Baibul a cikin shekara guda Yuni 271 Tarihi 17:1-271. Bayan Dawuda ya zauna a fadansa, sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar da aka yi da al’ul, yayinda akwatin alkawarin Ubangiji yana a ƙarƙashin tenti.”2. Natan ya amsa wa Dawuda ya ce, “Duk abin da kake tunani a zuciya, ka yi, gama Allah yana tare da kai.”3. A daren nan maganar Allah ta zo wa Natan cewa,4. “Ka tafi ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji ya ce ba kai ba ne za ka gida mini gidan da zan zauna a ciki.5. Ban taɓa zama a gida daga ranar da na fito da Isra’ila daga Masar ba har wa yau. Na yi ta yawo daga gefen da aka kafa tenti zuwa wani, daga wannan wuri zuwa wancan.6. Duk inda na tafi tare da Isra’ilawa, na taɓa ce wa wani daga cikin shugabanninsu waɗanda na umarta su yi kiwon mutanena, “Don me ba ku gida mini gidan al’ul ba?” ’7. “Yanzu, ka faɗa wa bawana Dawuda, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauke ka daga makiyaya da kuma daga bin garke, don ka zama mai mulki a bisa mutanena Isra’ila.8. Na kasance tare da kai ko’ina ka tafi, na kuma yanke dukan abokan gābanka a gabanka. Yanzu zan sa sunanka kamar sunayen mutane mafi girma na duniya.9. Zan kuma tanada wuri domin mutanena Isra’ila, zan kuma kafa su saboda za su kasance da gidan kansu ba kuwa za a ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara zaluntar su ba, yadda suka yi da farko10. da kuma suka yi tun lokacin da na sa shugabanni a bisa mutanen Isra’ila. Zan rinjaye dukan abokan gābanka. “ ‘Na furta maka cewa Ubangiji zai gina maka gida,11. sa’ad da kwanakinka suka ƙare ka kuma tafi don ka kasance da kakanninka, zan tā da ɗaya cikin ’ya’yanka maza, daga zuriyarka yă gāje ka, zan kuma kafa mulkinka.12. Shi ne zai gina gida domina, zan kuma kafa sarautarsa har abada.13. Zan zama Ubansa, zai kuma zama ɗana. Ba zan taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi, kamar yadda na ɗauke ta daga wanda ya riga ka ba.14. Zan sa shi a bisa gidana da mulkina har abada; kujerar sarautarsa za tă kahu har abada.’ ”15. Natan ya faɗa wa Dawuda dukan kalmomin wahayin nan.16. Sai Sarki Dawuda ya shiga ya zauna a gaban Ubangiji ya ce, “Wane ne ni, ya Ubangiji Allah, kuma wane ne iyalina, da ka kawo ni har zuwa nan?17. Kuma sai ka ce wannan bai isa ba a idonka, ya Allah, ka yi magana game da nan gaba na gidan bawanka. Ka dube ni sai ka ce ni ne mafi ɗaukaka cikin mutane, ya Ubangiji Allah.18. “Me kuma Dawuda zai ce maka saboda girmamawar da ka yi wa bawanka? Gama ka san bawanka,19. Ya Ubangiji. Gama saboda bawanka da kuma bisa ga nufinka, ka yi wannan babban abu, ka kuma sanar da dukan manyan alkawura.20. “Babu wani kamar ka, ya Ubangiji, babu kuma Allah sai kai, kamar yadda muka ji da kunnuwanmu.21. Wane ne kuma yake kamar mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allahnta ya fita don yă fanshi mutane wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa masu banmamaki masu banrazana ta wurin korin al’ummai daga gaban mutanenka, waɗanda ka fansa daga Masar?22. Ka mai da mutanenka Isra’ila na kanka har abada, kuma kai, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.23. “Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari,24. saboda zai kahu kuma sunanka zai zama mai girma har abada. Sa’an nan mutane za su ce, ‘ Ubangiji Maɗaukaki, Allah a bisa Isra’ila, Allahn Isra’ila ne!’ Kuma gidan bawanka Dawuda zai kahu a gabanka.25. “Kai, Allahna, ka bayyana ga bawanka cewa za ka gina gida dominsa. Ta haka bawanka ya sami ƙarfin gwiwa ya yi addu’a gare ka.26. Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka.27. Yanzu ka ji daɗi don ka albarkace gidan bawanka, don yă ci gaba har abada a gabanka; gama kai, ya Ubangiji, ka albarkace shi, ya kuma sami albarka ke nan har abada.”1 Tarihi 18:1-171. Ana nan sai Dawuda ya ci Filistiyawa ya kuma rinjaye su, ya ƙwace Gat da ƙauyukan kewayenta daga mulkin Filistiyawa.2. Dawuda ya kuma ci Mowabawa, suka zama bayinsa suka kuma biya haraji.3. Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer sarkin Zoba, har can Hamat, sa’ad da ya je don yă kafa mulkinsa a wajen Kogin Yuferites.4. Dawuda ya kame keken yaƙinsa dubu ɗaya, da mahayan kekunan yaƙi dubu bakwai da sojojin kafa guda dubu ashirin. Ya yayyanke dukan agaran dawakansa, amma ya bar dawakai da suka isa jan kekunan yaƙi ɗari.5. Da Arameyawan Damaskus suka zo su taimaki Hadadezer sarkin Zoba, sai Dawuda ya bugi dubu ashirin da biyunsu.6. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus. Arameyawan kuwa suka zama bayinsa, suka kuma kawo haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.7. Dawuda ya kwashe garkuwoyin zinariyan da shugabannin sojojin Hadadezer suke riƙe, ya kawo su Urushalima.8. Daga Teba da Kun, garuruwan da suke ƙarƙashin Hadadezer, Dawuda ya kwashe tagulla da yawa sosai, wanda Solomon ya yi amfani don yă yi Tekun tagulla, ginshiƙai da kuma kayayyakin tagulla dabam-dabam.9. Sa’ad da Towu sarkin Hamat ya ji cewa Dawuda ya ci mayaƙan Hadadezer sarkin Zoba gaba ɗaya,10. sai ya aiki ɗansa Hadoram zuwa wurin Sarki Dawuda yă gaishe shi yă kuma yi masa barka da nasara a yaƙi a kan Hadadezer, wanda yake yaƙi da Towu. Hadoram ya kawo kowane irin kayayyakin zinariya da na azurfa da na tagulla.11. Sarki Dawuda ya miƙa waɗannan kayayyakin ga Ubangiji, kamar yadda ya yi da azurfa da kuma zinariyan da ya kwaso daga dukan waɗannan al’ummai. Edom da Mowab, Ammonawa da Filistiyawa, da kuma Amalek.12. Abishai ɗan Zeruhiya ya bugi mutanen Edom dubu goma sha takwas a Kwarin Gishiri.13. Ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan mutanen Edom kuwa suka zama bayin Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a ko’ina da ya tafi.14. Dawuda ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila, yana yin abin da yake daidai da kuma gaskiya saboda dukan mutanensa.15. Yowab ɗan Zeruhiya shi ne shugaban mayaƙa; Yehoshafat ɗan Ahilud shi ne marubuci;16. Zadok ɗan Ahitub da Abimelek ɗan Abiyatar su ne firistoci; Shafsha shi ne magatakarda;17. Benahiya ɗan Yehohiyada shi ne shugaban Keretawa da Feletiyawa; ’ya’yan Dawuda maza su ne manyan ma’aikata a gefen sarki.Zabura 78:17-2517. Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.18. Da gangan suka gwada Allah ta wurin neman abincin da suke kwaɗayi.19. Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?20. Sa’ad da ya bugi dutse, ruwa ya ɓulɓulo, rafuffuka suka yi gudu a yalwace. Amma zai iya ba mu abinci? Zai iya tanada wa mutanensa nama?”21. Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,22. gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.23. Duk da haka ya ba da umarni ga sarari a bisa ya kuma buɗe ƙofofin sammai;24. ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.25. Mutane suka ci burodin mala’iku; ya aika musu dukan abincin da za su iya ci.Karin Magana 19:25-2625. Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani.26. Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.Ayyukan Manzanni 8:1-251. Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. A wannan rana wani babban tsanani ya auka wa ikkilisiyar da take a Urushalima, sai duka suka warwatsu ko’ina a Yahudiya da Samariya, manzanni kaɗai ne suka rage.2. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa.3. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.4. Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi.5. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.6. Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa.7. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.8. Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.9. To, akwai wani mutum mai suna Siman wanda ya kwana biyu yana yin sihiri a birnin har ya ba wa duk mutanen Samariya mamaki. Ya kuma yi taƙama cewa shi wani mai girma ne,10. dukan mutane kuwa, manyan da ƙanana, suka mai da hankali gare shi suka kuma ce, “Mutumin nan shi ne ikon Allah da aka sani a matsayin Iko Mai Girma”11. Suka bi shi domin ya daɗe yana ba su mamaki da sihirinsa.12. Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.13. Siman kansa ya gaskata aka kuma yi masa baftisma. Ya kuma bi Filibus ko’ina, yana mamakin manyan alamu da ayyukan banmamakin da ya gani.14. Sa’ad da manzannin da suke a Urushalima suka ji cewa Samariya ta karɓi maganar Allah, sai suka aika musu da Bitrus da Yohanna.15. Da suka iso, sai suka yi musu addu’a domin su karɓi Ruhu Mai Tsarki,16. domin Ruhu Mai Tsarki bai riga ya sauka wa waninsu ba tukuna, an dai yi musu baftisma ne kawai a cikin sunan Ubangiji Yesu.17. Sa’an nan Bitrus da Yohanna suka ɗibiya hannuwansu a kansu, suka kuwa karɓi Ruhu Mai Tsarki.18. Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi,19. ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.”20. Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!21. Ba ruwanka da wannan hidimar, domin zuciyarka ba daidai take a gaban Allah ba.22. Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.23. Gama na lura kana cike da ɗacin rai kana kuma daure cikin zunubi.”24. Sai Siman ya amsa ya ce, “Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda ni don kada ko ɗaya daga cikin abin da ka faɗa ya same ni.”25. Sa’ad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna wa’azin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.