Baibul a cikin shekara guda Yuni 211 Tarihi 5:1-261. ’Ya’yan Ruben maza ɗan farin Isra’ila (shi ne ɗan fari, amma sa’ad da ya ƙazantar da gadon auren mahaifinsa, sai aka ba wa ’yancin ɗan farinsa wa ’ya’yan Yusuf maza ɗan Isra’ila; don kada a lissafta shi a tarihin zuriya bisa ga matsayin haihuwarsa,2. ko da yake Yahuda shi ne mafi ƙarfi cikin ’yan’uwansa kuma mai mulki ya fito daga gare shi, ’yancin zaman ɗan fari na Yusuf ne),3. ’ya’yan Ruben ɗan farin Isra’ila maza su ne, Hanok, Fallu, Hezron da Karmi.4. Zuriyar Yowel su ne, Shemahiya, Gog, Shimeyi,5. Mika, Reyahiya, Ba’al,6. da Beyera, wanda Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya ɗauka zuwa zaman bauta. Beyera shi ne shugaban mutanen Ruben.7. Danginsu bisa ga iyalansu da aka jera bisa ga tarihin zuriyarsu su ne, Yehiyel shi ne sarki, akwai Zakariya,8. da Bela ɗan Azaz. Azaz ɗan Shema daga dangin Yowel. Yowel ya yi zama a yankin Arower har zuwa Nebo da Ba’al-Meyon.9. Ta waje gabas sun zauna a ƙasar har zuwa bakin hamadan da ya nausa zuwa Kogin Yuferites, domin dabbobinsu sun ƙaru a Gileyad.10. A zamanin Shawulu zuriyar Ruben sun yi yaƙi da Hagirawa, suka ci su da yaƙi, suka zauna a wuraren zaman Hagirawan ko’ina a dukan yankin gabashin Gileyad.11. Mutanen Gad sun zauna kusa da mutanen Ruben a Bashan, har zuwa Saleka.12. Yowel shi ne babba, sai Shafan na biyu, sa’an nan Yanai da Shafat, su ne tushen Bashan.13. Danginsu, bisa ga iyalai su ne, Mika’ilu, Meshullam, Sheba, Yorai, Yakan, Ziya da Eber, su bakwai ne duka.14. Waɗannan su ne ’ya’yan Abihayil ɗan Huri, ɗan Yarowa, ɗan Gileyad, ɗan Mika’ilu, ɗan Yeshishai, ɗan Yado, ɗan Buz.15. Ahi ɗan Abiyel, ɗan Guni, shi ne kan iyalinsu.16. Mutanen Gad sun zauna a Bashan da ƙauyukan da suke kurkusa da shi, da kuma a dukan makiyayan Sharon har zuwa iyaka inda suka kai.17. Dukan waɗannan sun shiga tarihin zuriya a lokacin mulkin Yotam sarkin Yahuda da Yerobowam sarkin Isra’ila.18. Mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse sun kasance da mutane 44,760 shiryayyu don aikin soja, jarumawan da za su iya riƙe garkuwa da takobi, waɗanda suke iya yin amfani da baka, waɗanda kuma aka horar don yaƙi.19. Suka yi yaƙi da Hagirawa, Yetur, Nafish da Nodab.20. Aka taimake su a yaƙin, Allah kuma ya ba da Hagirawa da dukan abokansu gare su, domin sun yi kuka gare shi a lokacin yaƙin. Ya amsa addu’o’insu, domin sun dogara gare shi.21. Suka ƙwace dabbobin Hagirawa, raƙuma dubu hamsin, tumaki dubu ɗari biyu da hamsin da kuma jakuna dubu biyu. Suka kuma kame mutane dubu ɗari ɗaya,22. waɗansu suka mutu, domin yaƙin na Allah ne. Suka zauna a ƙasar har lokacin da aka kai su zaman bauta.23. Mutanen rabin kabilar Manasse sun yi yawa; suka zauna a ƙasar daga Bashan har zuwa Ba’al-Hermon, wato, zuwa Senir (Dutsen Hermon).24. Waɗannan su ne kawunan iyalansu. Efer, Ishi, Eliyel, Azriyel, Irmiya, Hodawiya da Yadiyel. Su jarumawa ne, sanannu, su ne kuma kawunan iyalansu.25. Amma ba su yi aminci da Allahn kakanninsu ba, suka kuma yi karuwanci ga waɗansu allolin mutanen ƙasar, waɗanda Allah ya hallaka a gabansu.26. Saboda haka Allah na Isra’ila ya zuga ruhun Ful sarkin Assuriya (wato, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya), wanda ya kwashe mutanen Ruben, mutanen Gad da rabin kabilar Manasse zuwa zaman bauta. Ya kwashe su zuwa Hala, Habor, Hara da kuma kogin Gozan, inda suke har wa yau.1 Tarihi 6:1-811. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershon, Kohat da Merari.2. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.3. Yaran Amram su ne, Haruna, Musa da Miriyam. ’Ya’yan Haruna maza su ne, Nadab, Abihu, Eleyazar da Itamar.4. Eleyazar shi ne mahaifin Finehas, Finehas mahaifin Abishuwa,5. Abishuwa mahaifin Bukki, Bukki mahaifin Uzzi,6. Uzzi mahaifin Zerahiya, Zerahiya mahaifin Merahiyot,7. Merahiyot mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,8. Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Ahimawaz,9. Ahimawaz mahaifin Azariya, Azariya mahaifin Yohanan,10. Yohanan mahaifin Azariya (shi ne ya yi hidima a matsayin firist a haikalin da Solomon ya gina a Urushalima),11. Azariya mahaifin Amariya, Amariya mahaifin Ahitub,12. Ahitub mahaifin Zadok, Zadok mahaifin Shallum,13. Shallum mahaifin Hilkiya, Hilkiya mahaifin Azariya,14. Azariya mahaifin Serahiya, Serahiya kuwa mahaifin Yehozadak.15. Yehozadak ne aka ɗauka sa’ad da Ubangiji ya tura Yahuda da Urushalima zuwa zaman bauta ta hannun Nebukadnezzar.16. ’Ya’yan Lawi maza su ne, Gershom, Kohat da Merari.17. Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Gershom. Libni da Shimeyi.18. ’Ya’yan Kohat maza su ne, Amram, Izhar, Hebron da Uzziyel.19. ’Ya’yan Merari maza su ne, Mali da Mushi. Waɗannan suke gidajen Lawiyawan da aka jera bisa ga kakanninsu.20. Na Gershom su ne, Libni, Yahat, Zimma,21. Yowa, Iddo, Zera da Yeyaterai.22. Zuriyar Kohat su ne, Amminadab, Kora, Assir,23. Elkana, Ebiyasaf, Assir,24. Tahat, Uriyel, Uzziya da Shawulu.25. Zuriyar Elkana su ne, Amasai, Ahimot,26. Elkana, Zofai, Nahat,27. Eliyab Yeroham, Elkana da Sama’ila.28. ’Ya’yan Sama’ila maza su ne, Yowel ɗan fari da Abiya ɗa na biyu.29. Zuriyar Merari su ne, Mali, Libni, Shimeyi, Uzza,30. Shimeya, Haggiya da Asahiya.31. Waɗannan su ne mutanen da Dawuda ya sa su lura da waƙa a cikin gidan Ubangiji bayan da aka kawo akwatin alkawari yă huta a can.32. Suka yi hidima da waƙa a gaban tabanakul, Tentin Sujada, sai da Solomon ya gina haikalin Ubangiji a Urushalima. Suka yi ayyukansu bisa ga ƙa’idodin da aka shimfiɗa musu.33. Ga mutanen da suka yi hidimar, tare da ’ya’yansu maza. Daga mutanen Kohat akwai, Heman, mawaƙi ɗan Yowel, ɗan Sama’ila,34. ɗan Elkana, ɗan Yeroham, ɗan Eliyel, ɗan Towa,35. ɗan Zuf, ɗan Elkana, ɗan Mahat, ɗan Amasai,36. ɗan Elkana, ɗan Yowel, ɗan Azariya, ɗan Zefaniya37. ɗan Tahat, ɗan Assir, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora,38. ɗan Izhar, ɗan Kohat, ɗan Lawi, ɗan Isra’ila;39. da kuma Asaf ’yan’uwan Heman, waɗanda suka yi hidima a hannun damansa. Asaf ɗan Berekiya, ɗan Shimeya,40. ɗan Mika’ilu, ɗan Ba’asehiya, ɗan Malkiya,41. ɗan Etni, ɗan Zera, ɗan Adahiya42. ɗan Etan, ɗan Zimma, ɗan Shimeyi,43. ɗan Yahat, ɗan Gershom, ɗan Lawi;44. da kuma daga ’yan’uwansu, mutanen Merari, a hannun hagunsa. Etan ɗan Kishi, ɗan Abdi, ɗan Malluk,45. ɗan Hashabiya, ɗan Amaziya, ɗan Hilkiya,46. ɗan Amzi, ɗan Bani, ɗan Shemer,47. ɗan Mali, ɗan Mushi, ɗan Merari, ɗan Lawi.48. Aka ba ’yan’uwansu Lawiyawa dukan sauran ayyukan tabanakul, gidan Allah.49. Amma Haruna da zuriyarsa su ne waɗanda suke miƙa hadayu a kan bagaden hadaya ta ƙonawa da kuma a kan bagaden turare haɗe da dukan abin da ake yi a Wuri Mafi Tsarki, suna yin kafara domin Isra’ila, bisa ga dukan abin da Musa bawan Allah ya umarta.50. Waɗannan su ne zuriyar Haruna, Eleyazar, Finehas, Abishuwa,51. Bukki, Uzzi, Zerahiya,52. Merahiyot, Amariya, Ahitub,53. Zadok da Ahimawaz.54. Waɗannan su ne wuraren zamansu da aka ba su rabo su zama yankunansu (aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga gidan Kohat, domin rabo na fari nasu ne):55. Aka ba su Hebron a Yahuda tare da wuraren kiwon da suke kewayenta.56. Amma filaye da ƙauyukan da suke kewayen birnin aka ba wa Kaleb ɗan Yefunne.57. Saboda haka aka ba wa zuriyar Haruna Hebron (birnin mafaka), da Libna, Yattir Eshtemowa,58. Hilen, Debir,59. Ashan, Yutta da Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu.60. Daga kabilar Benyamin kuma aka ba su Gibeyon, Geba, Alemet da Anatot, tare da wuraren kiwonsu. Waɗannan garuruwa waɗanda aka raba a tsakanin mutanen gidan Kohat, goma sha uku ne duka.61. Aka ba sauran zuriyar Kohat rabon garuruwa goma daga gidajen rabin kabilar Manasse.62. Aka ba zuriyar Gershom, gida-gida, rabon garuruwa goma sha uku daga kabilan Issakar, Asher da Naftali, da kuma daga sashen rabi kabilar Manasse da yake a Bashan.63. Aka ba zuriyar Merari, gida-gida, rabon garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.64. Saboda haka Isra’ilawa suka ba Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwonsu.65. Daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin suka ba su rabon sunayen garuruwan da aka ambata.66. Aka ba wa waɗansu na mutanen gidan Kohat yankin garuruwansu daga kabilar Efraim.67. A ƙasar tudun Efraim aka ba su Shekem (birnin mafaka), da Gezer,68. Yokmeyam, Bet-Horon,69. Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu.70. Daga rabin kabilar Manasse kuwa, Isra’ilawa suka ba da Aner da Bileyam, tare da wuraren kiwonsu, ga sauran gidajen mutanen Kohat.71. Mutanen Gershom suka sami waɗannan. Daga gidan rabin kabilar Manasse, sun sami Golan a Bashan da kuma Ashtarot, tare da wuraren kiwonsu;72. daga kabilar Issakar suka sami Kedesh, Daberat,73. Ramot da Anem, tare da wuraren kiwonsu;74. daga kabilar Asher suka sami Mashal, Abdon,75. Hukok da Rehob, tare da wuraren kiwonsu;76. daga kabilar Naftali kuwa suka sami Kedesh a Galili, Hammon da Kiriyatayim, tare da wuraren kiwonsu.77. Mutanen Merari (sauran Lawiyawan) suka sami waɗannan. Daga kabilar Zebulun suka sami Yokneyam, Karta, Rimmon da Tabor, tare da wuraren kiwonsu;78. daga kabilar Ruben a hayin Urdun a gabashi Yeriko suka sami Bezer a hamada, Yahza,79. Kedemot da Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu;80. daga kabilar Gad kuwa suka sami Ramot a Gileyad, Mahanayim,81. Heshbon da Yazer, tare da wuraren kiwonsu.Zabura 77:1-31. Na yi kuka ga Allah don taimako; na yi kuka ga Allah don yă ji ni.2. Sa’ad da nake cikin damuwa, na nemi Ubangiji; da dare na miƙa hannuwa ba gajiya raina kuma ya ƙi yă ta’azantu.3. Na tuna da kai, ya Allah, na kuma yi nishi; na yi nishi, ƙarfina kuwa duk ya raunana.Karin Magana 19:10-1210. Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki!11. Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi.12. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.Ayyukan Manzanni 5:1-211. To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa.2. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.3. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?4. Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”5. Da Ananiyas ya ji wannan, sai ya fāɗi ya mutu. Sai babban tsoro kuwa ya kama duk waɗanda suka ji abin da ya faru.6. Sai samari suka zo gaba, suka naɗe gawarsa, suka fitar da shi suka je suka binne.7. Bayan kusan awa uku, sai matarsa ta shigo, ba da sanin abin da ya faru ba.8. Bitrus ya tambaye ta ya ce, “Gaya mini, kuɗin da yake da Ananiyas kuka sayar da filin ke nan?” Ta ce, “I, haka ne muka sayar.”9. Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”10. Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.11. Babban tsoro ya kama dukan ikkilisiya da kuma duk wanda ya ji game da abubuwan nan.12. Manzannin suka yi ayyukan da alamu masu banmamaki masu yawa a cikin mutanen. Dukan masu bi kuwa sukan taru a Shirayin Solomon.13. Ba wanda ya yi karambanin shiga cikinsu, duk da haka mutane suna girmama su ƙwarai.14. Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa.15. A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa.16. Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.17. Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi.18. Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa.19. Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su.20. Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”21. Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.