Baibul a cikin shekara guda Yuli 52 Tarihi 5:1-141. Sa’ad da dukan aikin da Solomon ya yi domin haikalin Ubangiji ya gama, sai ya kawo abubuwan da mahaifinsa Dawuda ya keɓe a ciki, azurfa da zinariya da kuma dukan kayayyaki, ya kuwa sa su a cikin ma’ajin haikalin Allah.2. Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda.3. Dukan mutanen Isra’ila kuwa suka tattaru gaba ɗaya suka zo wurin sarki a lokacin biki a wata na bakwai.4. Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, Lawiyawa suka ɗauki akwatin alkawarin,5. suka haura da akwatin alkawarin da kuma Tentin Sujada da dukan kayayyaki masu tsarkin da yake cikinta. Firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, suka ɗauke su;6. Sarki Solomon kuwa da taron Isra’ila gaba ɗaya da suka taru kewaye da shi suna a gaban akwatin alkawarin, suna miƙa tumaki da shanu masu yawa da suka wuce ƙirge ko lissafi.7. Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji zuwa wurinsa a ciki cikin wuri mai tsarki na haikali, Wuri Mafi Tsarki, suka sa shi ƙarƙashin fikafikan kerubobin.8. Kerubobin suka buɗe fikafikansu a bisa wurin akwatin alkawari suka kuma rufe akwatin alkawarin da sandunan ɗaukonsa.9. Waɗannan sanduna sun yi tsawo ƙwarai har ƙarshensu sun nausa daga akwatin alkawarin, ana iya ganinsu daga gaban ciki wuri mai tsarki na can ciki amma ba daga waje Wuri Mai Tsarki ba; kuma suna nan a can har wa yau.10. Babu wani abu a cikin akwatin alkawarin sai alluna biyu da Musa ya sa a cikinsa a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar.11. Sa’an nan firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki. Dukan firistocin da suke can sun tsarkake kansu, ko daga wace ɓangarori suka fito.12. Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni.13. Masu busan ƙahonin da mawaƙa suka haɗu da baki ɗaya sai ka ce murya guda ce, don su yabi su kuma yi godiya ga Ubangiji. Haɗe da busan ƙahoni, ganguna da sauran kayayyaki, suka tā da muryoyinsu cikin yabo ga Ubangiji suka rera, “Yana da kyau; ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai haikalin Ubangiji ya cika da girgije,14. Firistoci ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalin Allah.2 Tarihi 6:1-421. Sa’an nan Solomon ya ce, “ Ubangiji ya faɗa cewa zai zauna cikin duhun girgije;2. na gina ƙasaitaccen haikali dominka, wuri domin ka zauna har abada.”3. Yayinda dukan taron Isra’ila suke tsaye a can, sai sarki ya juya ya albarkace su.4. Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,5. ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.6. Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’7. “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.8. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.9. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’10. “ Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.11. A can na ajiye akwatin alkawari, inda alkawarin Ubangiji da ya yi da mutanen Isra’ila yake.”12. Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama.13. Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.14. Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka.15. Ka kiyaye alkawarinka ga bawanka Dawuda mahaifina; da bakinka ka yi alkawari kuma da hannunka ka cika shi, yadda yake a yau.16. “Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’17. Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.18. “Amma tabbatacce Allah zai zauna a duniya tare da mutane? Sammai, har ma da saman sammai, ba za su iya riƙe ka ba. Balle wannan haikalin da na gina!19. Duk da haka ka mai da hankali ga addu’ar bawanka da kuma roƙo don jinƙai, ya Ubangiji, Allahna. Ka ji kuka da addu’ar da bawanka yake yi a gabanka.20. Bari idanunka su buɗu ta wajen wannan haikali dare da rana, wannan wurin da ka ce za ka sa Sunanka a can. Bari ka ji addu’ar da bawanka ke yi ta wajen wannan wuri.21. Ka ji roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a suna duban wajen wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka; kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.22. “Sa’ad da mutum ya yi wa maƙwabcinsa laifi aka kuma bukaci ya yi rantsuwa, ya kuma zo ya rantse a gaban bagadenka a cikin wannan haikali,23. sai ka ji daga sama ka kuma yi wani abu. Ka shari’anta tsakanin bayinka, kana sāka wa mai laifi ta wurin kawo a kansa hakkin abin da ya yi. Ka nuna cewa marar laifi ba shi da laifi, ta haka a fiffita rashin laifinsa.24. “Sa’ad da an ci mutanenka Isra’ila a yaƙi ta wurin abokin gāba domin sun yi maka zunubi kuma sa’ad da suka juya suka furta sunanka, suna addu’a suka kuma yin roƙe-roƙe a gabanka a wannan haikali,25. sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin mutanenka Isra’ila ka kuma dawo da su zuwa ƙasar da ka ba su da kuma kakanninsu.26. “Sa’ad da sammai suka rufu ba kuwa ruwan sama saboda mutanenka sun yi maka zunubi, sa’ad da kuwa suka yi addu’a suna duban waje wannan wuri suka kuma furta sunanka suka juye daga zunubinsu domin ka azabta su,27. sai ka ji daga sama ka kuma gafarta zunubin bayinka, mutanenka Isra’ila. Ka koya musu hanyar da ta dace da za su yi zama, ka kuma aika ruwan sama a ƙasar da ka ba mutanenka gādo.28. “Sa’ad da yunwa ko annoba ta fāɗo a ƙasar, ko wahala ko fumfuna, ko fāra ko fāra ɗango, ko sa’ad da abokan gāba sun yi musu ƙawanya a kowane daga biranensu, dukan wata masifa ko cutar da za tă zo,29. sa’ad da kuwa wani cikin mutanenka Isra’ila ya yi wata addu’a ko roƙo, kowa yana sane a azabarsa da kuma zafinsa, yana buɗe hannuwansa yana duban wajen wannan haikali,30. sai ka ji daga sama, mazauninka. Ka gafarta, ka kuma yi da kowane mutum gwargwadon duk abin da yake yi, da yake ka san zuciyarsa (gama kai kaɗai ka san zukatan mutane),31. don su ji tsoronka su kuma yi tafiya a hanyoyinka a kowane lokacin da suke zama a ƙasar da ka ba wa kakanninsu.32. “Game da baƙo wanda shi ba na mutanenka Isra’ila ba kuwa amma ya zo daga ƙasa mai nisa saboda sunanka mai girma da kuma hannunka mai iko da hannunka mai ƙarfi, sa’ad da ya zo ya yi addu’a yana duban wannan haikali,33. sai ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi duk abin da baƙon ya nemi ka yi, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, su kuma san cewa wannan gidan da na gina na Sunanka ne.34. “Sa’ad da mutanenka suka je yaƙi da abokan gābansu, ko’ina ka kai su, kuma sa’ad da suka yi addu’a gare ka suna duban wannan birnin da ka zaɓa da haikalin nan da na gina domin Sunanka,35. sai ka ji addu’arsu da kuma roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatarsu.36. “Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wani wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su ka miƙa su ga abokin gāba, wanda ya kai su zaman bauta a ƙasa mai nisa ko kuwa kusa;37. Kuma in suka canja zuciya a cikin ƙasar da suke zaman bauta, suka tuba suka roƙe ka a ƙasar zaman bautarsu suka kuma ce, ‘Mun yi zunubi, mu yi abin da ba daidai ba, mu kuwa yi mugunta’;38. in kuma sun juye gare ka da dukan zuciyarsu da ransu a ƙasar zaman bautarsu inda aka kai su, suka kuma dubi wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, wajen birnin da ka zaɓa da kuma wajen haikalin da na gina domin Sunanka;39. to, daga sama, mazauninka, sai ka ji addu’arsu da kuma roƙe-roƙensu, ka kuwa biya musu bukatunsu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi.40. “Yanzu, Allahna, bari idanunka su buɗu kunnuwanka kuma su saurara ga addu’o’in da ake miƙa a wannan wuri.41. “Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari firistocinka, ya Ubangiji Allah, su sanye ceto, bari tsarkakanka su yi farin ciki cikin alherinka.42. Ya Ubangiji Allah, kada ka ƙyale shafaffenka. Ka tuna da ƙauna mai girma da ka alkawarta wa Dawuda bawanka.”Zabura 79:11-1311. Bari nishe-nishen ’yan kurkuku su zo gabanka; ta wurin ƙarfin hannunka ka kiyaye waɗanda aka yanke wa hukuncin mutuwa.12. Ka sāka a cinyoyin maƙwabtanmu sau bakwai zage-zagen da suka yi ta yi maka, ya Ubangiji.13. Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka.Karin Magana 20:13-1413. Kada ka so barci in ba haka ba za ka talauce; ka zauna a faɗake za ka kuwa kasance da sauran abinci.14. “Kai, ya yi tsada, ya yi tsada!” In ji mai saya; sa’ad da ya tafi yana taƙama a kan ya iya ciniki.Ayyukan Manzanni 13:1-251. A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu.2. Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.”3. Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.4. Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus.5. Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.6. Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu,7. wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah.8. Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya.9. Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce,10. “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba?11. Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.12. Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.13. Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima.14. Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna.15. Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.”16. Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni!17. Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar,18. ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada,19. ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa.20. Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450. “Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila.21. Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in.22. Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’23. “Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.24. Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.25. Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’ Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.