Baibul a cikin shekara guda Yuli 28Nehemiya 8:1-181. sai dukan mutane suka taru kamar mutum guda a dandali a gaban Ƙofar Ruwa. Suka faɗa wa Ezra malamin Doka yă fitar da Littafin Dokar Musa, wanda Ubangiji ya umarta domin Isra’ila.2. Saboda haka a rana ta farko ga watan bakwai, Ezra firist, ya kawo Doka a gaban taro, wanda ya ƙunshi maza da mata da dukan waɗanda za su iya fahimta.3. Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.4. Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya.5. Sai Ezra ya buɗe littafin. Dukan mutane kuwa suka gan shi domin yana tsaye a bisa fiye da inda mutane suke tsaye; yayinda ya buɗe littafin kuwa, dukan mutane suka miƙe tsaye.6. Ezra ya yabi Ubangiji, Allah mai girma; dukan mutane kuwa suka tā da hannuwansu suka amsa, “Amin! Amin!” Sa’an nan suka sunkuya suka yi wa Ubangiji sujada da fuskokinsu har ƙasa.7. Lawiyawa, wato, su Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma’asehiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan da Felahiya, suka koyar da mutane a cikin Dokar yayinda mutane suke a tsaye a can.8. Suka karanta daga Littafin Dokar Allah, suna sa kowa ya gane, suna kuma ba da fassarar domin mutane su fahimci abin da ake karatu.9. Sa’an nan Nehemiya gwamna, Ezra firist da kuma wanda yake malamin Doka, da Lawiyawa waɗanda suke koyar da mutane, suka ce musu duka, “Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangiji Allahnku. Kada ku yi makoki ko kuka.” Gama dukan mutane suna ta kuka yayinda suke sauraran kalmomin Dokar.10. Nehemiya ya ce, “Ku koma gidajenku ku ci abinci mai kyau, ku sha abin sha mai zaƙi, ku kuma aika wa wanda ba shi da shi. Wannan rana mai tsarki ce ga Ubangijinmu. Kada ku yi baƙin ciki, gama farin cikin Ubangiji shi ne ƙarfinku.”11. Lawiyawa suka rarrashi mutane duka suna cewa, “Ku natsu, gama wannan rana ce mai tsarki. Kada ku yi baƙin ciki.”12. Sa’an nan dukan mutane suka koma gidajensu suka ci, suka sha, suka aika wa wanda ba shi da abinci, gama yanzu sun fahimci kalmomin da aka karanta musu.13. A rana ta biyu ga wata, shugabannin iyalai, tare da firistoci da Lawiyawa, suka taru kewaye da Ezra malamin Doka don su mai da hankali ga kalmomin Dokar.14. Suka tarar a rubuce a cikin Doka wadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa, cewa Isra’ilawa su zauna a bukkoki a lokaci bikin watan bakwai15. kuma cewa ya kamata su yi shelar wannan magana, su kuma yaɗa ta a duk garuruwansu da kuma cikin Urushalima cewa, “Ku fita zuwa cikin ƙasar tudu ku kawo rassa daga itatuwan zaitun da na zaitun jeji, da kuma daga dargaza, da dabino da itatuwa masu ganye, don yin bukkoki”, kamar yadda yake a rubuce.16. Sai mutanen suka fita suka dawo da rassa suka kuma yi wa kansu bukkoki a bisa rufin ɗakunansu, a cikin filaye, a shirayin gidan Allah, da ciki dandalin da yake kusa da Ƙofar Ruwa, da kuma a dandalin da yake a Ƙofar Efraim.17. Dukan jama’ar da suka komo daga zaman bauta suka yi bukkoki suka kuma zauna a cikinsu. Daga kwanakin Yoshuwa ɗan Nun har yă zuwa yau, Isra’ilawa ba su taɓa yin bikinsa haka ba. Mutane suka cika da farin ciki sosai.18. Kowace rana, daga rana farko zuwa ƙarshe, Ezra ya karanta daga Littafin Dokar Allah. Suka yi bikin kwana bakwai, a rana ta takwas kuma suka yi muhimmin taro bisa ga ƙa’ida.Nehemiya 9:1-381. A rana ta ashirin da huɗu ga watan nan, Isra’ilawa suka taru, suna yin azumi, suna sa rigunan makoki, suna kuma zuba toka a kansu.2. Waɗanda suke zuriyar Isra’ilawa suka ware kansu daga dukan baƙi. Suka tsaya, suka kuma furta zunubansu da muguntar kakanninsu.3. Sa’ad da suke nan a tsaye, aka ɗauki awa uku ana karanta Littafin Dokar Ubangiji Allahnsu. Aka kuma ɗauki awa uku ana sujada ga Ubangiji Allahnsu.4. A kan dakalin kuwa akwai Lawiyawa, wato, Yeshuwa, Bani, Kadmiyel, Shebaniya, Bunni, Sherebiya, Bani da Kenani tsaye, waɗanda suka kira da babbar murya ga Ubangiji Allahnsu.5. Lawiyawan nan, Yeshuwa, Kadmiyel, Bani, Hashabnehiya, Sherebiya, Hodiya, Shebaniya da Fetahahiya, suka ce, “Ku miƙe tsaye ku yabi Ubangiji Allahnku, wanda yake har abada abadin.” “Albarka ta tabbata ga sunanka mai ɗaukaka, bari kuma a ɗaukaka shi bisa dukan albarka da yabo.6. Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.7. “Kai ne Ubangiji Allah, wanda ya zaɓi Abram, ya fitar da shi daga Ur na Kaldiyawa, ya kuma ba shi suna Ibrahim.8. Kai ka sami zuciyarsa da aminci a gare ka, ka kuma yi alkawari da shi cewa za ka ba zuriyarsa ƙasar Kan’aniyawa, da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, da ta Yebusiyawa, da kuma ta Girgashiyawa. Ka kiyaye alkawarinka domin kai mai adalci ne.9. “Ka ga wahalar kakanninmu a Masar; ka kuwa ji kukansu a Jan Teku.10. Ka aika da alamu masu banmamaki da al’ajabai a kan Fir’auna, a kan dukan shugabanninsa da kuma a kan dukan mutanen ƙasarsa, gama ka ga irin danniyar da suka yi wa mutanenka. Ka samo wa kanka suna, wadda ta dawwama har yă zuwa yau.11. Ka raba teku a gaban kakanninmu, saboda su wuce cikinsa a busasshiyar ƙasa, amma ka hallaka masu binsu cikin zurfafa, nutse kamar dutse a cikin ruwa.12. Da rana ka bishe kakanninmu da girgije, da dare kuwa ka bishe su da ginshiƙin wuta don ka ba su haske a hanyar da za su bi.13. “Ka sauko a kan Dutsen Sinai; ka yi musu magana daga sama. Ka ba su ƙa’idodi da dokokin da suke masu adalci da kuma daidai, ka ba su farillai da umarnai da suke da kyau.14. Ka sanar da su Asabbacinka mai tsarki, ka kuma ba su umarnai, da farillai, da kuma dokoki ta wurin bawanka Musa.15. Cikin yunwansu ka ba su burodi daga sama, cikin ƙishirwansu kuma ka fitar musu ruwa daga dutse. Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka rantse ta wurin ɗaga hannu cewa za ka ba su.16. “Amma su kakanninmu, suka yi fariya da taurinkai, ba su kuwa yi biyayya ga umarnanka ba.17. Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba,18. ko ma sa’ad da suka yi wa kansu siffar ɗan maraƙi, suka ce, ‘Wannan shi ne allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar,’ ko sa’ad da suka yi saɓo mai bantsoro.19. “Saboda jinƙanka mai girma, ba ka yashe su a hamada ba. Da rana, ginshiƙin girgije bai daina bishe su a hanyarsu ba, da dare kuma ginshiƙin wuta bai daina haskakawa a hanyar da za su bi ba.20. Ka ba da Ruhunka mai kyau don yă koyar da su. Ba ka janye Manna naka daga bakunansu ba, ka kuma ba su ruwa don ƙishirwansu.21. Shekaru arba’in ka riƙe su a cikin hamada; ba su rasa kome ba, rigunansu ba su yage ba, ƙafafunsu kuwa ba su kumbura ba.22. “Ka ba su mulkoki da al’ummai, kana ba su har ma da ƙasashen da suke jeji. Suka ci ƙasar Sihon na sarkin Heshbon da ƙasar Og inda sarkin Bashan yake mulki.23. Ka sa ’ya’yansu maza suka yi yawa kamar taurarin sararin sama, ka kuma kawo su cikin ƙasar da ka faɗa wa kakanninsu su shiga su mallake.24. ’Ya’yansu maza suka shiga suka kuma mallaki ƙasar. A gabansu ka rinjayi Kan’aniyawan da suke zama a cikin ƙasar; ka ba da Kan’aniyawa a gare su, tare da sarakunansu da kuma mutanen ƙasar, su yi da su yadda suke so.25. Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.26. “Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro.27. Saboda haka ka miƙa su ga abokan gābansu waɗanda suka yi musu danniya. Amma sa’ad da ake danniyarsu sai suka yi kuka gare ka. Daga sama ka ji su, cikin jinƙanka mai girma kuwa ka ba su mai ceto, wanda ya fisshe su daga hannun abokan gābansu.28. “Amma nan da nan, da suka sami hutu, sai suka sāke aikata abin da yake mugu a idonka. Sai ka yashe su ga hannun abokan gābansu don su yi mulki a kansu. Sa’ad da suka yi kuka kuma gare ka, ka ji daga sama, cikin jinƙanka kuma ka fisshe su sau da sau.29. “Ka gargaɗe su su dawo ga dokarka, amma suka yi fariya, suka bijire wa umarnanka. Suka yi zunubi game da farillanka waɗanda ta wurinsu ne mutum zai rayu in ya yi biyayya da su. Cikin taurinkai suka juye bayansu daga gare ka, suka zama masu taurinkai, suka kuma ƙi su saurara.30. Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu.31. Amma cikin tausayinka mai girma ba ka kawo su ga ƙarshe ko ka yashe su ba, gama kai Allah ne mai alheri da kuma mai jinƙai.32. “To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.33. Cikin dukan abubuwan da suka faru da mu, ka kasance mai adalci; ka yi aminci, yayinda mu kuwa muka aikata mugu.34. Sarakunanmu, da shugabanninmu, da firistocinmu da kuma kakanninmu ba su bi dokarka ba, ba su ma mai da hankali ga umarnanka ko gargaɗin da ka yi musu ba.35. Ko ma yayinda suke a masarautarsu, suna jin daɗin girmar kyautatawarka gare su, cikin ƙasar mai girma, da kuma mai fāɗin da ka ba su, ba su bauta maka ko su juye daga mugayen hanyoyinsu ba.36. “Amma duba, mu bayi ne a yau, bayi a ƙasar da ka ba kakanninmu don su ci amfaninta da kuma waɗansu abubuwa masu kyau da take bayarwa.37. Saboda zunubanmu, yalwar girbin da muke samu yana tafiya wurin sarakunan da ka sa a kanmu. Suna mulki bisa jikunanmu, da bisa garkenmu yadda suka ga dama. Muna cikin baƙin ciki.38. “Saboda wannan duka, muna yin zaunannen alkawari, muna sa shi a rubuce, shugabanninmu kuwa da Lawiyawanmu, da firistocinmu suna buga hatimansu a kai.”Zabura 89:11-1811. Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta.12. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.13. Hannunka mai iko ne; hannunka yana da ƙarfi, hannunka na dama ya sami ɗaukaka.14. Adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinka; ƙauna da aminci suna tafiya a gabanka.15. Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji.16. Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.17. Gama kai ne ɗaukakarsu da ƙarfinsu, kuma ta wurin alherinka ka ɗaukaka ƙahonka.18. Tabbatacce, garkuwarmu ta Ubangiji ce, ta sarkinmu ce, da kuma ta Mai Tsarki na Isra’ila ce.Karin Magana 21:29-3129. Mugun mutum kan yi tsayin daka, amma mai aikata gaskiya kan yi tunani a kan abin da yake yi.30. Babu hikima, babu tunani, babu shirin da zai yi nasara a kan Ubangiji.31. Akan shirya doki domin ranar yaƙi, amma nasara tana ga Ubangiji ne.Ayyukan Manzanni 27:27-4427. A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa.28. Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in.29. Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyin jirgin guda huɗu daga bayan jirgin suka yi fata gari ya waye.30. Cikin ƙoƙarin tserewa daga jirgin, sai masu tuƙin jirgin suka saukar da ɗan ƙaramin jirgin ruwan cikin tekun, suka yi kamar za su saki waɗansu ƙugiyoyi daga sashen gaba na babban jirgin ne.31. Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.”32. Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.33. Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba.34. Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.”35. Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.36. Dukansu kuwa suka sami ƙarfafawa, suka kuma ci abinci.37. Dukanmu a jirgin kuwa mutane 276 ne.38. Sa’ad da suka ci iyakar abin da suke so, sai suka rage nauyin jirgin ta wurin zubar da hatsin a cikin tekun.39. Da gari ya waye, ba su gane ƙasar da suke ba, amma suka ga wani lungu da gaci mai yashi, sai suka yanke shawara su kai jirgin can in za su iya.40. Da suka yanke ƙugiyoyin, sai suka bar su a cikin teku a lokaci guda kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Sai suka tā da filafilan gaban jirgin daidai yadda iska za tă tura shi gaba, sa’an nan suka nufi gaci.41. Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.42. Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere.43. Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci.44. Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.