Baibul a cikin shekara guda Yuni 221 Tarihi 7:1-401. ’Ya’yan Issakar maza su ne, Tola, Fuwa, Yashub da Shimron, su huɗu ne duka.2. ’Ya’yan Tola maza su ne, Uzzi, Refahiya, Yeriyel, Ibsam da Sama’ila, su ne kuma kawunan iyalansu. A zamanin mulkin Dawuda, an rubuta zuriyar Tola a matsayin mayaƙa a cikin tarihinsu, sun kai 22,600.3. Ɗan Uzzi shi ne, Izrahiya. ’Ya’yan Izrahiya maza su ne, Mika’ilu, Obadiya, Yowel da Isshiya. Dukansu biyar manya ne.4. Bisa ga tarihin iyalinsu, sun kai mutane 36,000 shiryayyu don yaƙi, gama suna da mata da ’ya’ya da yawa.5. Dangin da suke maza masu yaƙi sun kasance na dukan gidajen Issakar ne, kamar yadda aka rubuta a cikin tarihi, su 87,000 ne duka.6. ’Ya’ya uku maza na Benyamin su ne, Bela, Beker da Yediyayel.7. ’Ya’yan Bela maza su ne, Ezbon, Uzzi, Uzziyel, Yerimot da Iri, su ne kawunan iyalai, kuma su biyar ne duka. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna mazan da sun isa yaƙi 22,034.8. ’Ya’yan Beker maza su ne, Zemira, Yowash, Eliyezer, Eliyohenai, Omri, Yeremot, Abiya, Anatot da Alemet. Dukan waɗannan ’ya’yan Beker maza ne.9. Rubutaccen tarihin zuriyarsu ya nuna suna da kawunan iyalai da mazan da suka isa yaƙi 20,200.10. Ɗan Yediyayel shi ne, Bilhan. ’Ya’yan Bilhan maza su ne, Yewush, Benyamin, Ehud, Kena’ana, Zetan, Tarshish da Ahishahar.11. Dukan waɗannan ’ya’yan Yediyayel maza kawunan iyalai ne. Akwai mazan da suka isa yaƙi waje 17,200.12. Shuffiyawa da Huffiyawa zuriyar Ir ne, kuma Hushiyawa zuriyar Aher ne.13. ’Ya’yan Naftali maza su ne, Yaziyel, Guni, Yezer da Shallum, su zuriyar Bilha ne.14. Zuriyar Manasse su ne, Asriyel zuriyarsa ne ta wurin ƙwarƙwararsa mutuniyar Aram. Ta haifa wa Makir mahaifin Gileyad.15. Makir ya auri mata daga cikin Huffiyawa da Shuffiyawa. ’Yar’uwarsa ita ce Ma’aka. Wani daga zuriyar, sunansa Zelofehad, shi yana da ’ya’yan mata ne kawai.16. Ma’aka matar Makir ta haifi ɗa ta kuma ba shi suna Feresh. Sunan ɗan’uwansa Sheresh, ’ya’yan Feresh maza kuwa su ne Ulam da Rakem.17. Ɗan Ulam shi ne, Bedan. Duka waɗannan zuriyar Gileyad ne. Gileyad ɗan Makir ne, Makir kuma ɗan Manasse.18. ’Yar’uwarsa Makir mai suna Hammoleket ta haifi Ishod, Abiyezer da Mala.19. ’Ya’yan Shemida maza su ne, Ahiyan, Shekem, Liki da Aniyam.20. Zuriyar Efraim su ne, Shutela, Bered, Tahat, Eleyada, Tahat21. Zabad da Shutela. Wani ɗan ƙasa haifaffen mutanen Gat ya kashe Ezer da Elad, sa’ad da suka gangara don su ƙwace dabbobinsu.22. Mahaifinsu Efraim ya yi makoki dominsu kwanaki masu yawa sai danginsa suka zo don su yi masa ta’aziyya.23. Sa’an nan ya sāke kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi ɗa. Ya ba shi suna Beriya, saboda masifar da ta auko a cikin iyalinsa.24. ’Yarsa ita ce Sheyera, wadda ta gina Bet-Horon na kwari da na tudu da kuma Uzzen-Sheyera. Zuriyarsa ita ce,25. Refa, Reshef, Tela, Tahan,26. Ladan, Ammihud, Elishama,27. Nun da kuma Yoshuwa.28. Ƙasarsu da wuraren zamansu sun haɗa da Betel da ƙauyukan kewayenta, Na’aran wajen gabas, Gezer da ƙauyukanta wajen yamma, da kuma Shekem da ƙauyukan da suka nausa har zuwa Aiya da ƙauyukanta.29. A iyakokin Manasse akwai Bet-Sheyan, Ta’anak, Megiddo da Dor, tare da ƙauyukansu. Zuriyar Yusuf ɗan Isra’ila ta zauna a waɗannan garuruwa.30. ’Ya’yan Asher maza su ne, Imna, Ishba, Ishwi da Beriya. ’Yar’uwarsa ita ce Sera.31. ’Ya’yan Beriya maza su ne, Heber da Malkiyel, wanda yake mahaifin Birzayit.32. Heber shi ne mahaifin Yaflet, Shomer da Hotam da kuma ’yar’uwarsu Shuwa.33. ’Ya’yan Yaflet maza su ne, Fasak, Bimhal da Ashwat. Waɗannan su ne ’ya’yan Yaflet maza.34. ’Ya’yan Shemer maza su ne, Ahi, Roga, Yehubba da Aram.35. ’Ya’yan ɗan’uwansa Helem su ne, Zofa, Imna, Shelesh da Amal.36. ’Ya’yan Zofa maza su ne, Suwa, Harnefer, Shuwal, Beri, Imra,37. Bezer, Hod, Shamma, Shilsha, Itran da Bera.38. ’Ya’yan Yeter maza su ne, Yefunne, Fisfa da Ara.39. ’Ya’yan Ulla maza su ne, Ara, Hanniyel da Riziya.40. Dukan waɗannan zuriyar Asher ne, kawunan iyalai, zaɓaɓɓun mutane, jarumawa sosai da kuma fitattun shugabanni. Yawan mutanen da suke a shirye don yaƙi, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, 26,000 ne.1 Tarihi 8:1-401. Benyamin shi ne mahaifin, Bela ɗansa na fari, Ashbel ɗansa na biyu, Ahara na uku,2. Noha na huɗu da Rafa na biyar.3. ’Ya’yan Bela maza su ne, Addar, Gera, Abihud4. Abishuwa, Na’aman, Ahowa,5. Gera, Shefufan da Huram.6. Waɗannan su ne zuriyar Ehud, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Geba waɗanda aka kuma kwasa zuwa Manahat.7. Na’aman, da Ahiya, da Gera. Gera ne shugabansu lokacin da aka kai su bauta, shi ne ya haifi Uzza da Ahilud.8. An haifa ’ya’ya maza wa Shaharayim a Mowab bayan ya saki matansa Hushim da Ba’ara.9. Ya haifi Yobab, Zibiya, Hodesh, Malkam,10. Yewuz, Sakiya da Mirma ta wurin Hodesh matarsa. Waɗannan su ne ’ya’yansa, kawunan iyalai.11. Ya haifi Abitub da Efa’al ta wurin Hushim.12. ’Ya’yan Efa’al maza su ne, Eber, Misham, Shemed (wanda ya gina Ono da Lod tare da ƙauyukan kewayensu),13. da Beriya da Shema, waɗanda suke kawunan iyalan waɗanda suke zama a Aiyalon waɗanda kuma suka kori mazaunan Gat.14. Ahiyo, Shashak, Yeremot15. Zebadiya, Arad, Eder,16. Mika’ilu, Isfa da Yoha su ne ’ya’yan Beriya maza.17. Zebadiya, Meshullam, Hizki, Heber,18. Ishmerai, Izliya da Yobab su ne ’ya’yan Efa’al maza.19. Yakim, Zikri, Zabdi,20. Eliyenai, Zilletai, Eliyel,21. Adahiya, Berahiya da Shimra su ne ’ya’yan Shimeyi maza.22. Ishfan, Eber, Eliyel,23. Abdon, Zikri, Hanan,24. Hananiya, Elam, Antotiya,25. Ifdehiya da Fenuwel su ne ’ya’yan Shashak maza.26. Shamsherai, Shehariya, Ataliya,27. Ya’areshiya, Iliya da Zikri su ne ’ya’yan Yeroham maza.28. Dukan waɗannan su ne kawunan iyalai, manya kamar yadda aka lissafta a cikin zuriyarsu, suka zauna a Urushalima.29. Yehiyel na Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Sunan matarsa Ma’aka,30. ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,31. Gedor, Ahiyo, Zeker32. da Miklot, wanda ya zama mahaifin Shimeya. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.33. Ner shi ne mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.34. Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda ya zama mahaifin Mika.35. ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tereya da Ahaz.36. Ahaz shi ne mahaifin Yehowadda, Yehowadda shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.37. Moza shi ne mahaifin Bineya; Rafa, Eleyasa da kuma Azel.38. Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Dukan waɗannan ’ya’yan Azel maza ne.39. ’Ya’yan ɗan’uwansa Eshek su ne, Ulam ɗan farinsa, Yewush ɗansa na biyu da Elifelet na uku.40. ’Ya’yan Ulam maza jarumawa ne sosai waɗanda suke iya riƙe baka. Suna da ’ya’ya maza masu yawa da jikoki, 150 gaba ɗaya. Dukan waɗannan zuriyar Benyamin ne.Zabura 77:4-94. ka hana idanuna rufewa; na damu ƙwarai har ba na iya magana.5. Na yi tunani kwanakin da suka wuce, shekarun da suka wuce da daɗewa;6. na tuna da waƙoƙina da dare. Zuciyata ta yi nishi, ƙarfina kuwa ya nemi yă sani.7. “Ubangiji zai ƙi ne har abada? Ba zai taɓa nuna alherinsa kuma ba?8. Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?9. Allah ya manta yă yi jinƙai? Cikin fushinsa ya janye tausayinsa ne?”Karin Magana 19:13-1413. Wawan yaro lalacin mahaifinsa ne, mace mai yawan faɗa tana kama da ɗiɗɗigar ruwa.14. Ana gādon dawakai da wadata daga iyaye ne, amma mace mai basira daga Ubangiji ne.Ayyukan Manzanni 5:22-4222. Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce,23. “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.”24. Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.25. Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.”26. Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu.27. Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su.28. Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.”29. Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!30. Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace.31. Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.32. Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”33. Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su.34. Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci.35. Sa’an nan ya yi musu jawabi ya ce, “Mutanen Isra’ila, ku yi kula da kyau da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.36. Kwanan baya, Teyudas ya ɓullo, yana cewa wai shi wani mutum ne, kuma wajen mutane ɗari huɗu suka bi shi. Aka kuwa kashe shi, dukan masu binsa kuwa suka watse, kome ya wargaje.37. Bayansa, Yahuda mutumin Galili ya ɓullo a kwanakin ƙidaya, ya jagoranci mutane cikin tawaye. Shi ma aka kashe shi, dukan mabiyansa kuma aka watsar da su.38. Saboda haka, a wannan batu na yanzu, ina ba ku shawara. Ku ƙyale mutanen nan! Ku bar su su tafi! Gama in manufarsu ko ayyukansu na mutum ne, ai, zai rushe.39. Amma in daga Allah ne, ba za ku iya hana waɗannan mutane ba, za ku dai sami kanku kuna gāba da Allah ne.”40. Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi.41. Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.42. Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.