16. Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun; da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa.
17. Matsaran ƙofofi su ne, Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da ’yan’uwansu. Shallum ne babbansu
18. da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.
19. Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.
20. A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.
21. Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
22. Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu. Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci.
23. Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti.
24. Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu.
25. ’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai.
26. Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah.
27. Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya.
28. Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su.
29. An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji.
30. Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin.
31. Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa.
32. Waɗansu ’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci.
33. Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana.
34. Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima.
35. Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon. Matarsa ita ce Ma’aka
36. ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab,
37. Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot.
38. Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
39. Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.
40. Ɗan Yonatan shi ne, Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika.
41. ’Ya’yan Mika maza su ne, Fiton, Melek, Tareya da Ahaz.
42. Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza.
43. Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel.
44. Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu. Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne ’ya’yan Azel maza.
1. To, fa, Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra’ilawa; Isra’ilawa kuwa suka gudu a gabansu, da yawa kuma suka mutu a kan Dutsen Gilbowa.
2. Filistiyawa suka matsa sosai suna bin Shawulu da ’ya’yansa maza, suka kuma kashe ’ya’yansa maza Yonatan, Abinadab da Malki-Shuwa.
3. Yaƙin ya yi tsanani kewaye da Shawulu, kuma sa’ad da maharba suka rutsa shi, sai suka ji masa rauni.
4. Sai Shawulu ya ce wa mai riƙe masa kayan yaƙi, “Zare takobinka ka soke ni, in ba haka ba waɗannan marasa kaciya za su zo su yi mini ba’a.” Amma mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ji tsoro bai kuwa yi haka ba; saboda haka Shawulu ya zāre takobinsa ya fāɗi a kansa.
5. Da mai ɗaukar masa kayan yaƙi ya ga Shawulu ya mutu, sai shi ma ya fāɗi a kan takobinsa ya mutu.
6. Ta haka Shawulu da ’ya’yansa maza uku suka mutu, dukan gidansa kuwa suka mutu tare.
7. Sa’ad da dukan Isra’ilawa a cikin kwari suka ga cewa mayaƙansu suna gudu, kuma cewa Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu, sai suka bar garuruwansu suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.
8. Kashegari, da Filistiyawa suka zo don su tuttuɓe waɗanda suka mutu, sai suka sami Shawulu da ’ya’yansa maza sun mutu a Dutsen Gilbowa.
9. Suka tuttuɓe shi suka yanke kansa suka ɗauka duk da kayan yaƙinsa, suka kuma aika ’yan aika ko’ina a ƙasar Filistiyawa, a yi shela labarin a cikin gumakansu da kuma mutanensu.
10. Suka sa kayan yaƙinsa a haikalin allahnsu suka kuma rataye kansa a haikalin Dagon.
11. Sa’ad da mazaunan Yabesh Gileyad suka ji dukan abin da Filistiyawa suka yi wa Shawulu,
12. sai dukan jarumawa suka tafi suka ɗauki jikunan Shawulu da na ’ya’yansa maza suka kawo Yabesh. Sa’an nan suka binne ƙasusuwan a ƙarƙashin babban itace oak a Yabesh, suka kuma yi azumi kwana bakwai.
13. Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba,
14. bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.
10. Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”
11. Zan tuna da ayyukan Ubangiji; I, zan tuna mu’ujizanka na tun dā.
12. Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.
13. Hanyoyinka, ya Allah, masu tsarki ne. Wanda allah ne yake da girma kamar Allahnmu?
14. Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai; ka nuna ikonka a cikin mutane.
15. Da hannunka mai ƙarfi ka fanshi mutanenka, zuriyar Yaƙub da Yusuf.
15. Ragwanci kan jawo zurfin barci, mutum mai sanyin jiki kuma yana tare da yunwa.
16. Duk wanda ya bi umarnai kan tsare ransa, amma duk wanda ya ƙi binsu zai mutu.
1. A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.
2. Saboda haka Sha Biyun nan suka tara dukan almajirai wuri ɗaya, suka ce, “Bai zai yi kyau mu bar hidimar maganar Allah don mu shiga hidimar abinci ba.
3. ’Yan’uwa, ku zaɓi mutum bakwai daga cikinku waɗanda aka sani suna cike da Ruhu da kuma hikima. Mu kuwa za mu danƙa musu wannan aiki
4. mu kuwa mu mai da halinmu ga yin addu’a da kuma hidimar maganar Allah.”
5. Wannan shawarar kuwa ta gamshi dukan ƙungiyar. Sai suka zaɓi Istifanus, mutumin da yake cike da bangaskiya da kuma Ruhu Mai Tsarki; da Filibus, Burokorus, Nikano, Timon, Farmenas, da Nikolas daga Antiyok, wanda ya tuba zuwa Yahudanci.
6. Suka gabatar da waɗannan mutane wa manzanni, waɗanda kuwa suka yi addu’a, suka ɗibiya hannuwansu a kansu.
7. Saboda haka maganar Allah ta yaɗu. Yawan almajirai a Urushalima kuwa ya yi saurin ƙaruwa, firistoci masu yawa kuma suka zama masu biyayya ga wannan bangaskiya.
8. To, Istifanus, mutum cike da alheri da ikon Allah, ya aikata manyan ayyukan da alamu masu banmamaki a cikin mutane.
9. Sai hamayya ta taso daga ’yan ƙungiyar Majami’a na ’Yantattu (kamar yadda ake kiransu), Yahudawan Sairin da Alekzandariya da kuma lardunan Silisiya da Asiya. Mutanen nan suka fara muhawwara da Istifanus,
10. amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.
11. Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”
12. Ta haka suka tā da hankalin mutane da dattawa da kuma malaman dokoki. Suka kama Istifanus suka kawo shi a gaban Majalisa.
13. Suka kawo masu ba da shaidar ƙarya, waɗanda suka ba da shaida cewa, “Wannan mutum ba ya rabuwa da maganar banza a kan wurin nan mai tsarki da kuma doka.
14. Gama mun ji shi yana cewa wannan Yesu Banazare zai rushe wurin nan ya kuma canja al’adun da Musa ya ba mu.”
15. Dukan waɗanda suke zaune a Majalisar suka kafa wa Istifanus ido, suka kuma ga fuskarsa ta yi kama da ta mala’ika.