Baibul a cikin shekara guda Yuni 41 Sarakuna 17:1-241. To, Iliya mutumin Tishbe, daga Tishbe a Gileyad, ya ce wa Ahab, “Muddin Ubangiji, Allah na Isra’ila wanda nake bauta wa yana a raye, ba za a yi raɓa ko ruwan sama a ’yan shekaru masu zuwa ba, sai ko na faɗa haka.”2. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce,3. “Ka bar nan, ka nufi wajajen gabas, ka ɓuya a Rafin Kerit, gabas da Urdun.4. Za ka sha daga rafin, zan kuma umarci hankaki su ciyar da kai a can.”5. Saboda haka sai Iliya ya yi abin da Ubangiji ya faɗa masa. Ya tafi Rafin Kerit, gabas da Urdun, ya zauna a can.6. Hankaki suka riƙa kawo masa abinci da nama, safe da yamma, ya kuma sha daga rafin.7. Ana nan sai rafin ya bushe saboda ba a yi ruwan sama a ƙasar ba.8. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya cewa,9. “Je ka, nan take, zuwa Zarefat na Sidon, ka zauna a can. Na umarci wata gwauruwa a can tă ciyar da kai.”10. Saboda haka sai ya tafi Zarefat. Sa’ad da ya isa ƙofar gari, sai ga wata gwauruwa tana tattara ’yan itace. Sai ya kira ta, ya ce, “Ki kawo mini ɗan ruwa a tulu don in sha.”11. Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.”12. Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.”13. Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini ’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki.14. Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’ ”15. Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta.16. Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya.17. Ana nan sai ɗan matan, wato, gwauruwan nan ya fara ciwo. Ciwon ya ƙara muni, daga ƙarshe sai ya daina numfashi.18. Sai ta ce wa Iliya, “Mutumin Allah, yaya haka? Ka zo ne domin ka nuna wa Allah zunubaina, ka kuma jawo mutuwar ɗana?”19. Iliya ya ce, “Ki miƙa mini ɗanki.” Sai ya ɗauke shi daga hannuwanta, ya kai shi ɗakin sama inda yake zama, ya kwantar da shi a gadonsa.20. Sa’an nan ya yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, don me ka kawo wannan masifa a kan gwauruwan nan? Kai ka ce in zauna tare da ita, ga shi yanzu ɗanta ya mutu.”21. Sai ya kwanta, ya miƙe kansa a kan yaron sau uku, ya kuma yi kuka ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allahna, ka mai da ran yaron nan!”22. Ubangiji kuwa ya ji kukan Iliya, sai ran yaron ya dawo masa, ya kuma rayu.23. Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga ɗakin sama zuwa cikin gida. Ya ba da shi ga mahaifiyarsa, ya ce, “Duba, ɗanki yana da rai!”24. Sai matar ta ce wa Iliya, “Yanzu na san cewa kai mutumin Allah ne, Ubangiji kuma yana magana ta wurinka.”1 Sarakuna 18:1-461. Bayan dogon lokaci, a cikin shekara ta uku, maganar Ubangiji ta zo wa Iliya, ta ce, “Tafi, ka gabatar da kanka ga Ahab, zan kuwa aika da ruwan sama a ƙasar.”2. Saboda haka Iliya ya tafi ya gabatar da kansa ga Ahab. Yanzu dai yunwa ta tsananta a Samariya,3. Ahab kuma ya aika a kawo Obadiya, sarkin fadansa (Obadiya dai cikakken mai gaskata da Ubangiji ne.4. Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.)5. Ahab ya ce wa Obadiya, “Ka ratsa ƙasar zuwa dukan maɓulɓulai da fadamu. Mai yiwuwa ka sami ciyawa mu ba dawakai da alfadarai don su rayu, don kada mu kashe dabbobinmu.”6. Saboda haka suka raba ƙasar da za su ratsa, Ahab zai tafi gefe ɗaya, Obadiya kuma yă bi gefe ɗaya.7. Yayinda Obadiya yana tafiya, sai Iliya ya sadu da shi. Obadiya ya gane shi, ya rusuna har ƙasa, ya ce, “Kai ne, shugabana, Iliya?”8. Iliya ya amsa, ya ce, “I, je ka faɗa wa maigidanka cewa, ‘Iliya yana a nan.’ ”9. Obadiya ya yi tambaya, “Me na yi da ba daidai ba, da kake miƙa bawanka ga Ahab don yă kashe?10. Na rantse da Ubangiji Allahnka, babu al’umma ko masarauta da mai girma sarki bai aika a nemo ka ba. In suka ce ba ka can, sai yă sa mulkin ko al’ummar su rantse, cewa ai, ba su same ka ba.11. Amma yanzu kana faɗa mini in tafi wurin mai girma in ce, ‘Iliya yana a nan.’12. Ban san inda Ruhun Ubangiji zai kai ka sa’ad da na bar ka ba. In na tafi na faɗa wa Ahab bai kuma same ka a nan ba, zai sa a kashe ni. Tuna fa, ni bawanka, na yi wa Ubangiji sujada tun ina saurayi.13. Ranka yă daɗe, ashe, ba a faɗa maka abin da na yi lokacin da Yezebel ta karkashe annabawan Ubangiji ba? Yadda na ɓoye annabawa ɗari, na sa su hamsin-hamsin a kogwanni biyu, na yi ta ba su abinci da ruwa.14. Yanzu fa, kana ce in tafi wurin mai girma sarki, in ce, ‘Iliya yana a nan.’ Ai, zai kashe ni!”15. Iliya ya ce, “Na rantse da Ubangiji Maɗaukaki, wanda nake bauta wa, tabbatacce zan gabatar da kaina ga Ahab a yau.”16. Saboda haka sai Obadiya ya tafi wurin Ahab ya faɗa masa, Ahab kuwa ya tafi wurin Iliya.17. Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?”18. Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al.19. Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”20. Sai Ahab ya aika a duk fāɗin Isra’ila, ya kuma tattara annabawan a kan Dutsen Karmel.21. Iliya ya je gaban mutane ya ce, “Har yaushe za ku yi ta yawo tsakanin ra’ayoyi biyu? In Ubangiji ne Allah, ku bi shi; amma in Ba’al Allah ne, ku bi shi.” Mutane dai ba su ce uffam ba.22. Sai Iliya ya ce musu, “Ni ne kaɗai annabin Ubangiji da ya rage, amma Ba’al yana da annabawa ɗari huɗu da hamsin.23. Ku samo mana bijimai biyu. Bari su zaɓa ɗaya wa kansu, bari kuma su yanka shi kucu-kucu su sa a itace, sai dai, kada su sa wuta a kansa. Ni kuwa zan shirya ɗaya bijimin in sa a kan itace, ni ma, ba zan sa wuta a kansa ba.24. Sa’an nan ku kira bisa sunan allahnku, ni kuwa zan kira bisa sunan Ubangiji. Duk allahn da ya amsa ta wurin wuta, shi ne Allah.” Sai dukan jama’a suka ce, “Abin nan da faɗa yana da kyau.”25. Iliya ya ce wa annabawan Ba’al, “Ku ku fara zaɓi bijimi ɗaya, ku shirya, da yake kuna da yawa. Ku kira a bisa sunan allahnku, amma kada ku ƙuna wuta.”26. Sai suka ɗauki bijimin da aka ba su suka shirya shi. Sa’an nan suka kira bisa sunan Ba’al daga safe har tsakar rana. Suna ihu, “Ya Ba’al, ka amsa mana!” Amma babu wata amsa, babu wani da ya amsa. Suka yi ta rawa kewaye da bagaden da suka yi.27. Da tsakar rana, Iliya ya fara yin musu ba’a. Ya ce, “Ku yi ihu da ƙarfi, tabbatacce shi allah ne! Mai yiwuwa yana cikin zurfin tunani, ko dai aiki ya yi masa yawa, ko ya yi tafiya. Mai yiwuwa yana barci ne, dole a tashe shi.”28. Sai suka yi ta ihu da ƙarfi suna tsattsaga kansu da takuba da māsu, yadda al’adarsu take, sai da jininsu ya yi ta zuba.29. Tsakar rana ta wuce, suka ci gaba da ƙoƙari, suna annabci har lokacin miƙa hadayar yamma ya yi. Amma babu wani da ya tanƙa, babu wani da ya amsa, babu wanda ya kula.30. Sa’an nan Iliya ya ce wa dukan mutane, “Ku zo nan wurina.” Suka zo wurinsa, ya kuma shirya bagaden Ubangiji, da ya riga ya zama kufai.31. Iliya ya ɗauki duwatsu goma sha biyu, ɗaya don kowace kabila zuriyar Yaƙub, wanda maganar Ubangiji ta zo masa, cewa, “Sunanka zai zama Isra’ila.”32. Da waɗannan duwatsun ya gina bagade cikin sunan Ubangiji, ya kuma haƙa wuriya kewaye da shi, isashe da zai ci garwa biyu na irin ƙwayar gyada.33. Ya shirya itace, ya yayyanka bijimin kucu-kucu, ya shimfiɗa shi a itacen. Sa’an nan ya ce musu, “Ku cika manyan tuluna da ruwa, ku zuba a kan hadayar da kuma a kan itacen.” Suka zuba.34. Ya ce, “Ku sāke yin haka,” sai suka sāke yin haka. Ya umarta, “Ku yi haka sau na uku,” suka kuma yi haka sau na uku.35. Ruwan ya gangara kewaye da bagaden har ma ya cika wuriyar.36. A lokacin hadaya, sai annabi Iliya ya zo gaba ya yi addu’a, ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Ibrahim, na Isra’ila da kuma na Yaƙub, bari a sani a yau cewa kai Allah ne a cikin Isra’ila, a kuma san cewa ni bawanka ne, na kuma yi dukan waɗannan abubuwa bisa umarninka.37. Ka amsa mini, ya Ubangiji, ka amsa mini, saboda waɗannan mutane su san cewa kai, ya Ubangiji, kai ne Allah, su kuma san cewa kana sāke juye zukatansu zuwa gare ka.”38. Sai wutar Ubangiji ya fāɗo, ya cinye hadayar, itacen, duwatsun da kuma ƙasar, ya lashe ruwan da yake cikin wuriyar.39. Sa’ad da mutane suka ga wannan, sai suka rusuna, suka sunkuyar da kai suka ce, “ Ubangiji, shi ne Allah! Ubangiji, shi ne Allah!”40. Sa’an nan Iliya ya umarce su, ya ce, “Ku kama annabawan Ba’al, kada ku bar waninsu yă tsere!” Suka kama su, Iliya kuwa ya sa aka gangara da su zuwa Kwarin Kishon, aka yayyanka su a can.41. Sai Iliya ya ce wa Ahab, “Ka haura gida, ka ci, ka sha, gama ina jin motsin ruwan sama mai yawa.”42. Sai Ahab ya ruga don yă ci, yă sha, amma Iliya ya hau kan ƙwanƙolin Karmel, ya rusuna ƙasa, ya sa fuska a tsakanin gwiwarsa.43. Ya ce wa bawansa, “Tafi ka dubi wajen teku.” Sai bawan ya haura ya duba. Ya ce, “Ba kome a can.” Sau bakwai Iliya ya ce, “Koma.”44. Sau na bakwai, bawan ya ce, “Wani girgije ƙarami kamar hannun mutum yana tasowa daga teku.” Sai Iliya ya ce, “Je ka faɗa wa Ahab, ‘Shirya keken yaƙinka, ka gangara kafin ruwan sama yă tare ka.’ ”45. Ana cikin haka, sarari ya ƙara duhunta da girgije, iska ta taso, sai ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauko, Ahab kuwa ya hau zuwa Yezireyel.46. Ikon Ubangiji ya sauko a kan Iliya, ya sha ɗamara, ya ruga a guje a gaban Ahab har zuwa Yezireyel.Zabura 69:29-3629. Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.30. Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.31. Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.32. Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!33. Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.34. Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,35. gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,36. ’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.Karin Magana 17:27-2827. Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne.28. Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.Yohanna 13:21-3821. Bayan Yesu ya faɗi haka, sai ya yi juyayi a ruhu, ya kuma furta cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.”22. Almajiransa suka dubi juna, suka rasa ko da wa yake.23. Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi.24. Sai Siman Bitrus ya taɓa wannan almajirin ya ce, “Tambaye shi, wa yake nufi?”25. Shi kuwa da yake jingine kusa da Yesu, ya ce, “Ubangiji, wane ne?”26. Yesu ya amsa ya ce, “Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.” Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman.27. Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, “Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.”28. Amma ba wani a wurin cin abincin da ya fahimci dalilin da ya sa Yesu ya faɗa masa haka.29. Da yake Yahuda ne ma’aji, waɗansunsu suka ɗauka Yesu yana ce masa yă sayi abin da ake bukata don Bikin ne, ko kuwa yă ba wa matalauta wani abu.30. Nan da nan da Yahuda ya karɓi burodin, sai ya fita. A lokacin kuwa dare ya yi.31. Da ya tafi, sai Yesu ya ce, “Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.32. In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.33. “’Ya’yana, zan kasance da ku na ɗan ƙanƙani lokaci ne. Za ku neme ni. Kuma kamar yadda na gaya wa Yahudawa, haka nake gaya muku yanzu. Inda zan tafi, ba za ku iya zuwa ba.34. “Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.35. Ta haka kowa zai san cewa ku almajiraina ne, in kuna ƙaunar juna.”36. Siman Bitrus ya tambaye shi ya ce, “Ubangiji ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Wurin da za ni, ba za ka iya zuwa yanzu ba, amma za ka bi ni daga baya.”37. Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”38. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Anya, za ka iya ba da ranka saboda ni? Gaskiya nake faɗa maka, kafin zakara yă yi cara, za ka yi mūsun sanina sau uku! Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.