Baibul a cikin shekara guda Yuli 24Ezra 9:1-151. Bayan an yi waɗannan abubuwa duka, sai shugabanni suka zo wurina suka ce, “Mutanen Isra’ila, har da firistoci da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga maƙwabtansu ba, ba su kuma keɓe kansu daga irin rayuwar ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato, rayuwar irinta Kan’aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa da Amoriyawa.2. Sun auro wa kansu da ’ya’yansu ’yan mata mutanen nan, ta haka aka kwaɓa zuriyar da aka tsarkake da ta mutanen nan da suke tare da su. Shugabanni da manyan ma’aikata su ne a gaba-gaba a aikata wannan abin kunya.”3. Sa’ad da na ji wannan, sai na yaga rigata da alkyabbata, na tsittsige gashin kaina da na gemuna, na zauna, na rasa abin da yake mini daɗi.4. Sai duk waɗanda suke tsoron maganar Allah na Isra’ila suka kewaye ni don su ji wannan rashin imani wanda waɗanda suka dawo bauta suka yi. Na kuwa zauna a can a rikice, har lokacin miƙa hadaya na yamma.5. Sa’an nan a lokacin miƙa hadaya na yamma, na tashi da ɓacin raina, da yagaggun kayana, na durƙusa na miƙa hannuwana sama ga Ubangiji Allahna6. na kuma yi addu’a, na ce, “Ya Allah, ina cike da kunya, ba zan iya ɗaga fuskata gare ka ba, ya Allahna, domin zunubanmu sun fi mu tsayi, tudunsu har ya kai sama.7. Tun daga zamanin kakanninmu har zuwa yanzu, zunubanmu suna da yawa. Domin zunubanmu, mu da sarakunanmu, da firistocinmu aka kama mu, aka wulaƙanta mu, muka zama bayi a hannun sarakuna waɗansu ƙasashe.8. “Amma a yanzu a wannan ɗan lokaci Ubangiji Allahnmu ya yi mana jinƙai, ya bar mana saura, ya kuma ba mu wuri a wurinsa mai tsarki, ya kuma ba mu ganin haske, ya ɗan rage mana nauyin bauta.9. Ko da yake mu bayi ne, Allahnmu bai yashe mu cikin daurin talala da muke ciki ba, ya sa sarakunan Farisa suka yi mana kirki. Ya ba mu sabuwar dama don mu sāke gina haikalin Allahnmu, mu kuma gyara katangar, ya kuma ba mu kāriya a Yahuda da Urushalima.10. “Amma yanzu, ya Allahnmu, me za mu ce game da wannan? Gama mun ƙi bin11. dokokin da ka bayar ta wurin annabawa lokacin da ka ce, ‘Ƙasar da za ku mallaka, ƙasa ce marar tsarki, mutanenta sun ɓata ta da ƙazamin hali, ƙazamin halinsu ya ɓata ko’ina.12. Saboda haka kada ku aurar musu da ’yan matanku, kada kuma ku auro wa ’ya’yanku maza ’yan matansu. Kada ku yi wata yarjejjeniya ta abokantaka da su. Idan kun yi biyayya za ku yi ƙarfi, ku kuma ci albarkar ƙasar, har ku bar wa ’ya’yanku gādo na har abada.’13. “Abubuwan nan sun faru da mu sakamakon mugayen ayyukanmu ne, amma duk da haka ya Allahnmu, ba ka ba mu horo bisa ga yawan zunubanmu ba, ka kuma bar mana saura.14. Za mu sāke ƙin yin biyayya da umarninka mu yi auratayya da mutanen nan da suke aikata waɗannan abubuwan banƙyama? Ba za ka yi fushi da mu, ka ƙone mu da fushinka har babu ɗan saura ba?15. Ya Ubangiji Allah na Isra’ila, kai mai adalci ne! Yau an bar mu da sauran da ya tsira. Ga mu nan a gabanka masu zunubi, gama ba wanda zai iya tsayawa a gabanka.”Ezra 10:1-441. Yayinda Ezra yake addu’a, yake kuma furta laifi, yana kuka, yana a durƙushe da kansa ƙasa a gaban gidan Allah, sai babban taron jama’ar Isra’ilawa, maza, mata da yara, suka taru a wurinsa. Su ma suka yi kuka mai zafi.2. Sai Shekaniya ɗan Yehiyel, daga zuriyar Elam ya ce wa Ezra, “Mun yi wa Allah rashin aminci ta wurin yin auratayya da maƙwabtanmu, amma duk da haka bai yashe mutanen Isra’ila ba.3. Yanzu bari mu yi alkawari da Allahnmu, mu kori matan da yaransu bisa ga abin da ranka yă daɗe da sauran shugabannin da kuke girmama umarnin Allah kuka shawarce mu, bari mu yi haka bisa ga doka.4. Sai ka tashi, gama wannan hakkinka ne, za mu ba ka goyon baya. Saboda haka ka yi ƙarfin hali ka aikata shi.”5. Sai Ezra ya tashi ya sa firistoci da suke shugabanni, da Lawiyawa, da dukan mutanen Isra’ila su rantse, cewa za su yi abin da aka ce. Sai suka yi rantsuwar.6. Sa’an nan Ezra ya tashi daga gidan Allah ya tafi gidan Yehohanan ɗan Eliyashib, a can ma bai ci wani abu ba, bai sha ruwa ba domin ya ci gaba da yin baƙin cikin rashin aminci na waɗanda suka dawo daga bauta.7. Aka yi shela a duk fāɗin Yahuda da Urushalima cewa dukan waɗanda suka dawo daga bauta su tattaru a Urushalima.8. Duk wanda bai zo a cikin kwana uku ba, za a washe shi, a kuma ware shi daga jama’ar da suka dawo daga bauta. Haka shugabanni da dattawa suka zartar.9. A cikin kwana uku duk mutanen Yahuda da na Benyamin suka taru a Urushalima. A ranar ashirin ga watan tara, dukan mutanen suka zauna a dandali a gaban gidan Allah cike da ɓacin rai saboda abin da ya faru da kuma ruwan da aka yi.10. Sai Ezra firist ya miƙe tsaye ya yi musu magana ya ce, “Kun yi rashin aminci; kun aure mata baƙi, ta haka kuka ƙara kan zunubin Isra’ila.11. Yanzu sai ku furta zunubanku ga Ubangiji, Allahn kakanninku, ku kuma yi nufinsa. Ku raba kanku da mutanen da suke kewaye da ku, ku kuma rabu da baƙin mata.”12. Mutanen kuwa suka tā da murya da ƙarfi suka ce, “Gaskiya ka faɗa, dole mu yi yadda ka ce,13. Amma akwai mutane da yawa, kuma lokacin damina ne; saboda haka ba za mu iya tsayawa a waje ba. Ban da haka ma, aikin nan ba na kwana ɗaya ko biyu ba ne, domin ba ƙaramin laifi muka yi ba.14. Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.”15. Yonatan ɗan Asahel, da Yazehiya ɗan Tikba su ne kaɗai ba su yarda da wannan shirin ba, sai Meshullam da Shabbetai Balawe kuma suka goyi bayansu.16. Sai waɗanda suka dawo daga bauta suka yi yadda aka zartar. Ezra firist ya zaɓi mutane waɗanda su ne shugabannin iyalai, ɗaya daga kowane sashe, aka rubuta sunan kowannensu. A ranar ɗaya ga watan goma kuwa suka zauna don su yi binciken waɗannan abubuwa.17. A rana ta farko ga watan farko, suka gama da bincike duk waɗanda suka auri baƙin mata.18. A cikin zuriyar firistoci, ga waɗanda suka auri mata baƙi. Daga zuriyar Yeshuwa ɗan Yozadak da ’yan’uwansa, akwai Ma’asehiya, da Eliyezer, da Yarib, da Gedaliya.19. (Su ne suka miƙa hannuwansu suka nuna sun yarda su kori matansu baƙi, kowannensu kuma ya ba da rago daga cikin garkensa don a miƙa hadaya don zunubi.)20. Daga zuriyar Immer, akwai Hanani da Zebadiya.21. Daga zuriyar Harim, akwai Ma’asehiya, Iliya, Shemahiya, Yehiyel da Uzziya.22. Daga zuriyar Fashhur, akwai Eliyohenai, Ma’asehiya, Ishmayel, Netanel, Yozabad da Eleyasa.23. Cikin Lawiyawa, akwai Yozabad, Shimeyi, Kelaya (wato, Kelita), Fetahahiya, Yahuda, Eliyezer.24. Daga mawaƙa, akwai Eliyashib. Daga masu tsaron ƙofofin haikali, akwai Shallum, Telem da Uri.25. Ga sunayen sauran mutanen Isra’ilan da suke da wannan laifi. Daga zuriyar Farosh, akwai Ramiya, da Izziya, Malkiya, Miyamin, Eleyazar, Malkiya da Benahiya.26. Daga zuriyar Elam, akwai Mattaniya, Zakariya, Yehiyel, Abdi, Yeremot, da Iliya.27. Daga iyalin Zattu, akwai Eliyohenai, Eliyashib, Mattaniya Yeremot da Zabad da Aziza.28. Daga zuriyar Bebai, akwai Yehohanan, Hananiya, Zabbai, da Atlai.29. Daga zuriyar Bani, akwai Meshullam, Malluk, Adahiya, Yashub, Sheyal, da Ramot.30. Daga zuriyar Fahat-Mowab, akwai Adna, Kelal, Benahiya, Ma’asehiya, Mattaniya, Bezalel, Binnuyi, da Manasse.31. Daga zuriyar Harim, akwai Eliyezer, Isshiya, Malkiya, Shemahiya, Simeyon,32. Benyamin, Malluk da Shemariya.33. Daga zuriyar Hashum, akwai Mattenai, da Mattatta, Zabad, Elifelet, Irmai, Manasse, da Shimeyi.34. Daga zuriyar Bani, akwai Ma’adai, Amram, Yuwel,35. Benahiya, Bedeya, Keluhi,36. Baniya, Meremot, Eliyashib,37. Mattaniya, Mattenai da Ya’asu.38. Daga zuriyar Binnuyi, akwai Shimeyi,39. Shelemiya, Natan, Adahiya,40. Maknadebai, Shashai, Sharai,41. Azarel, Shelemiya, da Shemariya,42. Shallum da Amariya da Yusuf.43. Daga zuriyar Nebo, akwai Yehiyel, Mattitiya, Zabad, Zebina, Yaddai, Yowel da Benahiya.44. Dukan waɗannan sun auri baƙin mata, waɗansunsu suna da ’ya’ya.Zabura 88:6-106. Ka sa ni a ramin da yake can ƙasa cikin zurfafa mafi duhu.7. Hasalarka tana da nauyi a kaina; ka turmushe ni da dukan raƙumanka.8. Ka ɗauke abokaina na kurkusa daga gare ni ka sa na zama abin ƙyama a gare su. An kange ni, ba yadda zan kuɓuta9. idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.10. Kakan nuna wa matattu ayyukanka na banmamaki ne? Waɗanda suka mutu sukan tashi su yabe ka ne?Karin Magana 21:23-2423. Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.24. Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.Ayyukan Manzanni 24:1-271. Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna.2. Sa’ad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa, “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa.3. Ko’ina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka.4. Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.5. “Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa6. har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.