Baibul a cikin shekara guda Yuli 26Nehemiya 3:1-311. Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.2. Mutanen Yeriko kuwa suka kama ginin daga mahaɗin, Zakkur ɗan Imri kuma ya fara ginin biye da su.3. ’Ya’yan Hassenaya ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka kafa ginshiƙan, suka kuma sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu.4. Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare.5. Mutanen Tekowa ne suka yi gyare-gyare biye da shi, amma manyan garinsu suka ƙi su sa hannu cikin aikin da shugabanninsu suka bayar.6. Yohiyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodehiya ne suka gyara Ƙofar Yeshana. Suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.7. Biye da su, mutanen Gibeyon da Mizfa Melatiya na Gibeyon da Yadon Meronot waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnan Kewayen Kogin Yuferites ne suka yi gyare-gyaren.8. Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi.9. Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye.10. Kusa da Refahiya, Yedahiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyaren daga gaban gidansa, sai Hattush ɗan Hashabnehiya ya yi gyare-gyaren biye da shi.11. Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-Mowab ya yi gyare-gyaren wani sashe da kuma Hasumiyar Wurin Gashi.12. Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon ’ya’yansa mata.13. Hanun da mazaunan Zanowa ne suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sāke gina ta suka sa ƙofofinta, da sakatunta, da sandunan ƙarfenta a wurarensu. Suka kuma gyara yadi ɗari biyar na katangar har zuwa Ƙofar Juji.14. Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu.15. Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.16. Gaba da shi, Nehemiya ɗan Azbuk, mai mulkin rabin yankin Bet-Zur ne ya yi gyare-gyaren har zuwa kusa da kaburburan Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da kuma Gidan Jarumawa.17. Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa.18. Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren.19. Biye da su, Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya yi gyara wani sashe, daga inda yake fuskantar hawan gidan makamai har zuwa kusurwa.20. Biye da shi, Baruk ɗan Zakkai da ƙwazo ya gyara wani sashe, daga kusurwa zuwa mashigin gidan Eliyashib babban firist.21. Biye da shi, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya yi gyaran wani sashe, daga mashigin gidan Eliyashib zuwa ƙarshensa.22. Firistoci daga kewayen yankin ne suka yi gyare-gyaren biye da shi.23. Can gaba da su, Benyamin da Hasshub ne suka yi gyare-gyaren a gaban gidansu, biye da su kuwa, Azariya ɗan Ma’asehiya, ɗan Ananiya ne ya yi gyare-gyaren kusa da gidansa.24. Biye da shi, Binnuyi ɗan Henadad ya yi gyaran wani sashe, daga gidan Azariya zuwa kusurwa,25. sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh26. da masu hidimar haikali da suke zama a tudun Ofel ne suka yi gyare-gyaren har zuwa wani wuri ɗaura da Ƙofar Ruwa wajen gabas da kuma doguwar hasumiya.27. Biye da su, mutanen Tekowa suka yi gyaran wani sashe, daga babbar doguwar hasumiya zuwa katangar Ofel.28. Daga Ƙofar Doki, firistoci ne suka yi gyare-gyaren, kowanne a gaban gidansa.29. Biye da su, Zadok ɗan Immer ya yi gyare-gyaren ɗaura da gidansa. Biye da shi, Shemahiya ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare.30. Biye da shi, Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashe. Biye da su, Meshullam ɗan Berekiya ya yi gyare-gyaren ɗaura da wurin zamansa.31. Biye da shi, Malkiya, ɗaya daga cikin masu ƙera zinariya ya yi gyare-gyaren har zuwa gidan masu hidimar haikali da kuma ’yan kasuwa, ɗaura da Ƙofar Bincike, har zuwa ɗakin da yake bisa kusurwar.Nehemiya 4:1-231. Da Sanballat ya ji cewa muna sāke ginin katangar, sai ya husata, ya haukace ƙwarai. Ya yi wa Yahudawa dariya,2. a gaban abokansa da kuma sojojin Samariya ya ce, “Me waɗancan Yahudawan nan marasa ƙarfi suke yi? Za su maido da katangarsu ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama a rana ɗaya? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?”3. Tobiya wakilin mutanen Ammon wanda yake a gefensa ya ce, “Abin nan da suke gini, ko dila ma ya hau, zai rushe shi!”4. Ka ji mu, ya Allahnmu, gama an rena mu. Bari zagin da suke yi mana yă koma kansu. Ka sa a kwashe su a kai su bauta a wata ƙasa.5. Kada ka rufe laifinsu, kada kuwa ka gafarta musu, gama sun ci mutuncinmu, mu da muke gini.6. Sai muka sāke ginin katangar sai da duka ta kai rabin tsayinta, gama mutane sun yi aiki da dukan ƙarfinsu.7. Amma da Sanballat, da Tobiya, da Larabawa, da Ammonawa, da kuma mutanen Ashdod suka ji cewa gyare-gyaren katangar Urushalima yana cin gaba, ana kuma tattoshe wuraren da suka tsattsaga, sai suka husata ƙwarai.8. Dukansu suka ƙulla su zo, su yi yaƙi da Urushalima, su tā da hankali a cikinta.9. Amma muka yi addu’a ga Allahnmu muka kuma sa masu tsaro da rana da kuma dare don mu magance wannan barazana.10. Ana cikin haka, mutane a Yahuda suka ce, “Ƙarfin ma’aikata yana kāsawa, akwai kuma sauran tarkace da yawa da ba za mu iya sāke gina katangar ba.”11. Abokan gābanmu sun ce, “Ba za su sani ba, ba kuwa za su gan mu ba, sai dai kawai su gan mu a cikinsu, za mu karkashe su, mu tsai da aikin.”12. Sau da yawa Yahudawan da suke da zama kusa da abokan gābanmu sun yi ta zuwa suna yin mana magana, suna cewa “Ko’ina muka juya, za su fāɗa mana.”13. Saboda haka na sa jama’a su ja ɗamara bisa ga iyalinsu a bayan katanga, a wuraren da ba a gina ba. Suna riƙe da takuba, da māsu, da bakkuna.14. Bayan na dudduba abubuwa, sai na miƙe tsaye na ce wa manyan gari da shugabanni da kuma sauran jama’a, “Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda yake mai girma da banrazana, ku yi yaƙi don ’yan’uwanku, da ’ya’yanku maza da mata, da matanku da kuma gidajenku.”15. Da abokan gābanmu suka ji muna sane da shirinsu, Allah kuma ya wargaje shirin nan, sai duk muka dawo ga katangar, kowa ya kama aikinsa.16. Daga wannan rana zuwa gaba, rabin mutane suka yi aiki, yayinda sauran rabin suka kintsa da māsu, da garkuwa, da bakkuna da makamai. Shugabanni suka goyi bayan dukan mutanen Yahuda17. waɗanda suke ginin katanga. Waɗanda suke ɗaukan kaya suka yi aikinsu da hannu ɗaya, suna kuma riƙe da makami a ɗaya hannun,18. kuma kowane mai gini ya ɗaura takobinsa a gefe yayinda yake aiki. Amma mutum mai busa ƙaho ya kasance tare da ni.19. Sai na ce wa manyan gari, da shugabanni, da sauran jama’a, “Aikin nan babba ne kuma mai yawa, ga shi muna a rarrabe nesa da juna a katangar.20. Duk inda kuka ji an busa ƙaho, sai ku taru a wurin. Allahnmu zai yi yaƙi dominmu!”21. Saboda haka muka ci gaba da aiki, rabin mutane suna riƙe da māsu, daga wayewar gari har zuwa fitowar taurari.22. A wannan lokaci na kuma ce wa mutane, “A sa kowane mutum da mataimakinsa su zauna a Urushalima da dare, domin a yi tsaro da dare, da safe kuma a kama aiki.”23. Saboda haka ni, da ’yan’uwana, da bayina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa; kowa ya rataye makaminsa, ko ya je shan ruwa ma.Nehemiya 5:1-191. To, sai maza da matansu suka tā da fara gunaguni mai tsanani a kan ’yan’uwansu Yahudawa.2. Waɗansu suka ce, “Mu da ’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.”3. Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.”4. Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.5. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”6. Sa’ad da na ji kukansu da waɗannan koke-koke, na husata ƙwarai.7. Na yi tunaninsu a zuciyata sa’an nan na zargi manyan gari da shugabanni. Na ce musu, “Kuna musguna wa ’yan’uwanku ta wurin ba su rance da ruwa!” Saboda haka na kira babban taro gaba ɗaya don a magance wannan.8. Na ce, “Da dukan iyakar ƙoƙarinmu, mun fanshi ’yan’uwanmu Yahudawan da aka sayar wa Al’ummai. Amma ga shi kuna sayar da ’yan’uwanku ga Al’ummai, don kawai a sāke sayar mana da su!”9. Saboda haka na ci gaba na ce, “Abin da kuke yi a yanzu ba daidai ba ne. Bai kamata ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu don mu guji ba’ar Al’ummai abokan gābanmu ba?10. Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa!11. Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”12. Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari.13. Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari.14. Ban da haka ma, daga shekara ta ashirin ta Sarki Artazerzes, sa’ad da aka naɗa ni in zama gwamnansu a ƙasar Yahuda, har zuwa shekara ta talatin da biyu na mulkinsa, shekara sha biyu ke nan, ko ni, ko ’yan’uwana, ba wanda ya ci abincin da akan ba wa gwamna.15. Amma gwamnonin farko, waɗanda suka riga ni, sun ɗaura wa mutane kaya mai nauyi suka karɓi shekel arba’in na azurfa daga gare su haɗe da abinci da kuma ruwan inabi. Har bayin masu mulki ma sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.16. A maimakon haka, na miƙa kaina ga aiki a kan wannan katanga. Na tattara dukan mutanena a can don aikin; ba mu samar wa kanmu wata gona ba.17. Bugu da ƙari, Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin suna ci daga teburina, haka ma waɗanda suka zo wurinmu daga ƙasashen da suke kewaye.18. Kowace rana akan shirya mini saniya ɗaya, zaɓaɓɓun tumaki shida da waɗansu kaji, kuma kowace kwana goma akan tanadar da ruwan inabi na kowane iri a yalwace. Duk da haka, ban taɓa nemi a ba ni abincin da akan ba wa gwamna ba, domin wahala ta yi wa jama’a yawa.19. Ka tuna da ni, ka yi mini alheri, ya Allah, saboda dukan abubuwan da na yi saboda waɗannan mutane.Zabura 89:1-41. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.2. Zan furta cewa ƙaunarka tana nan daram har abada, cewa ka kafa amincinka a sama kanta.3. Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,4. cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ”Karin Magana 21:21-2721. Duk wanda ya nemi adalci da ƙauna kan sami rai, wadata da girmamawa.22. Mutum mai hikima kan fāɗa wa birnin jarumawa ya kuma rushe katangar da suka dogara a kai.23. Duk wanda yake lura da bakinsa da kuma harshensa kan kiyaye kansa daga masifa.24. Mai girmankai da kuma mai fariya, “Mai ba’a” ne sunansa; yana yin abubuwa da girmankai ainun.25. Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki.26. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.27. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!Ayyukan Manzanni 26:1-321. Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “An ba ka izini ka yi magana.” Saboda haka Bulus ya yi alama da hannunsa ya fara kāriyarsa.2. Ya ce, “Sarki Agiriffa, na yi sa’a da na tsaya a gabanka yau yayinda nake kāriyata game da dukan zargin Yahudawa,3. musamman ma domin ka saba sosai da dukan al’adun Yahudawa da kuma maganganunsu. Saboda haka ina roƙonka ka saurare ni da haƙuri.4. “Yahudawa duk sun san yadda na yi rayuwa tun ina yaro, daga farkon rayuwata a ƙasarmu da kuma a Urushalima.5. Sun san ni tun da daɗewa za su kuwa shaida, in suna so, cewa bisa ga ɗarikar addininmu mafi tsanani, na yi rayuwar Bafarisiye ne.6. Yanzu kuwa saboda begena cikin abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari ne, ake mini shari’a yau.7. Wannan shi ne alkawarin da kabilanmu goma sha biyu suke bege su ga cikawarsa, yayinda suke bauta wa Allah da himma dare da rana. Ya Sarki, saboda wannan bege ne fa Yahudawa suke zargena.8. Don me wani a cikinku zai yi shakka cewa Allah yana tā da matattu?9. “Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare.10. Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su.11. Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.12. “A cikin irin tafiye-tafiyen nan ne ina kan hanya zuwa Damaskus tare da izini daga manyan firistoci.13. Da tsakar rana, ya sarki, sa’ad da nake kan hanya, sai na ga wani haske daga sama, fiye da hasken rana, yana haskakawa kewaye da ni da abokan tafiyata.14. Dukanmu muka fāɗi ƙasa, na kuwa ji wata murya tana ce mini da harshen Arameyik, ‘Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini? Yana da wuya ka shuri tsinken tsokanar dabba.’15. “Sai na yi tambaya na ce, ‘Wane ne kai, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.16. Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.17. Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin18. ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’19. “Saboda haka fa, Sarki Agiriffa, ban yi rashin biyayya ga wahayin nan daga sama ba.20. Da farko ga waɗanda suke a Damaskus, sa’an nan ga waɗanda suke a Urushalima da kuma cikin dukan Yahudiya, da kuma ga Al’ummai su ma, na yi wa’azi don su tuba su juyo ga Allah su kuma tabbatar da tubansu ta wurin ayyukansu.21. Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni.22. Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru,23. cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.”24. A nan ne fa Festus ya tsai da kāriyar Bulus. Ya yi ihu ya ce, “Bulus! Kai dai ruɗaɗɗe ne, yawan karatunka yana juya maka kai.”25. Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau.26. Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba.27. Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.”28. Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?”29. Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”30. Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su.31. Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.”32. Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.