Baibul a cikin shekara guda Yuli 21 Tarihi 28:1-211. Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.2. Sarki Dawuda ya miƙe tsaye ya ce, “Ku saurare ni, ’yan’uwana da kuma mutanena. Na yi niyya in gina gida a matsayin wurin hutu domin akwatin alkawarin Ubangiji, domin zatin Allahnmu, na kuma yi shiri don in gina shi.3. Amma Allah ya ce mini, ‘Ba za ka gina gida domin Sunana ba, saboda kai mayaƙi ne ka kuma zub da jini.’4. “Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila.5. Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.6. Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa.7. Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’8. “Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada.9. “Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.10. Ka lura fa, gama Ubangiji ya zaɓe ka don ka gina haikali a matsayin wuri mai tsarki. Ka yi ƙarfin hali ka kuma yi aiki.”11. Sa’an nan Dawuda ya ba ɗansa Solomon tsari domin shirayin haikalin, gine-ginensa, ɗakunan ajiyarsa, ɓangarorin bisansa, ɗakunan cikinsa da kuma wurin kafara.12. Ya ba shi tsarin dukan abin da Ruhu ya sa a zuciyarsa saboda filayen haikalin Ubangiji da ɗakunan kewaye, da ma’ajin haikalin Allah da kuma baitulmali na kayayyakin da aka keɓe.13. Ya ba shi tsari game ɓangarori na firistoci da Lawiyawa, da game dukan aikin hidima a cikin haikalin Ubangiji, da kuma game da dukan kayayyakin da za a yi amfani da su a hidima.14. Ya kimanta yawan zinariya don dukan kayayyakin zinariyar da za a yi amfani a kowane irin hidima, da yawan azurfa don dukan kayayyakin azurfan da za a yi amfani a kowace irin hidima.15. Da yawan zinariya don wurin ajiye fitilan fitilu da fitilunsu, da yawan zinariyan da za a yi amfani don kowace fitila da wurin ajiye fitilanta; da kuma yawan azurfa don kowane wurin ajiye fitila da fitilunsa bisa ga yadda za a yi amfani da kowane wurin ajiye fitila;16. yawan zinariya don kowane tebur saboda burodi mai tsaki; da kuma yawan azurfa saboda teburin azurfa;17. yawan zinariya zalla, don cokula masu yatsu, kwanonin yayyafawa ruwa da kuma tuluna; yawan zinariya don kowane kwanon zinariya; yawan azurfa don kowane kwanon azurfa;18. da kuma yawan tacecciyar zinariya don bagaden turare. Ya kuma ba shi tsari don keken yaƙi, wato, kerubobin zinariyar da suka miƙe fikafikansu suka inuwantar da akwatin alkawarin Ubangiji.19. Dawuda ya ce, “Dukan wannan, ina da shi a rubuce daga hannun Ubangiji zuwa gare ni, ya kuma ba ni ganewa cikin dukan tsarin fasalin, filla-filla.”20. Dawuda ya kuma ce wa Solomon ɗansa, “Ka yi ƙarfin hali, ka kuma yi aikin. Kada ka ji tsoro ko ka fid da zuciya, gama Ubangiji Allah, Allahna, yana tare da kai. Ba zai bari ka ji kunya ko yă yashe ka ba, sai an gama dukan aikin saboda hidimar haikalin Ubangiji.21. Sassan firistoci da na Lawiyawa suna a shirye domin dukan aiki a haikalin Allah, kuma kowane gwani mai niyya a kowace sana’a, zai taimake ka a cikin dukan aikin. Shugabanni da dukan mutane za su yi biyayya da kowane umarninka.”1 Tarihi 29:1-301. Sa’an nan Sarki Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ɗana Solomon, wanda Allah ya zaɓa, matashi ne, kuma bai gogu ba. Aikin yana da yawa, domin wannan ƙasaitaccen ginin ba na mutum ba ne, na Ubangiji Allah ne.2. Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.3. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,4. talenti dubu uku na zinariya (zinariyar Ofir) da tacecciyar azurfa dubu bakwai; don adon bangon gine-ginen,5. don aikin zinariya da kuma aikin azurfa, don kuma dukan aikin da gwanaye za su yi. Yanzu fa wa yake da niyya yă miƙa kansa a yau don Ubangiji?”6. Sai shugabannin iyalai, shugabannin kabilan Isra’ila, manyan hafsoshin mayaƙa dubu-dubu da manyan hafsoshi mayaƙa ɗari-ɗari, da shugabannin lura da ayyukan sarki suka yi bayarwa da yardar rai.7. Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah.8. Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji.9. Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.10. Dawuda ya yabi Ubangiji a gaban dukan taron, yana cewa, “Yabo gare ka, ya Ubangiji, Allah na mahaifinmu Isra’ila, har abada abadin.11. Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.12. Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.13. Yanzu fa, Allahnmu, muna gode maka, muna kuma yabon ɗaukakar sunanka.14. “Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.15. Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.16. Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.17. Na sani, Allahna, cewa kakan gwada zuciya, kakan kuma gamsu da mutunci. Dukan waɗannan abubuwa na bayar da yardar rai da kuma kyakkyawar niyya. Yanzu kuma da farin ciki na ga yadda mutanenka waɗanda suke a nan da yardar rai suka ba ka.18. Ya Ubangiji Allah na kakanninmu Ibrahim, Ishaku da Isra’ila, ka sa wannan sha’awa a cikin zukatan mutanenka har abada, ka kuma bar zukatansu su yi maka biyayya.19. Ka kuma ba ɗana Solomon cikakkiyar zuciya don yă kiyaye umarnanka, farillanka da ƙa’idodinka yă kuma yi kome don yă gina ƙasaitaccen gini wanda na riga na yi tanadi dominsa.”20. Sa’an nan Dawuda ya ce wa dukan taron, “Ku yabi Ubangiji Allahnku.” Saboda haka suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu; suka rusuna suka kuma fāɗi rubda ciki a gaban Ubangiji da kuma sarki.21. Kashegari suka miƙa hadayu ga Ubangiji suka kuma miƙa hadayu bijimai dubu, raguna dubu da kuma ’yan raguna dubu na ƙonawa gare shi, tare da hadayunsu na sha da sauran hadayu a yalwace saboda dukan Isra’ila.22. Suka ci suka sha da farin ciki mai girma a gaban Ubangiji a wannan rana. Sa’an nan suka yarda da Solomon ɗan Dawuda a matsayin sarki sau na biyu, suka shafe shi a gaban Ubangiji don yă zama mai mulki, Zadok kuwa ya zama firist.23. Saboda haka Solomon ya zauna a kujerar sarautar Ubangiji a matsayin sarki a maimakon mahaifinsa Dawuda. Ya yi nasara, dukan Isra’ila kuwa suka yi masa biyayya.24. Dukan shugabanni da jarumawa, har ma da dukan ’ya’yan Sarki Dawuda maza, suka yi alkawari za su yi wa Sarki Solomon biyayya.25. Ubangiji ya ɗaukaka Solomon sosai a idon dukan Isra’ila, ya kuma ba shi darajar sarauta yadda babu sarki a Isra’ilan da ya taɓa samu.26. Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila.27. Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima.28. Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.29. Game da ayyukan mulkin Sarki Dawuda, daga farko har ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin Sama’ila mai duba, tarihin annabi Natan da kuma tarihin Gad mai duba,30. tare da yadda mulkinsa da ikonsa da yanayin da suka kewaye shi da Isra’ila da kuma dukan masarautai na dukan sauran ƙasashe.Zabura 78:67-7267. Sa’an nan ya ƙi tentunan Yusuf, bai zaɓi kabilar Efraim ba;68. amma ya zaɓi kabilar Yahuda, Dutsen Sihiyona, wanda ya ƙaunaci.69. Ya gina wurinsa mai tsarki kamar bisa, kamar duniyar da ya kafa har abada.70. Ya zaɓi Dawuda bawansa ya kuma ɗauke shi daga ɗakin tumaki;71. daga kiwon tumaki ya kawo shi don yă kuma zama makiyayin mutanensa Yaƙub, na Isra’ila gādonsa.72. Dawuda kuwa ya zama makiyayinsu da mutuncin zuciya; da hannuwa masu gwaninta ya bi da su.Karin Magana 20:6-76. Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne, amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.7. Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi; masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.Ayyukan Manzanni 10:24-2824. Kashegari sai ya iso Kaisariya. Korneliyus kuwa yana nan yana jiransu, ya kuma gayyaci ’yan’uwansa da abokansa na kusa.25. Da Bitrus ya shiga gidan, Korneliyus ya sadu da shi ya kuma fāɗi a gabansa cikin bangirma.26. Amma Bitrus ya sa shi ya tashi. Ya ce, “Tashi, ni mutum ne kawai.”27. Yana magana da shi, sai Bitrus ya shiga ciki ya kuma tarar da taron mutane da yawa.28. Sai ya ce musu, “Ku da kanku kun san cewa dokarmu ta hana mutumin Yahuda yin cuɗanya, ko ya ziyarci Ba’al’umme. Amma Allah ya nuna mini cewa kada in kira wani mutum marar tsarki ko marar tsabta. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.