Baibul a cikin shekara guda Yuli 62 Tarihi 7:1-221. Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin.2. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi.3. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “ Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”4. Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji.5. Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah.6. Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.7. Solomon ya tsarkake sashen tsakiya na filin da yake gaban haikalin Ubangiji, a can ya miƙa hadayun ƙonawa da kitsen hadayun salama domin bagaden tagullar da ya yi ba zai iya ɗaukan hadayun ƙonawa, hadayun hatsi da kuma ɓangarori na kitsen ba.8. Ta haka Solomon ya kiyaye bikin a wannan lokaci har kwana bakwai, dukan Isra’ila kuwa tare da shi, babban taro, mutane daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar.9. A rana ta takwas sai suka yi taro, gama sun yi bikin keɓewar bagade na kwana bakwai da kuma biki na ƙarin kwana bakwai.10. A rana ta ashirin da uku na watan bakwai sai ya sallami mutane su tafi gidajensu da farin ciki da kuma murna a zuciya saboda abubuwa masu kyau da Ubangiji ya yi domin Dawuda da Solomon da kuma domin mutanensa Isra’ila.11. Sa’ad da Solomon ya gama haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki ya kuma yi nasara a yin dukan abin da yake a zuciyarsa da zai yi a haikalin Ubangiji da kuma a fadarsa,12. sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu.13. “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena,14. in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.15. Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.16. Na zaɓi na kuma tsarkake wannan haikali saboda Sunana yă kasance a can har abada. Idanuna da kuma zuciyata kullum za su kasance a can.17. “Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,18. zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’19. “Amma in ka juya daga gare ni ka yashe ƙa’idodi da umarnan da na ba ka, ka yi gaban kanka don ka bauta wa waɗansu alloli ka kuma yi musu sujada,20. zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane.21. Ko da yake wannan haikali yanzu mai girma ne, dukan wanda ya wuce zai kaɗa kai yă ce, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi irin wannan abu ga wannan ƙasa da kuma ga wannan haikali?’22. Mutane za su amsa, ‘Domin sun yashe Ubangiji Allah na kakanninsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna musu sujada, suna bauta musu, shi ya sa ya kawo dukan wannan masifa a kansu.’ ”2 Tarihi 8:1-181. A ƙarshen shekaru ashirin, a lokacin da Solomon ya gina haikalin Ubangiji da nasa fadan,2. Solomon ya sāke gina ƙauyukan da Hiram ya ba shi, ya kuma zaunar da Isra’ilawa a cikinsu.3. Sa’an nan Solomon ya tafi Hamat-Zoba ya ci ta da yaƙi.4. Ya kuma gina Tadmor a hamada da kuma dukan biranen ajiyar da ya gina a Hamat.5. Ya sāke gina Bet-Horon na Bisa da kuma Bet-Horon na Ƙasa a matsayin birane masu katanga, da bangaye da ƙofofi da kuma ƙyamare,6. haka kuma Ba’alat da dukan biranen ajiyarsa, da kuma dukan birane domin keken yaƙinsa da dawakansa, duk abin da ya so yă gina a Urushalima, a Lebanon da kuma dukan yankin da ya yi mulki, ya gina shi.7. Dukan mutanen da suka rage daga Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa (waɗannan mutane ba Isra’ilawa ba ne),8. wato, zuriyarsu da suka ragu a ƙasar, wadda Isra’ilawa ba su hallaka ba, waɗannan ne Solomon ya mai da su bayinsa na aikin dole, kamar yadda yake har wa yau.9. Amma Solomon bai mai da Isra’ilawa bayi don aikinsa ba; su ne mayaƙansa, shugabannin hafsoshinsa, da shugabannin keken yaƙinsa da kuma mahayan keken yaƙinsa.10. Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane.11. Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”12. A kan bagaden Ubangiji da ya gina a gaban shirayi, Solomon ya miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji,13. bisa ga bukace-bukace na kullum don hadayun da Musa ya umarta don Asabbatai, Sabon Wata da kuma bukukkuwa uku na shekara, Bikin Burodi Marar Yisti, Bikin Makoni da Bikin Tabanakul.14. Bisa ga farillar mahaifinsa Dawuda, ya naɗa ɓangarori na firistoci don ayyukansu da Lawiyawa don su jagoranci yabo su kuma taimaki firistoci bisa ga bukace-bukacen kowace rana. Ya kuma naɗa matsara ƙofofi ɓangarori, ɓangarori don ƙofofi dabam-dabam domin abin da Dawuda mutumin Allah ya umarta ke nan.15. Ba a kuwa yi rashin biyayya ba game da abin da sarki ya umarta game da firistoci ko Lawiyawa a kan kayan haikalin ba.16. An yi dukan ayyukan Solomon, daga ranar kafa tushen haikalin Ubangiji har gamawarsa. Ta haka aka gama haikalin Ubangiji.17. Sa’an nan Solomon ya tafi Eziyon Geber da Elot a bakin tekun Edom.18. Sai Hiram ya aika masa jiragen ruwan da masu tuƙinsu waɗanda suka san teku sosai. Ma’aikatan Hiram suka tafi da na Solomon zuwa Ofir suka dawo da talentin zinariya ɗari huɗu da hamsin wa Sarki Solomon.Zabura 80:1-61. Ka ji mu, ya Makiyayin Isra’ila, kai da ka bishe Yusuf kamar garke. Kai da kake zaune a kursiyi tsakanin kerubobi, ka haskaka2. a gaban Efraim, Benyamin da Manasse. Ka tā da ƙarfinka; ka zo ka cece mu.3. Ka mai da mu, ya Allah; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.4. Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, har yaushe fushinka zai yi ta ƙuna a kan addu’o’in mutanenka?5. Ka ciyar da su da burodin hawaye; ka sa suka sha hawaye ta cikakken kwaf.6. Ka mai da mu abin faɗa ga maƙwabtanmu, kuma abokan gābanmu suna mana ba’a.Karin Magana 20:15-1515. Zinariya akwai ta, lu’ulu’u kuma ga shi a yalwace, amma leɓunan da suke magana da sani suna da wuyan samu kamar duwatsu masu daraja.Ayyukan Manzanni 13:26-5226. “Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto.27. Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci.28. Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi.29. Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari.30. Amma Allah ya tashe shi daga matattu,31. kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.32. “Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,33. ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa, “ ‘Kai Ɗana ne, yau na zama Uba a gare ka.’34. Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi. “ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’35. Haka kuma aka faɗa a wani wuri. “ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’36. “Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe.37. Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba.38. “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.39. Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.40. Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku.41. “ ‘Ku duba, ku masu ba’a, ku yi mamaki, ku hallaka, gama zan yi wani abu a zamaninku da ba za ku taɓa gaskatawa ba ko da wani ya gaya muku.’ ”42. Bulus da Barnabas suna fita daga majami’ar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa.43. Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.44. A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji.45. Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.46. Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai.47. Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’ ”48. Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.49. Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin.50. Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu.51. Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.52. Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.