Baibul a cikin shekara guda Yuli 82 Tarihi 11:1-231. Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.2. Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah.3. “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin,4. ‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.5. Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda.6. Betlehem, Etam, Tekowa,7. Bet-Zur, Soko, Adullam,8. Gat, Maresha, Zif,9. Adorayim, Lakish, Azeka,10. Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.11. Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.12. Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.13. Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.14. Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.15. Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.16. Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.17. Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.18. Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.19. Ta haifa masa ’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham.20. Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.21. Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.22. Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.23. Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.2 Tarihi 12:1-161. Bayan mulkin Rehobowam ya kahu kamar sarki ya kuma yi ƙarfi, shi da dukan Isra’ila suka yi biris da dokar Ubangiji.2. Domin sun yi rashin biyayya ga Ubangiji, saboda haka Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima a shekara ta biyar ta Sarki Rehobowam.3. Da kekunan yaƙi dubu ɗaya da ɗari biyu da kuma mahayan dawakai dubu haɗe da mayaƙan Libiyawa, Sukkatawa da kuma Kushawa waɗanda suka wuce ƙidaya suka zo tare da shi daga Masar,4. ya ci biranen katanga na Yahuda har zuwa Urushalima.5. Sai annabi Shemahiya ya zo wurin Rehobowam da kuma wajen shugabannin Yahuda waɗanda suka taru a Urushalima don tsoron Shishak, ya kuma faɗa musu, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Kun yi biris da ni; saboda haka, yanzu na bashe ku ga Shishak.’ ”6. Shugabannin Isra’ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka ce, “ Ubangiji mai adalci ne.”7. Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.8. Duk da haka za su zama bayinsa, don su san bambanci tsakanin yin mini bauta da kuma yin wa sarakunan sauran ƙasashe bauta.”9. Da Shishak sarkin Masar ya yaƙi Urushalima, sai ya kwashi ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin fadan sarki. Ya kwashe kome da kome, har da garkuwoyin zinariyar da Solomon ya yi.10. Sai sarki Rehobowam ya ƙera garkuwoyin tagulla a madadin na zinariya, ya sa su a hannun shugabannin matsara na mashigin gidan sarki.11. Duk sa’ad da sarki ya tafi haikalin Ubangiji, masu tsaron sukan tafi tare da shi, suna riƙe da garkuwoyi, daga baya kuma su mai da su a ɗakin tsaro.12. Gama Rehobowam ya ƙasƙantar da kansa, fushin Ubangiji ya bar shi, ba a kuwa hallaka shi ƙaƙaf ba. Tabbatacce an yi ’yan abubuwa masu kyau a Yahuda.13. Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce.14. Ya aikata mugunta domin bai sa zuciyarsa ga neman Ubangiji ba.15. Game da ayyukan mulkin Rehobowam, daga farko zuwa ƙarshe, ba a rubuce suke a tarihin Shemahiya annabi da Iddo mai gani wanda yake zancen zuriyoyi ba? Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Rehobowam da Yerobowam.16. Rehobowam ya huta da kakanninsa aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Abiya ɗansa kuma ya gāje shi a matsayin sarki.Zabura 80:14-1914. Ka komo wurinmu, ya Allah Maɗaukaki! Ka duba daga sama ka gani! Ka lura da wannan inabi,15. saiwar da hannun damarka ya dasa, ɗan da ka renar wa kanka.16. An yanke inabinka, an ƙone shi da wuta; a tsawatawarka mutanenka sun hallaka.17. Bari hannunka yă zauna a kan mutumin da yake hannun damarka, ɗan mutum da ka renar wa kanka.18. Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.19. Ka mai da mu, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu, za mu kuwa cetu.Karin Magana 20:19-2119. Mai gulma yakan lalace yarda; saboda haka ka guji mutum mai yawan surutu.20. In mutum ya zargi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, fitilarsa za tă mutu a tsakiyar duhu.21. Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.Ayyukan Manzanni 15:1-211. Waɗansu mutane suka gangara daga Yahudiya zuwa Antiyok suna kuma koya wa ’yan’uwa cewa, “Sai ko an yi muku kaciya bisa ga al’ada da Musa ya koyar, in ba haka ba, ba za ku sami ceto ba.”2. Wannan ya kai Bulus da Barnabas suka shiga babban gardama da muhawwara da su. Saboda haka aka naɗa Bulus da Barnabas tare da waɗansu masu bi, su haura zuwa Urushalima don su ga manzanni da dattawa a kan wannan magana.3. Ikkilisiya ta raka su suka tafi, yayinda suke ratsawa ta Funisiya da Samariya, suka ba da labari yadda Al’ummai suka tuba. Wannan labarin ya sa dukan ’yan’uwa suka yi murna ƙwarai.4. Sa’ad da suka isa Urushalima, sai ikkilisiya da manzanni da kuma dattawa suka marabce su, sai suka ba su rahoton dukan abin da Allah ya aikata ta wurinsu.5. Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”6. Sai manzanni da dattawa suka taru don su duba maganar.7. Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.8. Allah, wanda ya san zuciya, ya nuna cewa ya karɓe su ta wurin ba su Ruhu Mai Tsarki, kamar yadda ya ba mu.9. Bai nuna bambanci tsakaninmu da su ba, gama ya tsarkake zukatansu ta wurin bangaskiya.10. To, fa, don me kuke ƙoƙari ku gwada Allah ta wurin ɗora wa almajiran nan kayan da mu ko kakanninmu ba mu iya ɗauka ba?11. A’a! Mun gaskata cewa ta wurin alherin Ubangiji Yesu ne muka sami ceto, kamar yadda su ma suka samu.”12. Sai duk taron suka yi tsit yayinda suke sauraron Barnabas da Bulus suna ba da labari game da ayyuka da kuma abubuwan banmamakin da Allah ya yi a cikin Al’ummai ta wurinsu.13. Da suka gama, sai Yaƙub ya yi magana ya ce, “’Yan’uwa, ku saurare ni.14. Siman ya bayyana mana yadda Allah da farko ya nuna damuwarsa ta wurin ɗaukan mutane daga cikin Al’ummai su zama nasa.15. Kalmomin annabawa sun yi daidai da wannan, kamar yadda yake a rubuce cewa,16. “ ‘Bayan wannan zan koma in kuma sāke gina tentin Dawuda da ya rushe. Kufansa zan sāke gina, in kuma mai da shi,17. don ragowar mutane su nemi Ubangiji, kuma duk Al’umman da suke kira bisa sunana, in ji Ubangiji, wanda yake yin waɗannan abubuwa’18. da aka sani tun zamanai.19. “Saboda haka, a ganina, kada mu matsa wa Al’ummai waɗanda suke juyowa ga Allah.20. A maimakon haka, ya kamata mu rubuta musu cewa, su guji abincin da alloli suka ƙazantar, da fasikanci, da naman dabbar da aka murɗe da kuma jini.21. Gama Musa ya yi wa’azi a kowace birni tun zamanin dā, ana kuma karanta shi a majami’u kowane Asabbaci.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.