Taffuwa, Rekem da Shema.44. Shema shi ne mahaifin Raham, Raham kuma shi ne mahaifin Yorkeyam. Rekem shi ne mahaifin Shammai.45. Ɗan Shammai shi ne Mawon, Mawon kuma shi ne mahaifin Bet-Zur.46. Efa ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Haran, Moza da Gazez. Haran shi ne mahaifin Gazez.47. ’Ya’yan Yadai maza su ne, Regem, Yotam, Geshan, Felet, Efa da Sha’af.48. Ma’aka ƙwarƙwarar Kaleb ita ce mahaifiyar Sheber da Tirhana.49. Ta kuma haifi Sha’af mahaifin Madmanna da kuma Shewa, mahaifin Makbena da Gibeya. ’Yar Kaleb ita ce Aksa.50. Waɗannan su ne zuriyar Kaleb. ’Ya’yan Hur maza, ɗan farin Efrata su ne, Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim,51. Salma mahaifin Betlehem, da kuma Haref mahaifin Bet-Gader.52. Zuriyar Shobal mahaifin Kiriyat Yeyarim su ne, Harowe, rabin Manahatiyawa,53. kuma gidan Kiriyat Yeyarim su ne, Itrayawa, Futiyawa, Shumatiyawa da Mishratiyawa. Daga waɗannan ne Zoratiyawa da Eshtawoliyawa suka fito.54. Zuriyar Salma su ne, Betlehem, Netofawa, Atrot Bet Yowab, rabin Manahatiyawa, Zoriyawa,55. kuma gidan marubuta waɗanda suke zama a Yabez su ne, Tiratiyawa, Shimeyatiyawa da Sukatiyawa. Waɗannan su ne Keniyawa waɗanda suka zo daga Hammat, mahaifin gidan Rekab.Zabura 76:1-61. A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.2. Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.3. A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi.4. Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.5. Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.6. A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.Karin Magana 19:6-76. Kowa na ƙoƙari ya sami farin jini wurin mai mulki, kuma kowa na so a ce shi abokin mutumin nan mai yawan kyauta ne.7. ’Yan’uwan matalauci sukan guje shi, balle abokansa, su ma za su guje shi. Ko da yake matalaucin yana binsu yana roƙo, ba zai sam su ba.Ayyukan Manzanni 4:1-221. Sai firistoci da shugaban masu gadin haikalin da kuma Sadukiyawa suka hauro wurin Bitrus da Yohanna yayinda suke cikin magana da mutane.2. Sun damu ƙwarai da gaske domin manzannin suna koya wa mutane suna kuma shela a cikin Yesu cewa akwai tashin matattu.3. Sai suka kama Bitrus da Yohanna, amma da yake yamma ta riga ta yi sai suka sa su cikin kurkuku sai kashegari.4. Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.5. Kashegari, sai masu mulki, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru a Urushalima.6. Annas babban firist yana nan, haka ma Kayifas Yohanna, Alekzanda da kuma sauran mutanen da suke iyalin babban firist.7. Suka sa aka kawo Bitrus da Yohanna a gabansu suka kuma fara yin musu tambayoyi cewa, “Da wane iko ko da wane suna kuka yi wannan?”8. Sai Bitrus, cike da Ruhu Mai Tsarki ya ce musu, “Masu mulki da dattawan mutane!9. In ana tuhumarmu ne yau saboda alherin da aka yi wa gurgun nan da kuma yadda aka warkar da shi,10. to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye.11. Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’12. Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”13. Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.14. Amma da yake sun ga mutumin da aka warkar yana tsaye a wurin tare da su, sai suka rasa abin faɗi.15. Saboda haka suka umarta a fitar da su daga Majalisar, sa’an nan suka yi shawara da juna.16. Suka ce, “Me za mu yi da waɗannan mutane? Kowa da yake zama a Urushalima ya san sun yi abin banmamaki, kuma ba za mu iya yin mūsu wannan ba.17. Amma don a hana wannan abu daga ƙara bazuwa cikin mutane, dole mu kwaɓe mutanen nan kada su ƙara yi wa kowa magana cikin wannan suna.”18. Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu.19. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah.20. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”21. Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.22. Gama mutumin da ya sami warkarwar banmamaki, shekarunsa sun fi arba’in. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.