Baibul a cikin shekara guda Yuli 192 Tarihi 34:1-331. Yosiya yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara talatin da ɗaya.2. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin kakansa Dawuda, ba tare da juye dama ko hagu ba.3. A shekara ta takwas ta mulkinsa, yayinda yake matashi, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma sha biyunsa ya fara tsabtacce Yahuda da Urushalima daga masujadan kan tudu, ginshiƙan Ashera, sassaƙaƙƙun gumaka da kuma siffofin da aka yi zubi.4. A ƙarƙashin umarninsa aka rurrushe bagadan Ba’al, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu, ya farfashe ginshiƙan Ashera da kuma sassaƙaƙƙun siffofi. Ya ragargaza waɗannan kucu-kucu, ya barbaɗa su a kan kaburburan waɗanda suka miƙa musu hadayu.5. Ya ƙone ƙasusuwan firistocin gumaka a kan bagaden da a dā suke miƙa hadayunsu, ta haka ya tsabtacce Yahuda da Urushalima.6. Ya yi haka cikin garuruwan Manasse, Efraim da Simeyon, har zuwa Naftali, da kuma cikin kangwayen kewayensu,7. ya farfashe bagadai da ginshiƙan Ashera; ya niƙa gumaka suka zama gari, ya kuma yayyanka dukan bagadan turare kucu-kucu ko’ina a Isra’ila. Sa’an nan ya koma Urushalima.8. A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya, ya tsarkake ƙasar da haikalin, ya aiki Shafan ɗan Azaliya da Ma’asehiya mai mulkin birni, tare da Yowa ɗan Yowahaz, marubuci, su gyara haikalin Ubangiji Allah.9. Suka tafi wurin Hilkiya babban firist suka ba shi kuɗin da aka kawo cikin haikalin Allah, wanda Lawiyawa masu tsaron ƙofofi sun tattara daga mutanen Manasse, Efraim da dukan raguwar Isra’ila da kuma daga dukan mutanen Yahuda da Benyamin da kuma mazaunan Urushalima.10. Sa’an nan suka danƙa su ga mutanen da aka naɗa su lura da aiki a kan haikalin Ubangiji. Waɗannan mutane ne suke biyan ma’aikatan da suka gyara suka kuma mai da haikalin.11. Suka kuma ba da kuɗi ga kafintoci da magina don su sayi sassaƙaƙƙun duwatsu, da katakai don yin tsaiko da tankar ginin da sarakunan Yahuda suka bari yă fāɗi ya zama kango.12. Mutanen fa suka yi aiki da aminci. Shugabanninsu, su ne Yahat da Obadiya, Lawiyawa zuriyar Merari da Zakariya da Meshullam, zuriyar Kohat. Dukan Lawiyawa waɗanda suke gwanaye a kayan kiɗi,13. sun lura da ma’aikata, suka kuma lura da dukan masu aiki daga aiki zuwa aiki. Waɗansu Lawiyawan su ne marubuta, magatakarda da kuma masu tsaron ƙofofi.14. Yayinda suke fitar da kuɗin da aka kai cikin haikalin Ubangiji, sai Hilkiya firist ya sami Littafin Dokar Ubangiji da aka bayar ta wurin Musa.15. Hilkiya ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a cikin haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan.16. Sa’an nan Shafan ya ɗauki littafin zuwa wurin sarki, ya faɗa masa, “Manyan ma’aikatanka suna yin kome da aka sa su.17. Mun ɗauke kuɗin da an ajiye a haikalin Ubangiji muka ba wa masu aiki da waɗanda suke lura da su.”18. Sa’an nan Shafan magatakarda ya sanar da sarki ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta daga cikinsa a gaban sarki.19. Da sarki ya ji kalmomin Doka, sai ya yage rigunansa.20. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki.21. Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”22. Hilkiya tare da waɗanda sarki ya aika, suka tafi suka yi magana da annabiya Hulda, wadda take matar Shallum ɗan Tokhat ɗan Hasra, mai tsaron wurin ajiyar riguna. Tana zama a Urushalima, a Yanki na Biyu.23. Sai ta ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce faɗa wa mutumin da ya aike ku gare ni,24. ‘Ga abin da Ubangiji ya ce zai kawo masifa a wannan wuri da mutanensa, dukan la’anar da aka rubuta a cikin littafin da aka karanta a gaban sarkin Yahuda.25. Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’26. Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yake cewa game da kalmomin da ka ji.27. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah sa’ad da ka ji abin da ya yi magana a kan wannan wuri da mutanensa, domin kuma ka ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yage rigunanka ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.28. Yanzu zan tara ka da kakanninka, za a kuma binne ka cikin salama. Idanunka ba za su ga dukan masifar da zan kawo a kan wannan wuri da kuma a kan waɗanda suke zama a nan ba.’ ” Sai suka kai amsar wa sarki.29. Sai sarki ya kira dukan dattawan Yahuda da Urushalima.30. Ya haura zuwa haikalin Ubangiji tare da mutanen Yahuda, mutanen Urushalima, firistoci da Lawiyawa, dukan mutane daga ƙarami zuwa babba. Ya karanta dukan kalmomin Littafin Alkawari wanda aka samu a cikin haikalin Ubangiji a kunnuwansu.31. Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya sabunta alkawari a gaban Ubangiji, don yă bi Ubangiji yă kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma farillansa da dukan zuciyarsa da kuma dukan ransa, ya kuma yi biyayya da kalmomin alkawarin da aka rubuta a cikin wannan littafi.32. Sa’an nan ya sa kowa a Urushalima da Benyamin ya yi alkawari ga wannan; mutanen Urushalima suka aikata wannan bisa ga alkawarin Allah, Allah na kakanninsu.33. Yosiya ya fitar da dukan gumakan banƙyama daga dukan yankunan Isra’ilawa, ya kuma sa dukan waɗanda suke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. Muddin ransa, ba su fasa bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.2 Tarihi 35:1-271. Yosiya ya yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji a Urushalima, aka kuma yanka ɗan ragon Bikin Ƙetarewa a ranar goma sha huɗu ga wata na farko.2. Ya zaɓi firistoci su yi aikinsu, sai ya ƙarfafa su su yi aikin da kyau a hidimar haikalin Ubangiji.3. Ya ce wa Lawiyawa waɗanda suke koyar da dukan Isra’ila da kuma waɗanda aka tsarkake wa Ubangiji. “Ku sa akwatin alkawari mai tsarki a cikin haikalin da Solomon ɗan Dawuda sarkin Isra’ila ya gina. Ba za a riƙa ɗaukansa a kafaɗa ba. Yanzu ku bauta wa Ubangiji Allahnku da kuma mutanensa Isra’ila.4. Ku shirya kanku iyali-iyali a sassanku, bisa ga umarnan da Dawuda sarkin Isra’ila da kuma ɗansa Solomon suka rubuta.5. “Ku tsaya a tsattsarkan wuri, bisa ga ƙungiyoyin gidajen kakannin ’yan’uwanku, waɗanda su ba firistoci ba ne. Kowanne ya sami kashi daga cikin gidan Lawiyawa.6. Ku yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, ku tsarkake kanku, ku kuma shirya raguna domin ’yan’uwanku, kuna yin abin da Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.”7. Yosiya ya tanada wa dukan mutanen da ba firistoci ba ne waɗanda suke a wurin, tumaki da awaki dubu talatin don a yanka saboda hadayun Bikin Ƙetarewa, ya kuma ba su shanu dubu uku. Dukan dabbobin kuwa daga garken sarki ne.8. Fadawansa su ma suka ba da taimako da yardar rai ga mutane da kuma firistoci da Lawiyawa. Hilkiya, Zakariya da Yehiyel masu aiki a haikalin Allah, suka ba firistoci hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyu da ɗari shida da kuma shanu ɗari uku.9. Haka kuma Konaniya tare da Shemahiya da Netanel, ɗan’uwansa, da Hashabiya, Yehiyel da Yozabad, shugabannin Lawiyawa, suka tanadar da hadayun Bikin Ƙetarewa dubu biyar da kuma bijimai ɗari biyar domin Lawiyawa.10. Sa’ad da aka shirya kome don Bikin Ƙetarewar, sai Firistoci tare da Lawiyawa suka tsaya wurin tsayawarsu bisa ga umarnin sarki.11. Aka yanka ragunan Bikin Ƙetarewa, firistoci kuma suka yayyafa jinin da aka ba su, yayinda Lawiyawa suna fiɗan dabbobi.12. Suka keɓe hadayun ƙonawa don su ba da su ga ƙungiyoyin iyalan mutane don su miƙa ga Ubangiji, yadda yake a rubuce a Littafin Musa. Suka yi haka da shanun.13. Suka gasa dabbobin Bikin Ƙetarewa a bisa wuta yadda aka tsara, suka dafa hadayu masu tsarki a tukwane, da manyan tukwane, da kuma kwanoni, suka raba su nan da nan ga dukan mutane.14. Bayan wannan, suka shirya wa kansu da kuma wa firistoci, saboda firistoci, zuriyar Haruna, suna miƙa hadayun ƙonawa da sashen kitse daga safe har dare. Saboda haka Lawiyawa suka shirya wa kansu da kuma wa firistocin daga zuriyar Haruna.15. Mawaƙa zuriyar Asaf, suna a wuraren da Dawuda, Asaf, Heman da Yedutun mai duba na sarki suka tsara. Bai zama lalle matsaran ƙofofi a kowace ƙofa su bar wuraren aikinsu ba, domin ’yan’uwansu Lawiyawa sun yi shiri dominsu.16. Ta haka fa aka yi dukan hidimar Ubangiji a wannan rana, domin su kiyaye Bikin Ƙetarewa, domin kuma su miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji, yadda sarki Yosiya ya umarta.17. Isra’ilawan da suka kasance a can suka yi Bikin Ƙetarewa a wannan rana, suka kuma kiyaye Bikin Burodi Marar Yisti kwana bakwai.18. Ba a taɓa yin Bikin Ƙetarewa haka ba tun zamanin annabi Sama’ila; kuma babu sarkin Isra’ilan da ya taɓa yin irin Bikin Ƙetarewa kamar yadda Yosiya ya yi, tare da firistoci, Lawiyawa da kuma dukan Yahuda da Isra’ila, waɗanda suke can tare da mutanen Urushalima.19. An yi wannan Bikin Ƙetarewa a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yosiya.20. Bayan wannan duka, sa’ad da Yosiya ya shirya haikali, Neko sarkin Masar ya haura don yă yi yaƙi a Karkemish a Yuferites, sai Yosiya ya fita don yă fafata da shi a yaƙi.21. Amma Neko ya aiki ’yan saƙo ga Yosiya, yana cewa, “Me ya gama ni da kai, ya Sarkin Yahuda? Ban zo in yi yaƙi da kai ba. Na zo ne in yi yaƙi da gidan da yake gāba da ni! Ka ƙyale ni! Allah ne ya riga ya faɗa mini in hanzarta. Kada ka yi gāba da Allah, wanda yake tare da ni, don kada yă hallaka ka.”22. Yosiya fa, bai juya daga gare shi ba, amma ya ɓad da kama don yă yi yaƙin. Bai saurari abin da Neko ya faɗa bisa ga umarnin Allah ba, amma ya tafi ya yaƙe shi a filin Megiddo.23. Maharba suka harbi Yosiya, sai ya ce wa hafsoshinsa, “Ku ɗauke ni ku fita da ni daga nan; gama an yi mini mummunan rauni.”24. Saboda haka suka ɗauke shi a keken yaƙin, suka fitar da shi, suka sa shi a wata keken yaƙin da yake da shi, suka kawo shi Urushalima, inda ya mutu. Aka binne shi a makabartar kakanninsa, sai dukan Yahuda da Urushalima suka yi makoki dominsa.25. Annabin Irmiya ya tsara waƙoƙin makoki domin Yosiya, wanda har wa yau mawaƙa maza da mata suke rera game da Yosiya. Suka sa waɗannan su zama al’ada a Isra’ila, suna kuma a rubuce cikin Littafin Makoki.26. Sauran ayyukan mulkin Yosiya da kuma kyawawan abubuwan da ya yi, bisa ga abin da aka rubuta a Dokar Ubangiji,27. dukan ayyukan, daga farko har zuwa ƙarshe, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda.2 Tarihi 36:1-231. Sai mutanen ƙasar suka ɗauki Yehoyahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki a Urushalima yă gāji mahaifinsa.2. Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku.3. Sarkin Masar ya tumɓuke shi a Urushalima, ya tilasta Yahuda su biya haraji talenti ɗari na azurfa da kuma talentin zinariya.4. Sarkin Masar ya naɗa Eliyakim, ɗan’uwan Yehoyahaz, sarki a bisa Yahuda da kuma Urushalima, ya kuma canja sunan Eliyakim zuwa Yehohiyakim. Amma Neko ya ɗauki Yehoyahaz ɗan’uwan Eliyakim ya kai Masar.5. Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.6. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya daure da sarƙoƙin tagulla, ya kuma kai shi Babilon.7. Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kuma kwaso kayayyaki daga haikalin Ubangiji ya sa su a haikalinsa a can.8. Sauran ayyukan mulkin Yehohiyakim, ayyukan banƙyamar da ya aikata da dukan abubuwan da aka same shi da su, suna a rubuce cikin littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. Sai Yehohiyacin ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki.9. Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.10. Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.11. Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya.12. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba.13. Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba.14. Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.15. Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.16. Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.17. Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar.18. Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon.19. Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can.20. Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na ’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa.21. Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.22. Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,23. “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘ Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”Zabura 86:1-51. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma.2. Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka.3. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini.4. Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina.5. Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.Karin Magana 21:13-1413. In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.14. Kyautar da aka yi a asirce takan kwantar da fushi, kuma cin hancin da aka rufe a cikin riga kan tā da fushi mai tsanani.Ayyukan Manzanni 21:13-1413. Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”14. Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.