Baibul a cikin shekara guda Yuni 261 Tarihi 15:1-291. Bayan Dawuda ya yi gine-gine wa kansa a Birnin Dawuda, sai ya shirya wuri domin akwatin alkawarin Allah, ya kuma kafa tenti dominsa.2. Sa’an nan Dawuda ya ce, “Babu wani sai ko Lawiyawa kaɗai za su ɗauka akwatin alkawarin Allah, gama Ubangiji ya zaɓe su su ɗauka akwatin alkawarin Ubangiji su kuma yi hidima a gabansa har abada.”3. Dawuda ya tattara dukan Isra’ila a Urushalima don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurin da aka shirya dominsa.4. Ya tattara zuriyar Haruna a wuri ɗaya da kuma Lawiyawa.5. Daga zuriyar Kohat, Uriyel shugaba da dangi 120;6. daga zuriyar Merari Asahiya shugaba da dangi 220;7. daga zuriyar Gershom, Yowel shugaba da dangi 130;8. daga zuriyar Elizafan, Shemahiya shugaba da dangi 200;9. daga zuriyar Hebron, Eliyel shugaba da dangi 80;10. daga zuriyar Uzziyel, Amminadab shugaba da dangi 112.11. Sa’an nan Dawuda ya kira Zadok da Abiyatar, firistoci, tare da Uriyel, Asahiya, Yowel, Shemahiya, Eliyel da Amminadab, Lawiyawa.12. Ya ce musu, “Ku ne kawunan iyalan Lawiyawa; ku da ’yan’uwanku Lawiyawa, sai ku tsarkake kanku ku hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila, zuwa wurin da na shirya dominsa.13. Domin ku, Lawiyawa ba ku haura da shi da farko ba ne ya sa Ubangiji Allahnmu ya husata a kanmu. Ba mu tambaye shi game da yadda za mu yi shi a hanyar da aka ƙayyade ba.”14. Saboda haka firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu don su hauro da akwatin alkawarin Ubangiji, Allah na Isra’ila.15. Sai Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah da sanduna a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.16. Dawuda ya faɗa wa shugabannin Lawiyawa su sa ’yan’uwansu su zama mawaƙa don su rera waƙoƙi masu farin ciki, da kayayyakin bushe-bushe, da kaɗe-kaɗe, molaye, garayu da ganguna.17. Saboda haka Lawiyawa suka zaɓi Heman ɗan Yowel, da Asaf ɗan Berekiya daga cikin ’yan’uwansu. Daga iyalin Merari kuma aka zaɓi Etan ɗan Kushahiya.18. Tare da su kuma ’yan’uwansa da suke biye bisa ga matsayi. Wato, Zakariya, Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ben, Ma’asehiya, Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom da Yehiyel, matsaran ƙofofi.19. Mawaƙan nan Heman, Asaf da Etan, ne za su buga kugen tagulla.20. Zakariya, Aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Unni, Eliyab, Ma’asehiya da Benahiya, ne za su kaɗa molaye masu murya sama-sama, bisa ga alamot.21. Mattitiya, Elifelehu, Miknehiya, Obed-Edom, Yehiyel da Azaziya, ne za su ja garayu masu murya ƙasa-ƙasa bisa ga sheminit.22. Kenaniya, shugaban Lawiyawa, shi ne mai bi da waƙoƙi. Wannan hakkinsa ne, gama shi gwani ne a wannan fanni.23. Berekiya da Elkana, ne za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.24. Shebaniya, Yoshafat, Netanel, Amasai, Zakariya, Benahiya da Eliyezer firistoci, su ne za su busa ƙahoni a gaban akwatin alkawarin Allah. Obed-Edom da Yehiya su ma za su zama masu lura da ƙofofi domin akwatin alkawarin.25. Sai Dawuda da dattawan Isra’ila da shugabannin ƙungiyoyi dubu suka haura don su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-Edom, da farin ciki.26. Domin Allah ya taimaki Lawiyawan da suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, aka miƙa hadayar bijimai bakwai da raguna bakwai.27. To, fa, Dawuda yana saye da kyakkyawar rigar lilin, kamar yadda dukan Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin suka sa, da kuma yadda mawaƙa, da Kenaniya, wanda yake bi da waƙar mawaƙan ya sa. Dawuda kuma ya sa efod lilin.28. Sai dukan Isra’ila suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji da sowa, da ƙarar ƙahonin raguna da busan ƙahoni, da na ganguna, suna kuma kaɗa molaye da garayu.29. Yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yake shiga Birnin Dawuda, Mikal ’yar Shawulu ta leƙa daga taga. Sa’ad da ta ga Sarki Dawuda yana rawa yana shagali, sai ta rena masa wayo a zuciyarta.1 Tarihi 16:1-431. Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.2. Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.3. Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.4. Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.5. Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,6. Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.7. A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.8. Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.9. Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan ayyukan banmamakinsa.10. Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.11. Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.12. Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,13. Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.14. Shi ne Ubangiji Allahnmu; hukuntansa suna a cikin dukan duniya.15. Yakan tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,16. alkawarin da ya yi wa Ibrahim rantsuwar da ya yi ga Ishaku.17. Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida, ga Isra’ila kamar madawwamin alkawari.18. “Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana kamar rabon da za ka gāda.”19. Sa’ad da suke kima, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,20. suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga wannan mulki zuwa wancan.21. Bai bar wani ya zalunce su ba; saboda su ya tsawata wa sarakuna.22. “Kada ku taɓa shafaffuna; kada ku yi wa annabawana lahani.”23. Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana.24. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.25. Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo; dole a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.26. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ya yi sammai.27. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da farin ciki suna a wurin zamansa.28. Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai, ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,29. ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa. Ku kawo hadaya ku kuma zo gabansa; ku yi wa Ubangiji sujada cikin darajar tsarkinsa.30. Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka! Duniya ta kahu sosai; ba za tă jijjigu ba.31. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari su ce a cikin al’ummai, “ Ubangiji yana mulki!”32. Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri; bari gonaki da kome a cikinsu su yi farin ciki!33. Sa’an nan itatuwan jeji za su rera, za su rera don farin ciki a gaban Ubangiji, gama ya zo don yă hukunta duniya.34. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.35. Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu; tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai, don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki, don mu ɗaukaka a cikin yabonka.”36. Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Sai dukan mutane suka ce, “Amin.” Suka kuma “Yabi Ubangiji.”37. Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.38. Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.39. Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon40. don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.41. Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”42. Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.43. Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.Zabura 78:12-1612. Ya yi mu’ujizai a idanun kakanninsu a ƙasar Masar, a yankin Zowan.13. Ya raba teku ya kuma bi da su ciki; ya sa ruwa ya tsaya daram kamar bango.14. Ya bishe su da girgije da rana da kuma haske daga wuta dukan dare.15. Ya tsage duwatsu a cikin hamada ya kuma ba su ruwaye a yalwace kamar tekuna;16. ya fid da rafuffuka daga dutsen da ya tsaga ya sa ruwa ya gudu kamar koguna.Karin Magana 19:22-2422. Abin da mutum yake sha’awa shi ne ƙauna marar ƙarewa; gara ka zama matalauci da ka zama maƙaryaci.23. Tsoron Ubangiji yakan kai ga rai. Sa’an nan mutum ya sami biyan bukata, ba abin da zai cuce shi.24. Rago kan sa hannunsa a kwano ba ya ma iya ɗaga shi ya kai bakinsa!Ayyukan Manzanni 7:44-6044. “Kakanni-kakanninmu suna da tabanakul na Shaida tare da su a hamada. An yi shi bisa ga yadda Allah ya umarci Musa, bisa ga zānen da ya gani.45. Bayan sun gāji tabanakul nan, kakanninmu a ƙarƙashin jagorancin Yoshuwa suka kawo shi tare da su, lokacin da suka ƙwace ƙasar daga al’umman da Allah ya kora a idanunsu. Tabanakul ɗin ya kasance a ƙasar har zamanin Dawuda,46. wanda ya sami tagomashi daga Allah, ya kuma nemi yă yi wa Allah na Yaƙub wurin zama.47. Amma Solomon ne ya gina masa gida.48. “Duk da haka, Mafi Ɗaukaka ba ya zama a gidajen da mutane suka gina. Kamar yadda annabi ya faɗi cewa,49. “ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.50. Ba hannuna ne ya yi dukan waɗannan abubuwa ba?’51. “Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!52. An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi53. ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.”54. Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu.55. Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah.56. Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”57. Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya.58. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu.59. Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.”60. Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.