Baibul a cikin shekara guda Yuni 201 Tarihi 3:1-241. Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron. Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;2. na ukun, Absalom ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;3. na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.4. Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida. Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,5. kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can. Shimeya, Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa ’yar Ammiyel ta haifa.6. Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet,7. Noga, Nefeg, Yafiya,8. Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka.9. Dukan waɗannan ’ya’yan Dawuda ne maza, ban da ’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce ’yar’uwarsu.10. Zuriyar Solomon su ne Rehobowam, da Abiya, da Asa, da Yehoshafat,11. da Yoram, da Ahaziya, da Yowash,12. da Amaziya, da Azariya, da Yotam,13. da Ahaz, da Hezekiya da Manasse,14. da Amon, da Yosiya.15. ’Ya’yan Yosiya maza su ne, Yohanan ɗan fari, Yehohiyakim ɗa na biyu, Zedekiya ɗa na uku Shallum ɗa na huɗu.16. Magādan Yehohiyakim su ne, Yekoniya ɗansa, da Zedekiya.17. Zuriyar Yekoniya kamamme su ne, Sheyaltiyel,18. Malkiram, Fedahiya, Shenazzar, Yekamiya, Hoshama da Nedabiya.19. ’Ya’yan Fedahiya su ne, Zerubbabel da Shimeyi. ’Ya’yan Zerubbabel maza su ne, Meshullam da Hananiya. Shelomit ce ’yar’uwarsu.20. Akwai kuma waɗansu biyar, Hashuba, Ohel, Berekiya, Hasadiya da Yushab-Hesed.21. Zuriyar Hananiya su ne, Felatiya da Yeshahiya, Refahiya, Arnan, Obadiya da Shekaniya.22. Zuriyar Shekaniya su ne, Shemahiya da ’ya’yansa maza. Hattush, Igal, Bariya, Neyariya da Shafat, su shida ne duka.23. ’Ya’yan Neyariya maza su ne, Eliyohenai, Hezekiya da Azrikam, su uku ne duka.24. ’Ya’yan Eliyohenai su ne, Hodawiya, Eliyashib, Felahiya, Akkub, Yohanan, Delahiya da Anani, su bakwai ne duka.1 Tarihi 4:1-431. Zuriyoyin Yahuda su ne, Ferez, Hezron, Karmi, Hur da Shobal.2. Reyahiya ɗan Shobal shi ne mahaifin Yahat, Yahat shi ne mahaifin Ahumai da Lahad. Waɗannan su ne gidajen Zoratiyawa.3. Waɗannan su ne ’ya’yan Etam. Yezireyel, Ishma da Idbash. ’Yar’uwarsu ita ce Hazzelelfoni.4. Fenuwel shi ne mahaifin Gedor, kuma Ezer shi ne mahaifin Husha. Waɗannan su ne zuriyar Hur, ɗan farin Efrata da mahaifin Betlehem.5. Asshur mahaifin Tekowa yana da mata biyu, Hela da Na’ara.6. Na’ara ta haifi Ahuzzam, Hefer, Temeni da Hawahashtari. Waɗannan su ne zuriyar Na’ara.7. ’Ya’yan Hela maza su ne, Zeret, Zohar, Etnan,8. da Koz. Koz ne mahaifin Anub da Hazzobeba, shi ne kuma kakan iyalin da suka fito daga zuriyar Aharhel ɗan Harum.9. Yabez ya fi ’yan’uwansa martaba. Mahaifiyarsa ta sa masa suna Yabez, tana cewa, “Na haife shi da azaba.”10. Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.11. Kelub, ɗan’uwan Shuha, shi ne mahaifin Mehir, wanda shi ne mahaifin Eshton.12. Eshton shi ne mahaifin Bet-Rafa, Faseya da Tehinna wanda ya haifi Ir Nahash. Waɗannan su ne mutanen Reka.13. ’Ya’yan Kenaz maza su ne, Otniyel da Serahiya. ’Ya’yan Otniyel maza su ne, Hatat da Meyonotai.14. Meyonotai shi ne mahaifin Ofra. Serahiya shi ne mahaifin Yowab, mahaifin Ge-Harashim. An kira shi haka domin mutanensa masu sana’ar hannu ne.15. ’Ya’yan Kaleb ɗan Yefunne maza su ne, Iru, Ela da Na’am. Ɗan Ela shi ne, Kenaz.16. ’Ya’yan Yahallelel su ne, Zif, Zifa, Tiriya da Asarel.17. ’Ya’yan Ezra maza su ne, Yeter, Mered, Efer da Yalon. Ɗaya daga cikin matan Mered ta haifi Miriyam, Shammai da Ishba wanda ya haifi Eshtemowa.18. (Matarsa mutuniyar Yahuda kuwa ta haifi Yared mahaifin Gedor, Heber mahaifin Soko, da kuma Yekutiyel mahaifin Zanowa.) Waɗannan su ne ’ya’yan Bitiya ’yar Fir’auna, wadda Mered ya aura.19. ’Ya’yan matar Hodiya, ’yar’uwar Naham su ne, suka haifi Keyila Bagarme, da Eshtemowa mutumin Ma’aka.20. ’Ya’yan Shimon maza su ne, Amnon, Rinna, Ben-Hanan da Tilon. Zuriyar Ishi su ne, Zohet da Ben-Zohet.21. ’Ya’yan Shela ɗan Yahuda maza su ne, Er mahaifin Leka, La’ada mahaifin Maresha da kuma gidajen masu aikin lilin a Bet-Ashbeya,22. da Yokim, mutanen Kozeba, da Yowash da Saraf wanda ya yi mulkin Mowab da kuma Yashubi Lehem (Waɗannan rubutattun tarihi ne na tun dā.)23. Su ne maginan tukwane waɗanda suka zauna a Netayim da Gedera; sun zauna a can suka kuma yi wa sarki aiki.24. Zuriyar Simeyon su ne, Nemuwel, Yamin, Yarib, Zera da Shawulu;25. Shawulu ya haifi Shallum, Shallum ya haifi Mibsam. Mibsam ya haifi Mishma.26. Zuriyar Mishma su ne, Hammuwel ɗansa, wanda ya haifi Zakkur, shi Zakkur kuma ya haifi Shimeyi.27. Shimeyi yana da ’ya’ya maza goma sha shida da ’ya’ya mata shida, amma ’yan’uwansa ba su da ’ya’ya da yawa; saboda haka gidansu gaba ɗaya ba tă zama mai mutane da yawa kamar mutanen Yahuda ba.28. Sun zauna a Beyersheba, Molada, Hazar Shuwal,29. Bilha, Ezem, Tolad30. Betuwel, Horma, Ziklag,31. Bet-Markabot, Hazar-Susim, Bet-Biri da Sha’arayim. Waɗannan su ne garuruwansu har lokacin mulkin Dawuda.32. Ƙauyukan da suke kewayensu su ne Etam, Ayin, Rimmon, Token da Ashan, garuruwa biyar;33. da kuma dukan ƙauyuka kewaye da waɗannan garuruwa har zuwa Ba’al. Waɗannan ne wuraren zamansu. Suka kuma ajiye tarihin zuriya.34. Zuriyar Simeyon ta ƙunshi Meshobab, da Yamlek, da Yosha ɗan Amaziya.35. Akwai Yowel, da Yehu ɗan Yoshibiya. Yoshibiya ɗan Seraya ne. Serahiya kuma ɗan Asiyel ne.36. Akwai Eliyohenai da Ya’akoba, da Yeshohahiya, da Asahiya, da Adiyel, da Yesimiyel, da Benahiya.37. Akwai Ziza ɗan Shifi. Shifi ɗan Allon ne. Allon ɗan Yedahiya ne. Yedahiya ɗan Shimri ne. Shimri kuma ɗan Shemahiya ne.38. Mutanen da aka jera sunayensu a bisa, shugabannin gidajensu ne. Iyalansu sun ƙaru sosai,39. suka tafi bayan garin Gedor wajajen gabashin kwari suna neman makiyaya domin garkunansu.40. Suka sami makiyaya mai ciyawa mai kyau, ƙasar kuma tana da fāɗi, da salama, kuma zaman lafiya. A dā waɗansu mutanen Ham sun zauna a can.41. Mutanen da aka jera sunayensu sun zo ne a zamanin Hezekiya sarkin Yahuda. Suka yaƙi mutanen Ham a wuraren zamansu, haka kuma suka yi da Meyunawa da suke can, suka hallaka su ƙaƙaf, yadda yake har yă zuwa yau. Sa’an nan suka zauna a wurin, gama akwai makiyaya domin garkunansu.42. Mutum ɗari biyar na waɗannan mutane Simeyon, waɗanda Felatiya, Neyariya, Refahiya da Uzziyel, ’ya’yan Ishi maza suka jagorance, sun mamaye ƙasar tudu ta Seyir.43. Suka karkashe raguwar Amalekawan da suka tsere, suka kuma zauna a can har yă zuwa yau.Zabura 76:7-127. Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?8. Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,9. sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar.10. Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.11. Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.12. Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.Karin Magana 19:8-98. Duk wanda ya sami hikima yana ƙaunar ransa; duka wanda yake jin daɗi fahimi kan ci gaba.9. Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.Ayyukan Manzanni 4:23-3723. Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu.24. Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.25. Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa, “ ‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza?26. Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’27. Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe.28. Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru.29. Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali.30. Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.”31. Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.32. Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi.33. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.34. Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar,35. su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.36. Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa)37. ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.