Baibul a cikin shekara guda Yuli 25Nehemiya 1:1-111. Kalmomin Nehemiya ɗan Hakaliya. A cikin watan Kisleb a shekara ta ashirin, yayinda nake a fadar Shusha.2. Hanani, ɗaya daga cikin ’yan’uwana, ya zo daga Yahuda tare da waɗansu mutane. Na kuwa tambaye shi game da raguwar Yahudawan da suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta, da kuma game da Urushalima.3. Suka ce mini, “Waɗanda suka tsira daga kwasan zuwa zaman bauta da kuma suka komo cikin yankin suna cikin babban damuwa da wulaƙanci. An rushe katangar Urushalima aka kuma ƙone ƙofofin da wuta.”4. Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama.5. Na ce, “Ya Ubangiji Allah na sama, Allah mai girma da mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna da waɗanda suke ƙaunarsa, suke kuma yin biyayya da umarnansa,6. ka sa kunne ka kuma buɗe idanunka ka ji addu’ar da bawanka yake yi a gabanka dare da rana saboda bayinka, mutanen Isra’ila. Na furta zunuban da mu Isra’ilawa, har da ni da kuma gidan mahaifina muka yi maka.7. Mun yi mugunta gare ka. Ba mu yi biyayya da umarnai, ƙa’idodi da kuma dokokin da ka ba wa bawanka Musa ba.8. “Ka tuna da umarnan da ka ba wa bawanka Musa, kana cewa, ‘In kun yi rashin aminci, zan warwatsar da ku a cikin al’ummai,9. amma in kuka dawo gare ni kuka kuma yi biyayya da umarnaina, to, ko mutanenku da aka kwasa zuwa zaman bauta suna can wuri mafi nisa, zan tattara su daga can in kawo su wurin da na zaɓa yă zama wurin zama don Sunana.’10. “Su bayinka ne da kuma mutanenka da ka fansa ta wurin ƙarfinka mai girma da kuma hannunka mai iko.11. Ya Ubangiji, ka kasa kunne ga addu’ar wannan bawanka da kuma ga addu’ar bayinka waɗanda suke farin cikin girmama sunanka. Ka ba wa bawanka nasara a yau ta wurinsa yă sami tagomashi a gaban wannan mutum.” Ni ne mai riƙon kwaf sarki.Nehemiya 2:1-201. A watan Nisan a shekara ta ashirin ta mulkin Sarki Artazerzes, sa’ad aka kawo masa ruwan inabi, sai na karɓa na ba shi. Ban taɓa ɓata fuskata a gabansa ba, sai wannan karo.2. Saboda haka sarki ya tambaye ni ya ce, “Me ya sa fuskarka ta ɓaci, ga shi, ba ciwo kake ba? Ba abin da ya kawo wannan, in ba dai kana baƙin ciki ba.” Sai na ji tsoro ƙwarai,3. na amsa na ce wa sarki, “Ran sarki yă daɗe! Me zai hana fuskata ta ɓaci, sa’ad da birnin da aka binne kakannina tana zaman kango, aka kuma rushe ƙofofinsa da wuta?”4. Sai sarki ya ce mini, “Me kake so?” Sai na yi addu’a ga Allah na sama,5. na kuwa ba wa sarki amsa, na ce, “In ya gamshi sarki, in kuma bawanka ya sami tagomashi a idonka, bari ka aike ni in tafi ƙasar Yahuda, birnin da aka binne kakannina, domin in sāke gina shi.”6. Sai sarki, a lokacin sarauniya da tana zama kusa da shi, ya tambaye ni, ya ce, “Kwana nawa tafiyar za tă ɗauke ka, kuma yaushe za ka dawo?” Ya gamshi sarki ya aike ni; saboda haka na shirya lokaci.7. Na kuma ce masa, “In ya gamshi sarki, zai yi kyau in sami wasiƙu zuwa ga gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, domin su tanada kāriya har sai na isa Yahuda?8. A kuma ba ni wasiƙa zuwa ga Asaf, sarkin daji, yă ba ni katako don yin ƙofofin kagara na kusa da fadar haikali da kuma don katangar birni, da na wurin da zan zauna?” Sarki kuwa ya ba ni abin da na roƙa, gama Allah yana tare da ni.9. Saboda haka na tafi wurin gwamnonin Kewayen Kogin Yuferites, na ba su wasiƙun sarki. Sarki kuma ya aika da hafsoshin mayaƙa da kuma mahayan dawakai tare da ni.10. Da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon suka ji cewa wani ya zo domin yă ƙarfafa zaman lafiyar mutanen Isra’ila, sai suka damu ƙwarai.11. Sai na je Urushalima, bayan na zauna a can na kwanaki uku,12. sai na fita da dare tare da mutane kalila. Ban faɗa wa wani abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi don Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.13. Da dare na fita ta Ƙofar Kwari wajen Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, ina dudduba katangar Urushalima waɗanda aka rushe da kuma ƙofofinta waɗanda aka ƙone da wuta.14. Sa’an nan na ci gaba zuwa wajen Ƙofar Maɓuɓɓuga da kuma Tafkin Sarki, amma babu isashen wuri saboda abin da na hau yă bi;15. saboda haka na haura ta kwarin da dad dare, ina dudduba katangar. A ƙarshe, na juya na sāke shiga ta Ƙofar Kwari.16. Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da nake yi ba, domin ban riga na faɗa wa Yahudawa, ko firistoci, ko manyan gari, ko shugabanni, ko sauran waɗanda za su yi aiki, kome ba.17. Sai na ce musu, “Kun ga matsalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta da wuta. Ku zo mu sāke gina katangar Urushalima, ba za mu ƙara shan kunya ba.”18. Na kuma faɗa musu game da yadda alherin Allahna yake tare da ni da kuma abin da sarki ya faɗa mini. Suka amsa, suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Sai suka fara wannan aiki mai kyau.19. Amma sa’ad da Sanballat mutumin Horon da Tobiya wakilin ƙasar Ammon da kuma Geshem mutumin Arab suka ji game da wannan, sai suka yi mana ba’a suka kuma yi mana dariya. Suka ce, “Me kuke tsammani kuke yi? Kuna so ku yi wa sarki tawaye ne?”20. Na amsa musu na ce, “Allah na sama zai ba mu nasara. Mu bayinsa za mu tashi mu fara gini, amma game da ku kam, ba ku da rabo cikin Urushalima, ba ku da wani hakki ko wani abin tunawa.”Zabura 88:11-1811. Ana furta ƙaunar a cikin kabari ne, ana zancen amincinka a cikin Hallaka ne?12. An san ayyukanka masu banmamaki a wurin duhu ne, ko ayyukan adalcinka a lahira?13. Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.14. Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?15. Tun ina ƙarami na sha wahala na kuma yi kusa in mutu; na sha wahalar razanarka kuma na kuma fid da zuciya.16. Hasalarka ta sha kaina; razanarka ta hallaka ni.17. Dukan yini sun kewaye ni kamar rigyawa; sun mamaye ni ɗungum.18. Ka ɗauke abokaina da ƙaunatattuna daga gare ni; duhu ne abokina na kurkusa.Karin Magana 21:25-2625. Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.26. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.Ayyukan Manzanni 25:1-271. Kwana uku bayan isowa a lardin, sai Festus ya haura daga Kaisariya zuwa Urushalima,2. inda manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka bayyana a gabansa suka kuma gabatar da ƙararsu a kan Bulus.3. Suka roƙi Festus a gaggauce a matsayin alfarma gare su, da yă sa a mai da Bulus Urushalima, gama sun ’yan kwanto su kashe shi a hanya.4. Festus ya amsa ya ce, “Bulus yana tsare a Kaisariya, ni da kaina kuma zan je can ba da daɗewa ba.5. Ku sa waɗansu daga cikin shugabanninku su tafi tare da ni su kawo ƙararsu a kan mutumin a can, in ya aikata wani laifi.”6. Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa.7. Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba.8. Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.”9. Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?”10. Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai.11. In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!”12. Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!”13. Bayan ’yan kwanaki sai Sarki Agiriffa da Bernis suka iso Kaisariya don su yi wa Festus gaisuwar bangirma.14. Da yake za su yi kwanaki da dama a can, sai Festus ya tattauna batun Bulus da sarki. Ya ce, “Akwai mutumin da Felis ya bari a daure.15. Sa’ad da na je Urushalima, manyan firistoci da dattawan Yahudawa suka kawo ƙara game da shi suka kuma nema a hukunta shi.16. “Na gaya musu cewa ba al’adar Romawa ba ce a hukunta mutum kafin ya fuskanci masu ƙararsa ya kuma sami damar kāre kansa game da ƙararsu.17. Da suka zo nan tare da ni, ban yi wani jinkiri ba, na kira zaman kotu kashegari kuma na umarta a kawo mutumin.18. Sa’ad da masu zarginsa suka tashi tsaye don su yi magana, ba su zarge shi da wani laifin da na yi tsammani ba.19. A maimako haka, sai suka kawo waɗansu ’yan maganganu game da addininsu da ba su yarda da shi ba da kuma game da wani Yesu da ya mutu wanda Bulus ya ce yana da rai.20. Na rasa yadda zan bincike irin abubuwan nan; saboda haka na yi tambaya ko zai yarda ya tafi Urushalima a yi masa shari’a a can game da waɗannan zargi.21. Da Bulus ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Babban Sarki sai na umarta a tsare shi har kafin in aika shi zuwa ga Kaisar.”22. Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Ni ma zan so in saurari mutumin da kaina.” Sai ya amsa ya ce, “Za ka kuwa ji shi gobe.”23. Kashegari Agiriffa da Bernis suka yi shiga irin ta sarauta suka shiga ɗakin jama’a tare da manyan sojoji da manyan mutanen birni. Da umarnin Festus, sai aka shigo da Bulus.24. Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da kuma dukan waɗanda suke tare da mu, kun ga wannan mutum! Dukan jama’ar Yahudawa sun kawo mini kararsa a Urushalima da kuma a nan Kaisariya, suna kururuwa suna cewa bai kamata a bar shi da rai ba.25. Ban same shi da wani laifin da ya isa kisa ba, amma saboda ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Babban Sarki sai na yanke shawara in aika da shi Roma.26. Ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa Mai Girma game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman a gabanka, Sarki Agiriffa, saboda a sakamakon wannan bincike zan iya samun abin da zan rubuta.27. Don a ganina wauta ce a aika da ɗan kurkuku ba tare da an nuna zargin da ake yi a kansa ba.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.