Baibul a cikin shekara guda Yuli 102 Tarihi 15:1-191. Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded.2. Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, “Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku.3. Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka.4. Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi.5. A waɗancan kwanaki akwai hatsari a yin tafiye-tafiye, gama dukan mazaunan ƙasashe suna cikin babbar damuwa.6. Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa.7. Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku.”8. Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji.9. Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.10. Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta mulkin Asa.11. A lokacin suka miƙa hadaya bijimai ɗari bakwai da tumaki da kuma awaki dubu bakwai ga Ubangiji daga ganimar da suka dawo da ita.12. Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu.13. Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace.14. Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni.15. Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe.16. Sarki Asa ya tuɓe mahaifiyar mahaifiyarsa daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, domin ta gina ginshiƙin banƙyama na Ashera. Asa ya rurrushe shi, ya farfasa shi ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron.17. Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa.18. Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyaki a haikalin Allah waɗanda shi da mahaifinsa suka keɓe.19. Ba a ƙara yin yaƙi ba sai a shekara ta talatin da biyar ta mulkin Asa.2 Tarihi 16:1-141. A shekara ta talatin da shida ta mulkin Asa, Ba’asha sarkin Isra’ila ya haura don yă yaƙi Yahuda da Rama mai katanga, don kuma yă hana wani daga fita ko shiga yankin Asa sarkin Yahuda.2. Sai Asa ya ɗauki azurfa da zinariya daga ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma na fadansa ya aika wa Ben-Hadad sarkin Aram, wanda yake mulki a Damaskus.3. Ya ce, “Bari yarjejjeniya ta kasance tsakani na da kai kamar yadda ya kasance tsakanin mahaifina da mahaifinka. Dubi ina aika maka azurfa da zinariya. Yanzu ka yanke yarjejjeniya da Ba’asha sarkin Isra’ila domin yă janye daga gare ni.”4. Ben-Hadad ya yarda da Sarki Asa ya kuma aika da manyan hafsoshin mayaƙansa a kan garuruwan Isra’ila. Suka ci Iyon, Dan, Abel-Mayim da kuma dukan biranen ajiya na Naftali.5. Da Ba’asha ya ji wannan, ya daina ginin Rama ya yashe aikinsa.6. Sa’an nan Sarki Asa ya kawo dukan mutanen Yahuda, suka kuma kwashe duwatsu da katako daga Rama waɗanda Ba’asha yake amfani da su. Da su ne Asa ya gina Geba da Mizfa.7. A lokacin Hanani mai duba ya zo wurin Asa sarkin Yahuda ya ce masa, “Don ka dogara ga sarkin Aram, ba kuwa ga Ubangiji Allahnka ba ne mayaƙan sarkin Aram sun kuɓuce daga hannunka.8. Ai, Kushawa da Libiyawa rundunar sojoji ne masu yawan gaske, suna kuma da kekunan yaƙi da mahayan dawakai masu yawa ƙwarai. Amma duk da haka, saboda ka dogara ga Ubangiji, ya kuwa ba da su cikin hannunka.9. Gama gaban Ubangiji yana ko’ina a duniya don yă ƙarfafa waɗanda zukatansu suke binsa cikin aminci. Ka yi wauta, daga yanzu nan gaba za ka yi ta yaƙi.”10. Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.11. Ayyukan mulkin Asa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.12. A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci.13. Sa’an nan a shekara ta arba’in da ɗaya ta mulkinsa, Asa ya mutu ya kuma huta tare da kakanninsa.14. Suka binne shi a kabarin da ya fafe wa kansa a Birnin Dawuda. Suka sa shi a makara wadda aka rufe da kayan yaji da kuma turare dabam-dabam da aka niƙa, suka kuma ƙuna babbar wuta don girmama shi.Zabura 81:6-106. Ya ce, “Na kau da nauyi daga kafaɗunku; an ’yantar da hannuwansu daga kwando.7. Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba.8. “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa gargaɗe ku, in ba za ku saurare ni ba, ya Isra’ila!9. Kada ku kasance da baƙon allah a cikinku; ba za ku rusuna ga baƙon allah ba.10. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.Karin Magana 20:24-2524. Ubangiji ne yake bi da matakan mutum, Ta yaya wani zai fahimci hanyarsa?25. Tarko ne ga mutum ya keɓe wani abu da ba tunani daga baya kuma ya yi la’akari da alkawarinsa.Ayyukan Manzanni 16:1-211. Bulus ya kai Derbe sa’an nan kuma zuwa Listira, inda wani almajiri mai suna Timoti yake da zama, wanda mahaifiyarsa mutuniyar Yahuda ce kuma mai bi ce, amma mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.2. ’Yan’uwa a Listira da Ikoniyum sun yi magana mai kyau ƙwarai a kansa.3. Bulus ya so ya ɗauke shi a tafiyar, saboda haka ya yi masa kaciya, domin Yahudawan da suke da zama a wurin, don duk sun san cewa mahaifinsa mutumin Hellenawa ne.4. Yayinda suke tafiya daga gari zuwa gari, suka dinga ba da shawarwarin da manzanni da dattawa a Urushalima suka zartar domin mutane su kiyaye.5. Saboda haka ikkilisiyoyi suka ginu cikin bangaskiya suka kuma yi girma suka yi ta ƙaruwa kowace rana.6. Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya.7. Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba.8. Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas.9. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.”10. Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.11. Daga Toruwas muka tashi zuwa teku muka kuma shiga jirgin ruwa muka miƙe kai tsaye zuwa Samotiras, kashegari kuma muka nufi Neyafolis.12. Daga can muka tafi Filibbi, wata babbar alkaryar Roma wadda kuma take babban birni a gundumar Makidoniya. Muka zauna a can kwanaki masu yawa.13. A Asabbaci, muka fita ƙofar birnin zuwa bakin kogi, inda muke tsammani za mu sami wurin yin addu’a. Muka zauna muka fara yin wa matan da suka taru a can magana.14. Ɗaya daga cikin waɗanda suka saurare mu mace ce mai suna Lidiya, mai sayar da yadunan jan garura masu tsada daga birnin Tiyatira, mai yi wa Allah sujada. Ubangiji ya buɗe zuciyarta har ta karɓi saƙon Bulus.15. Da aka yi mata baftisma tare da iyalin gidanta, sai ta gayyace mu zuwa gidanta. Ta ce, “In kun amince ni mai bi ce cikin Ubangiji, sai ku zo ku sauka a gidana.” Sai ta kuwa rinjaye mu.16. Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi.17. Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.”18. Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita.19. Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma.20. Sai suka kawo su a gaban alƙalai suka ce, “Waɗannan Yahudawa ne, suna kuma birkitar mana da gari,21. ta wurin koyar da al’adun da ba daidai ba ne mu Romawa mu karɓa ko mu aikata.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.