Baibul a cikin shekara guda Yuli 11 Tarihi 26:1-321. Ɓangarorin Matsaran Ƙofofi su ne, Daga Korayawa, Meshelemiya ɗan Kore, ɗaya daga cikin ’ya’yan Asaf maza.2. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza. Zakariya ɗan fari, Yediyayel na biyu, Zebadiya na uku, Yatniyel na huɗu,3. Elam na biyar, Yehohanan na shida da Eliyehoyenai na bakwai.4. Obed-Edom shi ma yana da ’ya’ya maza. Shemahiya ɗan fari, Yehozabad na biyu, Yowa na uku, Sakar na huɗu Netanel na biyar,5. Ammiyel na shida, Issakar na bakwai da Feyuletai na takwas. (Gama Allah ya albarkace Obed-Edom.)6. Ɗan Obed-Edom, wato, Shemahiya shi ma yana da ’ya’ya maza, waɗanda suke shugabanni a cikin iyalin mahaifinsu, gama su jarumawa ne ƙwarai.7. ’Ya’yan Shemahiya maza su ne, Otni, Rafayel, Obed da Elzabad; danginsa Elihu da Shemahiya su ma jarumawa ne.8. Ɗaukan waɗannan zuriyar Obed-Edom ne; su da ’ya’yansu maza da danginsu, jarumawa ne masu ƙarfin yin aiki. Zuriyar Obed-Edom, mutum 62 ne duka.9. Meshelemiya yana da ’ya’ya maza da kuma ’yan’uwa, waɗanda jarumawa ne, su 18 ne duka.10. Hosa dangin Merari yana da ’ya’ya maza. Shimri na fari (ko da yake ba shi ne ɗan fari ba, mahaifinsa ya sa shi na fari),11. Hilkiya ne na biyu, Tabaliya ne na uku sai kuma Zakariya na huɗu. ’Ya’ya da dangin Hosa su 13 ne duka.12. Waɗannan ɓangarori na matsaran ƙofofi, ta wurin manyansu, suna da ayyukan yin hidima a haikalin Ubangiji, kamar yadda danginsu suke da shi.13. Aka jefa ƙuri’u don kowace ƙofa bisa ga iyalansu, ƙarami da babba.14. Ƙuri’a don Ƙofar Gabas ta fāɗo a kan Shelemiya. Sai aka jefa ƙuri’u don ɗansa Zakariya, mai ba da shawara mai ma’ana, sai ƙuri’a ta ƙofar arewa ta fāɗo a kansa.15. Ƙuri’a don Ƙofar Kudu ta fāɗo a kan Obed-Edom, ƙuri’a don ɗakin ajiya kuwa ta fāɗo a kan ’ya’yansa maza.16. Ƙuri’u don Ƙofar Yamma da kuma Ƙofar Shalleket a hanyar bisa suka fāɗo a kan Shuffim da Hosa. Aikin tsaro bisa ga mai tsaro.17. Akwai Lawiyawa shida da suke tsaron ƙofar gabas, huɗu a ƙofar kudu, huɗu kuma a ƙofar arewa, biyu-biyu suke tsaron ɗakunan ajiya.18. Game da filin waje ta yamma kuwa, akwai masu tsaro huɗu a hanya da kuma biyu a filin kansa.19. Waɗannan su ne ɓangarori na matsaran ƙofofi waɗanda suke zuriyar Kora da Merari.20. ’Yan’uwansu Lawiyawa kuwa su ne suke lura da ma’ajin gidan Allah da kuma baitulmali don kayayyakin da aka keɓe.21. Ladan ɗan Gershon ne, kuma kaka ga iyalai masu yawa, har ma da iyalin ɗansa Yehiyeli,22. ’ya’yan Yehiyeli maza su ne, Zetam da ɗan’uwansa Yowel. Su ne suke kula da ma’ajin haikalin Ubangiji.23. Daga zuriyar Amram, Izhar, mutanen Hebron da kuma Uzziyel, su ma aka ba su aiki.24. Shebuwel ɗan Gershom, daga zuriyar Musa, shi ne babban jami’i mai lura da baitulmali.25. Danginsa na wajen Eliyezer su ne, Rehabiya, Yeshahiya, Yoram, Zikri da Shelomit.26. Shelomit da danginsa su ne suke lura da dukan baitulmali don kayayyakin da Sarki Dawuda ya keɓe, ta wajen kawunan iyalai waɗanda suke shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da kuma wajen sauran shugabannin mayaƙa.27. Sun keɓe waɗansu ganimar da aka kwaso a yaƙi don gyaran haikalin Ubangiji.28. Shelomit da ’yan’uwansa suka lura da dukan abubuwan da annabi Sama’ila da Shawulu ɗan Kish, da Abner ɗan Ner, da Yowab ɗan Zeruhiya suka keɓe.29. Daga mutanen Izhar, Kenaniya da ’ya’yansa maza su aka sa a ayyukan da ba na haikali ba, su suka zama manya da kuma alƙalai a bisa Isra’ila.30. Daga zuriyar Hebron, Hashabiya da danginsa, su jarumawa dubu ɗaya da ɗari bakwai ne, su suke lura da Isra’ila yamma da Urdun don dukan aikin Ubangiji da kuma hidimar sarki.31. Game da zuriyar Hebron kuwa, Yeriya ne babba bisa ga tarihin zuriyar iyalansu. A shekara ta arba’in ta sarautar Dawuda, sai aka yi binciken tarihi, aka tarar jarumawa cikin zuriyar Hebron suna zama a Yazer cikin Gileyad ne.32. Yeriya yana da ’yan’uwa guda dubu biyu da ɗari bakwai, jarumawa da kuma kawunan iyalai, sai Sarki Dawuda ya sa su lura da mutanen Ruben, Gad da rabin kabilar Manasse game da kome da ya shafi Allah da kuma al’amuran sarki.1 Tarihi 27:1-341. Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.2. Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.3. Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko.4. Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.5. Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa.6. Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa.7. Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.8. Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.9. Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.10. Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.11. Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.12. Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.13. Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.14. Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.15. Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.16. Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila, bisa mutanen Ruben su ne, Eliyezer ɗan Zikri; bisa mutanen Simeyon shi ne, Shefatiya ɗan Ma’aka17. bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel; bisa mutanen Haruna shi ne, Zadok;18. bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda; bisa mutanen Issakar shi ne, Omri ɗan Mika’ilu;19. bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya; bisa mutanen Naftali shi ne, Yerimot ɗan Azriyel;20. bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya; bisa rabin kabilar Manasse shi ne, Yowel ɗan Fedahiya;21. bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya; bisa mutanen Benyamin shi ne, Ya’asiyel ɗan Abner;22. bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham. Waɗannan su ne shugabanni a bisa kabilan Isra’ila.23. Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.24. Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.25. Azmawet ɗan Adiyel shi ne mai lura da ɗakuna ajiyar fada. Yonatan ɗan Uzziya shi ne mai lura da ɗakunan ajiya a yankuna, cikin garuruwa, ƙauyuka da kuma hasumiyoyin tsaro.26. Ezri ɗan Kelub shi ne mai lura da ma’aikatan gona waɗanda suke nome ƙasar.27. Shimeyi mutumin Ramat shi ne mai lura da gonakin inabi. Zabdi mutumin Shifam shi ne mai lura da amfanin gonakin inabi don matsin ruwan inabi.28. Ba’al-Hanan mutumin Geder shi ne mai lura da itatuwan zaitun da na al’ul a gindin tuddan yamma. Yowash shi ne mai lura da tanadin man zaitun.29. Shitrai mutumin Sharon shi ne mai lura da garkuna masu kiwo a Sharon. Shafat ɗan Adlai shi ne mai lura da garkuna a kwari.30. Obil mutumin Ishmayel shi ne mai lura da raƙuma. Yedehiya mutumin Meronot shi ne mai lura da jakuna.31. Yaziz mutumin Hagiri shi ne mai lura da tumaki. Dukan waɗannan shugabanni ne masu lura da mallakar Sarki Dawuda.32. Yonatan, kawun Dawuda, shi ne mashawarci, mutum mai hangen nesa kuma marubuci. Yehiyel ɗan Hakmoni ne ya lura da ’ya’yan sarki maza.33. Ahitofel shi ne mashawarcin sarki. Hushai mutumin Arkitawa shi ne abokin sarki na kud da kud.34. Yehohiyada ɗan Benahiya da Abiyatar ne suka gāji Ahitofel. Yowab shi ne shugaban mayaƙan masarauta.Zabura 78:56-6656. Amma suka gwada Allah suka tayar wa Mafi Ɗaukaka; ba su kiyaye ƙa’idodinsa ba.57. Kamar kakanninsu suka zama marasa biyayya da marasa aminci, marar tabbas kamar tanƙwararren baka.58. Suka ba shi haushi da masujadansu na kan tudu; suka tayar da kishinsa da gumakansu.59. Sa’ad da Allah ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; ya ƙi Isra’ila gaba ɗaya.60. Ya yashe tabanakul na Shilo, tentin da ya kafa a cikin mutane.61. Ya aika da akwatin alkawarin ƙarfinsa zuwa bauta, darajarsa zuwa cikin hannuwan abokin gāba.62. Ya ba da mutanensa ga takobi; ya yi fushi ƙwarai da gādonsa.63. Wuta ta cinye matasansu maza, ’yan matansu kuma ba su da waƙoƙin aure;64. aka karkashe firistocinsu, gwaurayensu kuwa ba su iya makoki ba.65. Sa’an nan Ubangiji ya farka sai ka ce daga barcinsa, kamar yadda mutum kan farka daga buguwar ruwan inabi.66. Ya kori abokan gābansa; ya sa suka sha madawwamiyar kunya.Karin Magana 20:4-54. Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.5. Manufofin zuciyar mutum zurfafan ruwaye ne, amma mutum mai basira yakan jawo su.Ayyukan Manzanni 10:1-231. A Kaisariya akwai wani mutum mai suna Korneliyus, wani jarumin Roma ne, a ƙungiyar soja da ake kira Bataliyar Italiya.2. Shi da dukan iyalinsa masu ibada ne masu tsoron Allah kuma; yakan ba da kyauta hannu sake ga masu bukata yana kuma addu’a ga Allah ba fasawa.3. Wata rana wajen ƙarfe uku na yamma ya ga wahayi. A sarari ya ga wani mala’ikan Allah, wanda ya zo wajensa ya ce, “Korneliyus!”4. Korneliyus kuwa ya zura masa ido a tsorace ya ce, “Mene ne, ya Ubangiji?” Mala’ikan ya ce, “Addu’o’inka da kyautanka ga matalauta sun kai har sama, hadayar tunawa ce a gaban Allah.5. Yanzu sai ka aiki mutane zuwa Yoffa su dawo da wani mutum mai suna Siman wanda ake kira Bitrus.6. Yana zama tare da Siman, mai aikin fatu, wanda gidansa ke bakin teku.”7. Sa’ad da mala’ikan da ya yi masa magana ya tafi, sai Korneliyus ya kira biyu daga cikin bayinsa da kuma wani soja mai ibada wanda yake ɗaya a cikin masu yin masa hidima.8. Ya fada musu duk abin da ya faru sa’an nan ya aike su Yoffa.9. Wajen tsakar rana kashegari yayinda suke cikin tafiyarsu suna kuma dab da birnin, sai Bitrus ya hau bisan rufin gida yă yi addu’a.10. Yunwa ta kama shi ya kuwa so yă ci wani abu, yayinda ake shirya abinci, sai wahayi ya zo masa.11. Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu.12. Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama.13. Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”14. Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”15. Muryar ta yi magana da shi sau na biyu ta ce, “Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.”16. Wannan ya faru har sau uku, sai nan da nan aka ɗauke mayafin zuwa sama.17. Tun Bitrus yana cikin tunani game da ma’anar wahayin nan, sai ga mutanen da Korneliyus ya aika sun sami gidan Siman suna kuma tsaye a ƙofar.18. Suka yi sallama, suna tambaya ko Siman wanda aka sani da suna Bitrus yana zama a can.19. Yayinda Bitrus yana cikin tunani game da wahayin, sai Ruhu ya ce masa, “Siman, ga mutum uku suna nemanka.20. Saboda haka ka tashi ka sauka. Kada ka yi wata-wata, gama ni ne na aiko su.”21. Sai Bitrus ya sauka ya ce wa mutanen, “Ni ne kuke nema. Me ya kawo ku?”22. Mutanen suka amsa, “Mun zo ne daga wurin Korneliyus wani jarumin. Shi mutum ne mai adalci mai tsoron Allah kuma, wanda dukan Yahudawa ke girmamawa. Wani mala’ika mai tsarki ya faɗa masa, yă sa ka zo gidansa don yă ji abin da za ka faɗa.”23. Sai Bitrus ya gayyaci mutanen cikin gida su zama baƙinsa. Kashegari Bitrus ya tafi tare da su, waɗansu ’yan’uwa daga Yoffa kuwa suka tafi tare da shi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.