Baibul a cikin shekara guda Yuni 281 Tarihi 19:1-191. Ana nan, sai Nahash sarkin Ammonawa ya mutu, sai ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.2. Dawuda ya yi tunani, “Zan nuna jinƙai ga Hanun ɗan Nahash, domin mahaifinsa ya nuna alheri gare ni.” Saboda haka Dawuda ya aika da tawaga don yă yi wa Hanun ta’aziyya game da mahaifinsa. Sa’ad da mutanen Dawuda suka iso wurin Hanun a ƙasar Ammonawa don su ta’azantar da shi,3. sai manyan Ammonawa suka ce wa Hanun, “Kana tsammani Dawuda yana girmama mahaifinka ne da ya aika mutanen nan wurinka su ta’azantar da kai? Ba mutanensa sun zo ne su bincika su kuma leƙi ƙasar su tumɓuke ta ba?”4. Saboda haka Hanun ya kama mutanen Dawuda, ya yi musu aski, ya yayyanka rigunansu a daidai ɗuwawunsu, sa’an nan ya sallame su.5. Da wani ya zo ya faɗa wa Dawuda game da mutanen, sai ya aiki ’yan aika su sadu da su, gama an ƙasƙantar da su ainun. Sarki ya ce, “Ku zauna a Yeriko har sai gemunku sun yi girma, sa’an nan ku dawo.”6. Sa’ad da Ammonawa suka gane cewa sun zama abin wurin a kafan hancin Dawuda, Hanun da Ammonawa suka aika da talenti dubu na azurfa don su yi haya da kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi daga Aram-Naharayim, Aram Ma’aka da Zoba.7. Suka yi hayar kekunan yaƙi da mahayan kekunan yaƙi dubu talatin da biyu, da kuma sarkin Ma’aka tare da mayaƙansa, waɗanda suka zo suka kafa sansani kusa da Medeba, yayinda Ammonawa suka tattaru daga garuruwansu suka fita yaƙi.8. Da jin haka, Dawuda ya aiki Yowab tare da dukan mayaƙa masu yaƙi.9. Ammonawa suka fito suka ja dāgā a ƙofar birninsu, yayinda sarakunan da suka zo, su kansu suka ware suna a fili.10. Yowab ya ga cewa akwai dāgā a gabansa da bayansa; sai ya zaɓi waɗansu mayaƙa mafi kyau a Isra’ila ya sa su a kan Arameyawa.11. Ya sa sauran mutanen a ƙarƙashin kulawar Abishai ɗan’uwansa, aka sa a kan Ammonawa.12. Yowab ya ce, “In Arameyawa suka fi ni ƙarfi, sai ka kawo mini ɗauke da ni; amma in Ammonawa sun fi ka ƙarfi, sai in kawo maka ɗauke.13. Ka yi ƙarfin hali bari mu yi yaƙi da jaruntaka saboda mutanenmu da biranen Allahnmu. Ubangiji zai yi abin da ya ga ya yi masa kyau.”14. Sai Yowab da ƙungiyoyin mayaƙan da suke tare da shi suka matso don su yi yaƙi da Arameyawa, Arameyawan kuwa suka gudu a gabansa.15. Sa’ad da Ammonawa suka ga Arameyawa suna gudu, sai su ma suka guda a gaban ɗan’uwansa Abishai suka shiga cikin birni. Sai Yowab ya koma Urushalima.16. Bayan Arameyawa suka ga cewa Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka aiki ’yan aika suka sa aka kawo Arameyawan da suke hayen Kogi waɗanda Shobak shugaban mayaƙan Hadadezer yake shugabanta.17. Sa’ad da aka faɗa wa Dawuda wannan, sai tattara dukan Isra’ila ya haye Urdun; ya tafi wurinsu ya kuwa ja dāgā ɗaura da su. Dawuda ya ja dāgārsa don yă sadu da Arameyawa a yaƙi, su kuwa suka yi yaƙi da shi.18. Amma Arameyawa suka gudu a gaban Isra’ila, mutanen Dawuda kuwa suka kashe masu hawan keken yaƙinsu dubu bakwai da sojojin ƙasa dubu arba’in. Ya kuma kashe Shobak shugaban mayaƙansu.19. Da abokan tarayyar Hadadezer suka ga Isra’ila sun ci su da yaƙi, sai suka nemi salama da Dawuda suka kuma zama bayinsa. Saboda haka Arameyawa ba su ƙara yarda su taimaki Ammonawa ba.1 Tarihi 20:1-81. Da bazara, a lokacin da sarakuna kan tafi yaƙi, Yowab ya jagorance mayaƙa. Ya lalatar da ƙasar Ammonawa ya kuma tafi Rabba ya yi mata kwanto, amma Dawuda ya zauna a Urushalima. Yowab ya yaƙi Rabba, ya kuma bar ta kango.2. Dawuda ya ɗauki rawani daga kan sarkinsu, nauyinsa ya kai talenti na zinariya, aka kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, sai Dawuda kuwa ya sa a kansa. Ya kuma kwashi ganima mai yawa daga birnin3. ya kuma fitar da mutanen da suke can, ya sa su aiki da zartuna da makamai masu kaifi da kuma gatura. Dawuda ya yi haka da dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da mayaƙansa gaba ɗaya suka koma Urushalima.4. Ana nan, sai yaƙi ya ɓarke a Gezer tsakanin Isra’ila da Filistiyawa. Sai Sibbekai mutumin Husha ya kashe Siffai, ɗaya daga cikin zuriyar Refahiyawa, ta haka kuma aka ci Filistiyawa da yaƙi.5. Yaƙi kuma ya sāke tashi tsakanin Isra’ilawa da Filistiyawa, Elhanan ɗan Yayir ya kashe Lahmi ɗan’uwan Goliyat mutumin Gat, wanda yake riƙe da māshi mai sandan masaƙa.6. Aka sāke yin wani yaƙin kuma, wanda ya faru a Gat, akwai wani ƙaton mutum mai yatsotsi shida a kowane hannu da kuma yatsotsi shida a kowace ƙafa, yatsotsi ashirin da huɗu ke nan. Shi ma daga zuriyar Rafa ce.7. Sa’ad da ya yi wa Isra’ila ba’a, sai Yonatan ɗan Shimeya, ɗan’uwan Dawuda ya kashe shi.8. Waɗannan su ne zuriyar Rafa a Gat, Dawuda da mutanensa sun kashe su.Zabura 78:26-3326. Ya saki iskar gabas daga sammai ya kuma saki iskar yamma ta wurin ikonsa.27. Ya sauko da nama a kansu kamar ƙura, tsuntsaye masu firiya kamar yashi a bakin teku.28. Ya sa suka sauka a cikin sansaninsu, ko’ina kewaye da tentunansu.29. Suka ci har suka sami fiye da abin da ya ishe su, gama ya ba su abin da suka yi kwaɗayi.30. Amma kafin su juyo daga abincin da suka yi kwaɗayi, kai tun ma yana a bakunansu,31. fushin Allah ya ƙuna a kansu; ya karkashe waɗanda suka fi ƙiba a cikinsu, yana yankan matasan Isra’ila.32. Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.33. Saboda haka ya sa kwanakinsu suka ƙare a banza shekarunsu kuma cikin masifa.Karin Magana 19:27-2927. In ka daina jin umarni, ɗana, za ka kuwa kauce daga kalmomin sani.28. Mai shaidar da yake malalaci yana wa shari’a ba’a ne, bakin mugaye kuma na haɗiye mugunta.29. An shirya tara saboda masu ba’a ne, dūka kuma saboda bayan wawaye.Ayyukan Manzanni 8:26-4026. To wani mala’ikan Ubangiji ya ce wa Filibus, “Ka yi kudu zuwa hanyar, hanyar hamada, da ta gangara daga Urushalima zuwa Gaza.”27. Saboda haka ya kama hanya, a kan hanyarsa kuwa sai ya sadu da wani mutumin Itiyofiya, wanda yake bābā, hafsa mai muhimmanci wanda yake lura da dukan ma’ajin Kandas (wanda yake nufin “sarauniyar mutanen Itiyofiya”). Mutumin nan ya tafi Urushalima ne domin yin sujada,28. a kan hanyarsa ta komawa gida kuwa yana zaune bisan keken yaƙinsa yana karatun littafin annabin Ishaya.29. Sai Ruhu ya ce wa Filibus, “Matsa wurin kekunan yaƙin nan ka yi kusa da ita.”30. Sai Filibus ya ruga zuwa wajen keken yaƙin ya kuma ji mutumin yana karatun littafin annabin Ishaya. Filibus ya yi tambaya ya ce, “Ka fahimci abin da kake karantawa?”31. Sai ya ce, “Ina fa zan iya, in ba dai wani ya fassara mini ba?” Saboda haka sai ya gayyaci Filibus yă hau yă zauna tare da shi.32. Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.33. A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.”34. Sai bābān ya tambayi Filibus ya ce, “Ka gaya mini, ina roƙonka, annabin yana magana a kan wane ne, kansa ne, ko kuwa wani dabam?”35. Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu.36. Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?”37. Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.38. Sa’ad da suka fita daga cikin ruwan, sai Ruhun Ubangiji ya fyauce Filibus, bābān kuwa bai ƙara ganinsa ba, amma ya ci gaba da tafiyarsa yana farin ciki.39. Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.