Baibul a cikin shekara guda Yuli 162 Tarihi 28:1-271. Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba.2. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila ya kuma yi zubin gumaka domin a bauta wa Ba’al.3. Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.4. Ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a masujadan kan tudu, a bisa tuddai da kuma ƙarƙashin kowane itace mai inuwa.5. Saboda haka Ubangiji Allahnsa ya miƙa shi ga sarkin Aram. Arameyawa suka ci shi a yaƙi, suka kuma kwashe mutanensa da yawa a matsayin ’yan kurkuku, suka kawo Damaskus. Ya kuma ba da shi ga sarkin Isra’ila, wanda ya jijji masa a yaƙi.6. A rana ɗaya Feka ɗan Remaliya ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu ashirin a Yahuda, domin Yahuda sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu.7. Zikri, wani jarumin Efraim, ya kashe Ma’asehiya ɗan sarki, Azrikam hafsa mai lura da fada, da kuma Elkana, mataimakin sarki.8. Isra’ilawa suka kame kamammu daga ’yan’uwansu mata, ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata dubu ɗari biyu. Suka kuma kwashe ganima mai yawan gaske, waɗanda suka kwasa zuwa Samariya.9. Amma wani annabin Ubangiji mai suna Oded yana a can, sai ya fito don yă sadu da mayaƙa sa’ad da suke komowa zuwa Samariya. Ya ce musu, “Domin Ubangiji Allah na kakanninku yana fushi da Yahuda, ya ba da su cikin hannunku. Sai kuka kashe su cikin fushin da ya kai sama.10. Yanzu kuma kuna niyya ku mai da maza da matan Yahuda da Urushalima bayinku. Amma ku ɗin ba ku da laifin zunubi ga Ubangiji Allahnku ne?11. To, ku saurare ni! Ku mai da ’yan’uwanku da kuka kama a matsayin ’yan kurkuku, gama fushin Ubangiji yana a kanku.”12. Sai waɗansu shugabanni a Efraim, Azariya ɗan Yehohanan, Berekiya ɗan Meshillemot, Hezekiya ɗan Shallum da Amasa ɗan Hadlai, suka tasar wa waɗanda suke isowa daga yaƙi.13. Suka ce, “Dole ku kawo waɗannan ’yan kurkukun a nan, ko kuwa za ku yi laifi a gaban Ubangiji. Kuna niyya ku ƙara ga zunubinmu da kuma laifinmu? Gama laifinmu ya riga ya yi yawa, kuma fushinsa mai tsanani yana a kan Isra’ila.”14. Saboda haka sojoji suka ba da ’yan kurkukun da ganima a gaban hafsoshi da dukan taron.15. Sai mutanen da aka kira sunansu suka tashi, suka ɗauki kamammun, da ganimar, suka sa wa dukan waɗanda suke tsirara sutura. Suka sa musu sutura, suka ba su takalma, suka ba su abinci da abin sha, suka shafa musu mai. Suka hawar da dukan raunana a kan jakuna, suka kai su wurin ’yan’uwansu a Yeriko, wato, Birnin Itatuwan Dabino, sa’an nan suka koma Samariya.16. A lokacin nan Sarki Ahaz ya aika wurin sarkin Assuriya neman taimako.17. Mutanen Edom sun sāke zuwa suka yaƙi Yahuda suka kuma kwashe ’yan kurkuku,18. yayinda Filistiyawa suka kai hari wa garuruwa a gindin tuddai da kuma a Negeb na Yahuda. Suka kame su suka kuma zauna a Bet-Shemesh, Aiyalon da Gederot, haka ma Soko, Timna da Gimzo tare da ƙauyuka kewayensu.19. Ubangiji ya ƙasƙantar da Yahuda saboda Ahaz sarkin Isra’ila, gama ya hadasa mugunta a Yahuda kuma ya kasance marar aminci ga Ubangiji.20. Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo wurinsa, sai ya wahalar da sarki Ahaz maimakon taimakonsa.21. Ahaz ya ɗauki waɗansu abubuwa daga haikalin Ubangiji da kuma daga fadan sarki da kuma daga sarakuna, ya ba da su ga sarkin Assuriya, amma wannan bai taimake shi ba.22. Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji.23. Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila.24. Ahaz ya tattara kayayyaki daga haikalin Allah ya kwashe su. Ya kulle ƙofofin haikalin Ubangiji ya kakkafa bagadai a kowace kusurwa a titin Urushalima.25. A kowane gari a Yahuda, ya gina masujadan kan tudu don ƙone hadayu ga waɗansu alloli, ya kuma tsokane Ubangiji Allah na kakanninsa ya yi fushi.26. Sauran ayyukan mulkinsa da dukan hanyoyinsa, daga farko zuwa ƙarshe, suna a rubuce a littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.27. Ahaz ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a birnin Urushalima, amma ba a sa shi a makabartan sarakunan Isra’ila ba. Sai Hezekiya ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.2 Tarihi 29:1-361. Hezekiya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Abiya, ’yar Zakariya.2. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda kakansa Dawuda ya yi.3. A wata na farkon a farkon shekarar mulkinsa, ya buɗe ƙofofin haikalin Ubangiji ya gyara su.4. Ya kawo firistoci da Lawiyawa, ya tattara su a filin da yake a gefen gabas5. ya kuma ce musu, “Ku saurare ni, Lawiyawa! Ku tsarkake kanku yanzu, ku kuma tsarkake haikalin Ubangiji Allah na kakanninku. Ku fid da ƙazanta daga wuri mai tsarki.6. Kakanninku ba su yi aminci ba; suka aikata abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnmu, suka kuma yashe shi. Suka juya fuskokinsu daga mazaunin Ubangiji suka kuma juya masa baya.7. Suka kulle ƙofofin shirayi, suka kuma kashe fitilu. Ba su ƙone turare ko su miƙa hadayun ƙonawa a wuri mai tsarki ga Allah na Isra’ila ba.8. Saboda haka, fushin Ubangiji ya fāɗo a kan Yahuda da Urushalima; ya mai da su abin tsoro da abin banrazana da kuma abin ba’a, kamar yadda kuke gani da idanunku.9. Abin da ya sa ke nan kakanninmu suka fāɗi ta takobi, kuma shi ya sa aka kai ’ya’yanmu maza da ’ya’yanmu mata da matanmu bauta.10. Yanzu ina niyya in yi alkawari da Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin fushinsa yă kauce daga gare mu.11. ’Ya’yana maza, kada ku yi sakaci yanzu, gama Ubangiji ya zaɓe ku don ku tsaya a gabansa ku kuma yi masa hidima, don ku yi hidima a gabansa ku kuma ƙone turare.”12. Sai waɗannan Lawiyawa suka shiga aiki, daga Kohatawa Mahat ɗan Amasai da Yowel ɗan Azariya. Daga Kabilar Merari, Kish ɗan Abdi da Azariya ɗan Yahallelel. Daga Gershonawa, Yowa ɗan Zimma da Eden ɗan Yowa.13. Daga zuriyar Elizafan, Shimri da Yehiyel. Daga zuriyar Asaf, Zakariya da Mattaniya.14. Daga iyalin Heman, Yehiyel da Shimeyi. Daga zuriyar Yedutun, Shemahiya da Uzziyel.15. Da suka tattara ’yan’uwansu suka kuma tsarkake kansu, sai suka shiga ciki suka tsarkake haikalin Ubangiji, kamar yadda sarki ya umarta, suna bin maganar Ubangiji.16. Firistoci suka shiga cikin wuri mai tsarki na Ubangiji suka tsarkake shi. Suka fitar da dukan abin da yake marar tsabta da suka samu a haikalin Ubangiji zuwa filin haikalin Ubangiji. Lawiyawa suka ɗauke su suka kai su Kwarin Kidron.17. Suka fara tsarkakewar a rana ta farko na farkon wata, a rana ta takwas na watan kuwa suka kai shirayin Ubangiji. Karin kwana takwas kuma suka tsarkake haikalin Ubangiji kansa, suka gama a rana ta goma sha shida na farkon wata.18. Sa’an nan suka tafi wurin Sarki Hezekiya suka faɗa masa, “Mun tsarkake haikalin Ubangiji gaba ɗaya, bagaden ƙone hadaya tare da dukan kayayyakinsa, da tebur don shirya tsarkaken burodi, tare da dukan kayayyakinsa.19. Mun shirya muka kuma tsarkake dukan kayayyakin da Sarki Ahaz ya cire cikin rashin amincinsa yayinda yake sarki. Yanzu suna a gaban bagaden Ubangiji.”20. Da sassafe kashegari Sarki Hezekiya ya tattara manyan birni wuri ɗaya, suka haura zuwa haikalin Ubangiji.21. Suka kawo bijimai bakwai, raguna bakwai, bunsurai bakwai da kuma awaki mata bakwai a matsayin hadaya don zunubi domin masarauta, domin wuri mai tsarki da kuma domin Yahuda. Sarki ya umarce firistoci, zuriyar Haruna, su miƙa waɗannan a bagaden Ubangiji.22. Saboda haka suka yayyanka bijiman, firistoci suka karɓi jinin suka yayyafa a kan bagade. Suka kuma yanka ragunan suka yayyafa jinin a bagaden. Haka kuma suka yanka ’yan ragunan suka yayyafa jinin a bagaden.23. Aka kawo awaki domin hadaya don zunubi a gaban sarki da taron, suka kuwa ɗibiya hannuwansu a kansu.24. Sa’an nan firistoci suka yayyanka awakin suka miƙa jininsu a bagade domin hadaya don zunubi don kafara saboda dukan Isra’ila, domin sarki ya umarta a yi hadaya ta ƙonawa da hadaya don zunubi domin dukan Isra’ila.25. Sarki Hezekiya ya ajiye Lawiyawa a cikin haikalin Ubangiji tare da ganguna, garayu da molaye, yadda Dawuda da Gad mai duba na sarki da kuma annabi Natan suka tsara. Ubangiji ne ya umarta wannan ta wurin annabawansa.26. Saboda haka Lawiyawa suka tsaya a shirye tare da kayan kiɗin Dawuda, firistoci kuma tare da ƙahoninsu.27. Hezekiya ya ba da umarni a miƙa hadaya ta ƙonawa a kan bagade. Yayinda aka fara miƙawa, ana rerawa ga Ubangiji, tare da bushe-bushe da kiɗe-kiɗen kayan waƙa na Dawuda sarkin Isra’ila.28. Dukan taron suka durƙusa suka yi sujada, yayinda mawaƙa suke rerawa, ana kuma busa ƙahoni, dukan wannan ya ci gaba sai da aka gama miƙa hadaya ta ƙonawa.29. Sa’ad da aka gama miƙawa, sai sarki da mutanen da suke tare da shi suka durƙusa suka yi sujada.30. Sarki Hezekiya da fadawansa suka umarci Lawiyawa su yabi Ubangiji da kalmomin Dawuda da na Asaf mai duba. Saboda haka suka rera yabai da murna, suka sunkuyar da kawunansu suka yi sujada.31. Sa’an nan Hezekiya ya ce, “Yanzu kun keɓe kanku ga Ubangiji. Ku zo ku kuma kawo hadayu da hadayun godiya zuwa ga haikalin Ubangiji.” Saboda haka taron suka kawo hadayu da hadayun godiya, da kuma dukan waɗanda suke da niyya suka kawo hadayun ƙonawa.32. Yawan hadayun ƙonawan da taron suka kawo, bijimai saba’in ne, raguna ɗari da kuma bunsurai ɗari biyu, dukansu kuwa domin hadayun ƙonawa ga Ubangiji ne.33. Dabbobin da aka tsarkake a matsayi hadayu sun kai bijimai ɗari shida da tumaki da kuma awaki dubu uku.34. Firistoci fa, suka kāsa sosai don fiɗan dukan dabbobin da za a miƙa don hadayun ƙonawa; saboda haka ’yan’uwansu Lawiyawa suka taimake su har aka gama aiki kafin sauran firistoci su sami damar tsarkake kansu. Gama Lawiyawa sun fi firistoci himma wajen tsarkakewar kansu.35. Aka kasance da hadayun ƙonawa a yalwace, tare da kitsen hadayun salama da hadayun sha da suke tafe da hadayun ƙonawa. Saboda haka aka sāke kafa hidimar haikalin Ubangiji.36. Hezekiya da dukan mutane suka yi farin ciki game da abin da Allah ya yi wa mutanensa, domin ya faru farat ɗaya.Zabura 84:8-128. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub.9. Ka dubi garkuwarmu, ya Allah; ka duba da alheri a kan shafaffenka.10. Rana guda a filayen gidan sun fi dubu a wani wuri dabam; zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna da in zauna a tentunan mugaye.11. Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.12. Ya Ubangiji Maɗaukaki, mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.Karin Magana 21:6-86. Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.7. Rikicin mugaye zai yi gāba da su, gama sun ƙi su yi abin da yake daidai.8. Hanyar mai laifi karkatacciya ce, amma halin marar laifi sukan aikata gaskiya.Ayyukan Manzanni 19:21-4121. Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.”22. Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.23. Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar.24. Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba.25. Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sana’ar ya ce, “Ku jama’a, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sana’a.26. Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan.27. Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”28. Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”29. Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya.30. Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba.31. Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada yă kuskura ya shiga filin nan.32. Taron kuwa ya ruɗe. Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba.33. Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yă kāre kansa a gaban mutane.34. Amma sa’ad da suka gane shi mutumin Yahuda ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa sa’a biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”35. Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, sa’an nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba tă san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba?36. Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje.37. Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba.38. To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sana’arsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara.39. In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa.40. Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.”41. Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.