Baibul a cikin shekara guda
Yuli 7

1. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ji shahararr Solomon, sai ta zo Urushalima tă gwada shi da tambayoyi masu wuya. Ta iso tare da ayari mai girma, da raƙuma ɗauke da kayan yaji, zinariya mai yawa, da kuma duwatsu masu daraja, ta zo wurin Solomon ta kuma yi magana da shi game da dukan abin da yake zuciyarta.
2. Solomon ya amsa dukan tambayoyinta; babu wani abin da ya yi masa wuya yă bayyana mata.
3. Sa’ad da sarauniyar Sheba ta ga hikimar Solomon da kuma fadan da ya gina,
4. ta ga abincin da yake teburinsa, ta ga zaman fadawansa, bayi masu yin masa hidima cikin rigunansu, ta ga masu riƙe kwaf cikin rigunansu da kuma hadayun ƙonawar da ya yi a haikalin Ubangiji, sai mamaki ya kama ta.
5. Ta ce wa sarki, “Labarin da na ji a ƙasata game da nasarorinka da hikimarka, gaskiya ne.
6. Amma ban gaskata abin da suka faɗa ba sai da na zo na kuma gani da idanuna. Tabbatacce, ko rabin girman hikimarka ba a faɗa mini ba, ka wuce labarin da na ji nesa ba kusa ba.
7. Abin farin ciki ne ga mutanenka! Abin farin ciki ne ga fadawanka, waɗanda suke cin gaba da tsayawa a gabanka suna kuma jin hikimarka!
8. Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.”
9. Sa’an nan ta ba sarki talenti 120 na zinariya, kayan yaji masu yawa, da kuma duwatsu masu daraja. Ba a taɓa kasance da irin kayan yaji mai yawa kamar waɗanda sarauniyar Sheba ta ba wa sarki Solomon ba.
10. (Mutanen Hiram da mutanen Solomon suka kawo zinariya daga Ofir, suka kuma kawo gungumen algum da duwatsu masu daraja.
11. Sarki ya yi amfani da gungumen algum don matakalan haikalin Ubangiji da kuma na fadan sarki, ya kuma yi garayu da molaye don mawaƙa. Ba a taɓa gani irinsu a Yahuda ba.)
12. Sarki Solomon ya ba sarauniyar Sheba duk abin da take so da kuma ta nema; ya ba ta fiye da abin da ta kawo masa. Sa’an nan ta tashi ta koma ƙasarta tare da masu rufe mata baya.
13. Nauyin zinariyar da Solomon yake karɓa shekara-shekara talenti 666 ne,
14. ban da harajin da fatakai da ’yan kasuwa suke biya. Haka kuma dukan sarakunan Arabiya da gwamnonin ƙasar suka kawo zinariya da azurfa wa Solomon.
15. Sarki Solomon ya yi manyan garkuwoyi ɗari biyu da zinariya; an yi kowane garkuwa da bekas ɗari shida na zinariya.
16. Ya kuma yi ƙanana garkuwoyi zinariya ɗari uku, da bekas ɗari uku na zinariya a kowanne. Sarki ya sa su a cikin Fadan da ake kira Kurmin Lebanon.
17. Sai sarki ya yi wata kujerar sarauta mai girma da aka shafe ta da hauren giwa, aka kuma dalaye ta da zinariya zalla.
18. Kujerar tana da matakalai shida, da wurin sa ƙafa na zinariya haɗe da ita. A kowane gefen wurin zama, akwai wurin ajiye hannu, da zaki tsaye kusa da kowannensu.
19. Zakoki goma sha biyu sun tsaya a kan matakalai shida, ɗaya a ƙarshen matakala guda. Ba a taɓa yin irin wannan abu don wata masarauta ba.
20. Dukan kwaf na Sarki Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon zinariya ne zalla. Ba a yi wani abu da azurfa ba, domin ba a ɗauki azurfa a zamanin Solomon a bakin kome ba.
21. Sarki yana da jerin jiragen ruwa na kasuwanci waɗanda mutanen Hiram ne suke kula da su. Sau ɗaya kowace shekara uku sukan dawo ɗauke da zinariya, azurfa, hauren giwa, gogo da kuma birai.
22. Sarki Solomon ya fi arziki da hikima in aka kwatanta da dukan sauran sarakunan duniya.
23. Dukan sarakunan duniya sun nemi su sadu da Solomon don su ji hikimar da Allah ya sa a zuciyarsa.
24. Shekara, shekara, duk wanda ya zo wurinsa yakan kawo kyauta, kayayyakin azurfa da na zinariya, da riguna, makamai da kayan yaji, da dawakai da kuma alfadarai.
25. Solomon ya kasance da wuraren ajiye dawakai dubu huɗu don dawakai da kekunan yaƙi, yana da dawakai dubu goma sha biyu waɗanda ya ajiye a biranen kekunan yaƙi da kuma tare da shi a Urushalima.
26. Ya yi mulki bisa dukan sarakuna daga Kogi Yuferites zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar.
27. Sarki ya sa azurfa ta zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma da yawa kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.
28. An sayo dawakan Solomon daga Masar da kuma daga dukan sauran ƙasashe.
29. Game da sauran ayyukan mulkin Solomon, daga farko har zuwa ƙarshe, an rubuta su a cikin tarihin annabi Natan, cikin annabcin Ahiya mutumin Shilo da kuma cikin wahayin Iddo mai gani game da Yerobowam ɗan Nebat.
30. Solomon ya yi mulki a Urushalima a bisa dukan Isra’ila shekaru arba’in.
1. Rehobowam ya tafi Shekem, gama dukan Isra’ilawa sun je can don su naɗa shi sarki.
2. Da Yerobowam ɗan Nebat ya ji wannan (a lokacin yana a Masar, inda ya gudu daga Sarki Solomon ya tafi), sai ya dawo daga Masar.
3. Saboda haka suka aika a zo da Yerobowam, sai shi da dukan Isra’ila suka je wurin Rehobowam suka ce masa.
4. “Mahaifinka ya sa mana kaya masu nauyi a kanmu, amma yanzu ka sauƙaƙa mana aiki mai zafin nan da kuma kaya masu nauyin da ya sa a kanmu, mu kuwa za mu bauta maka.”
5. Rehobowam ya amsa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Saboda haka mutanen suka watse.
6. Sai Sarki Rehobowam ya nemi shawarar dattawan da suka yi wa mahaifinsa Solomon hidima a lokacin da yake da rai, ya tambaye suya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa waɗannan mutane?”
7. Suka amsa suka ce, “In za ka ji tausayi waɗannan mutane ka kuma gamshe su, ka kuma ba su amsar da ta dace, kullum za su zama bayinka.”
8. Amma Rehobowam ya ƙi shawarar da dattawa suka ba shi ya kuma nemi shawarar matasan da suka yi girma tare, suke kuma yin masa hidima.
9. Ya tambaye su ya ce, “Mece ce shawararku? Yaya zan amsa wa waɗannan mutanen da suke ce mini, ‘Ka sauƙaƙa nauyin da mahaifinka ya sa a kanmu’?”
10. Matasan da suka yi girma tare shi suka amsa, “Faɗa wa mutanen da suke ce maka, ‘Mahaifinka ya sa kaya masu nauyi a kanmu, amma ka sauƙaƙa nauyinmu.’ Ka faɗa musu, ‘Ƙaramin yatsana ya fi ƙugun mahaifina kauri.
11. Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.’ ”
12. Bayan kwana uku sai Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam, yadda sarki ya ce, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.”
13. Sarki ya amsa musu da kakkausar murya. Ya ƙi shawarar dattawan,
14. ya kuma bi shawarar matasan ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; zan ma sa mafi nauyi. Mahaifina ya bulale ku da bulala; zan bulale ku da kunamai.”
15. Saboda haka sarki bai saurari mutane ba, gama wannan juyin al’amura daga Allah ne, don a cika maganar Ubangiji da ya yi ga Yerobowam ɗan Nebat ta wurin Ahiya mutumin Shilo.
16. Sa’ad da Isra’ila suka ga sarki ya ƙi yă saurare su, sai suka amsa wa sarki, suka ce, “Wanda rabo muke da shi a wurin Dawuda, wanda sashe muke da shi daga ɗan Yesse? Kowa yă koma tentinsa, ya Isra’ila! Ka lura da gidanka, ya Dawuda!” Saboda haka dukan Isra’ilawa suka tafi gida.
17. Amma game da Isra’ilawan da suke zama a garuruwan Yahuda kuwa, Rehobowam ya ci gaba da yin mulki a bisansu.
18. Sarki Rehobowam ya aiki Hadoram wanda yake lura da aikin dole, amma Isra’ilawa suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu. Sarki Rehobowam kuwa ya gaggauta ya shiga keken yaƙinsa ya gudu zuwa Urushalima.
19. Ta haka Isra’ila ya kasance cikin tawaye a kan gidan Dawuda har yă zuwa wannan rana.
7. Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.
8. Ka fitar da inabi daga Masar; ka kori al’ummai ka kuma dasa shi.
9. Ka gyara wuri saboda shi, ya kuwa yi saiwa ya cike ƙasa.
10. Aka rufe duwatsu da inuwarsa, manya-manyan itatuwan al’ul da rassansa.
11. Ya miƙe rassansa zuwa Teku tohonsa har zuwa Kogi.
12. Me ya sa ka rurrushe bangayensa don duk masu wucewa su tsinke ’ya’yan inabinsa?
13. Aladu daga kurmi suna ɓarnatar da shi halittun gonaki kuma suna cinsa.
16. A karɓi rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.
17. Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.
18. Ka yi shirye-shirye ta wurin neman shawara; in kana yaƙi, ka sami bishewa.
1. A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata.
2. Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa.
3. Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki.
4. Mutanen birnin suka rarrabu, waɗansu suka goyi bayan Yahudawa, waɗansu kuma suka goyi bayan manzannin.
5. Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu.
6. Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye,
7. inda suka ci gaba da wa’azin labari mai daɗi.
8. A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba.
9. Ya kasa kunne yayinda Bulus yake magana. Bulus kuma ya kafa masa ido, ya lura cewa yana da bangaskiyar da za tă warkar da shi
10. sai ya ɗaga murya ya ce, “Tashi ka tsaya kan ƙafafunka!” Da jin haka, sai mutumin ya yi wuf ya kuma fara tafiya.
11. Sa’ad da taron suka ga abin da Bulus ya yi, sai suka ihu da harshen Likayoniyawa, suna cewa, “Alloli sun sauka mana da siffar mutane!”
12. Sai suka ba wa Barnabas, sunan Zeyus, Bulus kuma suka kira Hermes domin shi ne shugaban magana.
13. Firist na Zeyus, wanda haikalinsa ke bayan birni, ya kawo bijimai da furanni a ƙofofin birni domin shi da taron mutanen sun so su miƙa musu hadayu.
14. Amma da manzannin nan Barnabas da Bulus suka ji haka, sai suka yayyage tufafinsu suka ruga cikin taron, suna ihu suna cewa,
15. “Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.
16. A zamanin dā, ya bar dukan ƙasashe su yi yadda suka ga dama.
17. Duk da haka bai bar kansa babu shaida ba. Ya nuna alheri ta wurin ba ku ruwan sama da kuma amfanin gona a lokutansu; ya ba ku abinci mai yawa ya kuma cika zukatanku da farin ciki.”
18. Ko da waɗannan kalmomi ma, da ƙyar suka hana jama’an nan yin musu hadaya.
19. Sai waɗansu Yahudawa suka zo daga Antiyok da Ikoniyum suka sha kan taron. Suka jajjefi Bulus da duwatsu suka kuma ja shi bayan birni, suna tsammani ya mutu.
20. Amma bayan da almajiran suka taru kewaye da shi, sai ya tashi ya koma cikin birni. Kashegari shi da Barnabas suka tashi zuwa Derbe.
21. Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok,
22. suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
23. Bulus da Barnabas suka naɗa musu dattawa a kowace ikkilisiya, tare da addu’a da azumi, suka miƙa su ga Ubangiji, wanda suka dogara da shi.
24. Bayan sun bi ta Fisidiya, sai suka zo cikin Famfiliya,
25. kuma sa’ad da suka yi wa’azi a Ferga, sai suka gangara zuwa Attaliya.
26. Daga Attaliya kuma suka shiga jirgin ruwa suka koma Antiyok, inda dā aka danƙa su ga alherin Allah saboda aikin da suka kammala yanzu.
27. Da isarsu a can, sai suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da rahoton duk abin da Allah ya aikata ta wurinsu da kuma yadda ya buɗe ƙofar bangaskiya domin Al’ummai.
28. Suka kuma jima a can tare da almajirai.
Hausa Bible 2020
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ 2009, 2020 by Biblica, Inc.