Baibul a cikin shekara guda Yuli 182 Tarihi 32:1-331. Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa.2. Sa’ad da Hezekiya ya ga Sennakerib ya zo yana kuma niyya yă yaƙi Urushalima,3. sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi.4. Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?”5. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.6. Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi.7. “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.8. Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.9. Daga baya, sa’ad da Sennakerib sarkin Assuriya da dukan mayaƙansa suke kwanto wa Lakish, sai ya aiki hafsoshinsa da wannan saƙo wa Hezekiya sarkin Yahuda da kuma wa dukan mutanen Yahuda waɗanda suke can cewa,10. “Ga abin da Sennakerib sarkin Assuriya ya ce ga me kake dogara, har da ka dāge cikin Urushalima da aka yi mata kwanto?11. Ai, Hezekiya, ruɗinku yake yi, don yă sa ku mutu da yunwa da ƙishirwa sa’ad da yake ce muku, ‘ Ubangiji Allahnmu zai cece mu daga hannun sarkin Assuriya.’12. Hezekiya kansa bai rushe waɗannan masujadan kan tudu da bagadai, yana ce wa Yahuda da Urushalima, ‘Dole ku yi sujada a gaban bagade guda ku kuma ƙone hadayu a kansa ba’?13. “Ba ku san abin da ni da kuma kakannina suka yi wa dukan mutanen sauran ƙasashe ba? Allolin ƙasashen nan sun taɓa iya ceton ƙasarsu daga hannuna ne?14. Wanne a cikin dukan allolin waɗannan ƙasashe da kakannina suka hallaka ya taɓa iya ceton mutanensa daga gare ni? To, yaya Allahnku zai iya cetonku daga hannuna?15. Yanzu fa, kada ku bar Hezekiya yă ruɗe ku yă kuma ɓad da ku haka. Kada ku gaskata shi, gama babu allahn wata ƙasa ko masarautar da ya taɓa iya ceton mutanensa daga hannuna ko kuwa hannun kakannina. Balle har Allahnku yă cece ku daga hannuna!”16. Hafsoshin Sennakerib suka ci gaba da maganar banza wa Ubangiji Allah da kuma a kan bawansa Hezekiya.17. Sarki ya kuma rubuta wasiƙu yana zagin Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana faɗin wannan a kansa, “Kamar yadda sauran allolin mutanen sauran ƙasashe ba su iya kuɓutar da mutane daga hannuna ba, haka Allahn Hezekiya ba zai kuɓutar da mutanensa daga hannuna ba.”18. Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin.19. Suka yi magana game da Allah na Urushalima yadda suka yi game da allolin sauran mutanen duniya, aikin hannuwan mutane.20. Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan.21. Sai Ubangiji ya aiki mala’ika, wanda ya karkashe dukan jarumawa da shugabanni da kuma hafsoshi a sansanin sarkin Assuriyawa. Saboda haka sai sarkin Assuriya ya janye zuwa ƙasarsa da kunya. Da ya shiga haikalin Allahnsa, sai waɗansu a cikin ’ya’yansa maza suka yanka shi da takobi.22. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mutanen Urushalima daga hannun Sennakerib sarkin Assuriya da kuma daga hannun dukan sauran. Ya magance su a kowane gefe.23. Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi.24. A kwanakin nan Hezekiya ya yi ciwo, ya yi kusan mutuwa. Sai ya yi addu’a ga Ubangiji, wanda ya amsa masa ya kuma ba shi alama.25. Amma zuciyar Hezekiya ta yi girman kai, bai kuwa yi amfani da alherin da aka nuna masa ba, saboda haka fushin Ubangiji ya sauko a kansa da kuma a kan Yahuda da Urushalima.26. Sai Hezekiya ya tuba daga girma kan zuciyarsa, haka ma mutanen Urushalima; saboda haka fushin Ubangiji bai zo a kansu a kwanakin Hezekiya ba.27. Hezekiya mai arziki da girma ne ƙwarai, ya kuma yi baitulmali domin azurfa da zinariyarsa da kuma domin duwatsu masu daraja, kayan yaji, garkuwoyi da kuma domin dukan kayayyaki masu daraja nasa.28. Ya kuma yi gine-gine domin ajiyar hatsi, sabon ruwa inabi da mai; ya kuma yi wuraren ajiyar kowane irin shanu dabam-dabam, da kuma turke domin tumaki.29. Ya gina ƙauyuka ya kuma samo shanu da garkuna masu yawa, gama Allah ya ba shi arziki mai yawa sosai.30. Hezekiya ne ya datse ruwan bisa na maɓulɓular Gihon, ya sa ruwan ya gangara zuwa gefe yamma na Birnin Dawuda. Ya yi nasara a kome da ya yi.31. Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa.32. Sauran ayyukan mulkin Hezekiya da kuma kyawawa ayyukansa, suna a rubuce a cikin wahayin annabi Ishaya ɗan Amoz, a cikin littafin sarakunan Yahuda da Isra’ila.33. Hezekiya ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a kan tudu inda makabartan zuriyar Dawuda suke. Dukan Yahuda da kuma mutanen Urushalima suka girmama shi sa’ad da ya mutu. Sai Manasse ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.2 Tarihi 33:1-251. Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar.2. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.3. Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada.4. Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.”5. Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari.6. Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.7. Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.8. Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.”9. Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.10. Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba.11. Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon.12. Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.13. Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.14. Daga baya ya sāke gina katangar waje na Birnin Dawuda, yamma da maɓulɓular Gihon a cikin kwari, har zuwa mashigin Ƙofar Kifi, ya kuma kewaye tudun Ofel; ya yi ta da tsayi sosai. Ya sa hafsoshin mayaƙa cikin dukan biranen katanga a Yahuda.15. Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni.16. Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila.17. Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai.18. Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila.19. Addu’arsa da yadda Allah ya taɓu ta wurin tubansa, da kuma dukan zunubansa da rashin biyayyarsa, da wuraren da ya gina masujadan kan tudu ya kuma kafa ginshiƙan Ashera da gumaka kafin ya ƙasƙantar da kansa, duka suna a rubuce cikin tarihin mai duba.20. Manasse ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a fadansa. Sai Amon ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.21. Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu.22. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi.23. Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.24. Fadawan Amon sukan yi masa maƙarƙashiya, suka kashe shi a fadansa.25. Sa’an nan mutanen ƙasar suka kashe dukan waɗanda suka yi wa Sarki Amon maƙarƙashiya, suka naɗa Yosiya ɗansa sarki a maimakonsa.Zabura 85:8-138. Zan saurari abin da Allah Ubangiji zai faɗa; ya yi alkawarin salama ga mutanensa, tsarkakansa, amma kada su koma ga wauta.9. Tabbatacce cetonsa yana kusa da waɗanda suke tsoronsa, don ɗaukakarsa ta zauna a cikin ƙasarmu.10. Ƙauna da aminci za su sadu; adalci da salama za su yi wa juna sumba.11. Aminci zai ɓulɓulo daga ƙasa, adalci kuma yă duba daga sama.12. Ubangiji tabbatacce zai bayar da abin da yake da kyau, ƙasarmu kuwa za tă ba da amfaninta.13. Adalci na tafiya a gabansa yana shirya hanya domin ƙafafunsa.Karin Magana 21:12-1212. Mai Adalci kan lura da gidan mugu kan kuma zama sanadin lalacin mugu.Ayyukan Manzanni 20:17-3817. Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya.18. Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya.19. Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa.20. Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida.21. Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.22. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba.23. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana.24. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.25. “Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina.26. Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina.27. Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba.28. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.29. Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba.30. Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai.31. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.32. “To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake.33. Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba.34. Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina.35. Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”36. Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a.37. Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba.38. Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.