Baibul a cikin shekara guda Yuli 92 Tarihi 13:1-221. A shekara ta sha takwas ta sarautar Yerobowam, Abiya ya zama sarkin Yahuda,2. ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru uku. Sunan mahaifiyarsa Mikahiya ce, ’yar Uriyel na Gibeya. Aka kasance da yaƙe-yaƙe tsakanin Abiya da Yerobowam.3. Abiya ya tafi yaƙi tare da mayaƙa dubu ɗari huɗu jarumawa, Yerobowam kuwa ya ja dāgār yaƙi a kan Abiya da mayaƙa dubu ɗari takwas jarumawa.4. Abiya ya tsaya a Dutsen Zemarayim, a ƙasar tudu ta Efraim ya ce, “Yerobowam da dukan Isra’ila, ku saurare ni!5. Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba?6. Duk da haka Yerobowam ɗan Nebat, ma’aikacin Solomon ɗan Dawuda, ya tayar wa maigidansa,7. sai ya tara wa kansa ’yan iska da mugayen mutane suka yi gāba da Rehobowam ɗan Solomon. Rehobowam lokacin kuwa ba shi da wayo, don haka bai iya tsai da su ba.8. “Yanzu kuna shirin yin tsayayya da mulkin Ubangiji, wanda yake a hannuwan zuriyar Dawuda. Tabbatacce ku ƙasaitacciyar mayaƙa ne kuma kuna tare da ku maruƙan zinariyar da Yerobowam ya yi domin su zama allolinku.9. Ba ku ne kuka kori firistocin Ubangiji, ’ya’yan Haruna maza, da Lawiyawa kuka kuma zaɓi firistocinku kamar yadda sauran al’ummai suke yi ba? Duk wanda ya zo ya miƙa ɗan bijimi da raguna bakwai don yă tsarkake kansa, ya zama firist na gumaka ke nan, ba na Allah ba.10. “Gare mu kuwa, Ubangiji shi ne Allah, kuma ba mu yashe shi ba. Firistocin da suke bauta wa Ubangiji ’ya’yan Haruna maza ne, Lawiyawa ne kuwa suke taimakonsu.11. Kowace safiya da kowace yamma sukan miƙa hadayun ƙonawa da turare mai ƙanshi ga Ubangiji. Sukan shirya burodi a tsarkaken tebur mai tsabta, sukan kuma ƙuna fitilu a alkukai kowace yamma. Muna kiyaye ƙa’idodin Ubangiji Allahnmu. Amma ku kun yashe shi.12. Allah yana tare da mu; shi ne shugabanmu. Firistocinsa tare da ƙahoni za su busa kirarin yaƙi a kanku. Mutanen Isra’ila, kada ku yi yaƙi da Ubangiji Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”13. To, fa, Yerobowam ya aiki mayaƙa su zagaya daga baya, domin yayinda yake a gaban Yahuda, sai ’yan kwanto su kasance a bayansu.14. Yahuda ya juya sai ya ga cewa ana yaƙe su gaba da baya. Sai suka yi kuka ga Ubangiji. Firistoci suka busa ƙahoni15. mutanen Yahuda kuwa suka tā da kirarin yaƙi. Da ji kirarin yaƙi, Allah ya fatattake Yerobowam da dukan Isra’ila a gaban Abiya da Yahuda.16. Isra’ilawa suka gudu a gaban Yahuda, Allah kuwa ya bashe su a hannuwansu.17. Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila.18. Aka cinye mutanen Isra’ila a wannan lokaci, mutanen Yahuda kuwa suka yi nasara domin sun dogara ga Ubangiji Allah na kakanninsu.19. Abiya ya kori Yerobowam ya kuma ƙwace garuruwan Betel, Yeshana da Efron, tare da ƙauyukan da suke kewaye daga gare shi.20. Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.21. Amma Abiya ya ƙara ƙarfi. Ya auri mata goma sha huɗu, ya kuma kasance da ’ya’ya maza ashirin da biyu da kuma ’ya’ya mata goma sha shida.22. Sauran ayyukan sauratar Abiya, abin da ya yi da abin da ya faɗa, a rubuce suke a cikin rubuce-rubucen annabi Iddo.2 Tarihi 14:1-151. Abiya kuwa ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Asa ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki, a zamaninsa kuma ƙasar ta zauna lafiya na shekara goma.2. Asa ya yi abin da yake da kyau da kuma daidai a gaban Ubangiji Allahnsa.3. Ya kawar da baƙin bagade da masujadai bisa tudu, ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya kuma sassare ginshiƙan Ashera.4. Ya umarci Yahuda su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kuma yi biyayya da dokoki da kuma umarnansa.5. Ya kawar da masujadan kan tudu da bagadan turare a kowane gari a Yahuda, masarautar kuwa ta zauna lafiya a ƙarƙashinsa.6. Ya gina biranen katanga na Yahuda, da yake ƙasar tana zaman lafiya. Babu wanda yake yaƙi da shi a waɗannan shekaru, gama Ubangiji ya ba shi hutu.7. Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara.8. Asa ya kasance da mayaƙa dubu ɗari uku daga Yahuda, kintsatse da manyan garkuwoyi da māsu, da kuma mayaƙa dubu ɗari biyu da dubu tamanin daga Benyamin, riƙe da ƙananan garkuwoyi da kuma baka. Dukan waɗannan jarumawa ne ƙwarai.9. Zera mutumin Kush ya taka ya fita don yă yaƙe su da babban runduna da kuma kekunan yaƙi ɗari uku, ya kuma zo har Maresha.10. Asa ya fita don yă ƙara da shi, suka ja dāgā yaƙi a Kwarin Zefata kusa da Maresha.11. Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “ Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”12. Ubangiji fa ya bugi mutanen Kush a gaban Asa da Yahuda. Mutanen Kush suka gudu,13. Asa kuwa da mayaƙansa suka bi su har Gerar. Mutanen Kush suka mutu a ranan nan har ba a iya ƙidaya, aka buge su a gaban Ubangiji da rundunansa. Mutanen Yahuda suka kwashi ganima sosai.14. Suka hallaka dukan ƙauyukan kewaye da Gerar, gama tsoron Ubangiji ya kama su. Suka kwashi ganima na dukan ƙauyukan nan, da yake akwai ganima sosai a can.15. Suka kuma yaƙi sansanin makiyaya suka kwashe tumaki da awaki da raƙuma. Suka koma Urushalima.Zabura 81:1-51. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!2. Ku fara kaɗe-kaɗe, ku buga ganga, ku kaɗa garaya da molo masu daɗi.3. Ku busa ƙahon rago a Sabon Wata, da kuma sa’ad da wata ya kai tsakiya, a ranar Bikinmu;4. wannan ƙa’ida ce domin Isra’ila, farilla ta Allah na Yaƙub.5. Ya kafa shi a matsayin ƙa’ida domin Yusuf sa’ad da ya fito daga Masar. Muka ji yaren da ba mu fahimta ba.Karin Magana 20:22-2322. Kada ka ce, “Zan rama wannan abin da aka yi mini!” Ka dogara ga Ubangiji, zai kuwa fisshe ka.23. Ubangiji ya ƙi ma’aunin da ba daidai ba, da kuma magwajin da ba su gamshe shi ba.Ayyukan Manzanni 15:22-4122. Sai manzanni da dattawa, tare da dukan ikkilisiya, suka yanke shawara su zaɓi waɗansu daga cikin mutanensu su kuma aike su zuwa Antiyok tare da Bulus da Barnabas. Sai suka zaɓi Yahuda (wanda ake kira Barsabbas) da kuma Sila, mutum biyu da suke shugabanni cikin ’yan’uwa.23. Tare da su suka aika da wannan wasiƙa. Daga manzanni da dattawa, ’yan’uwanku. Zuwa ga Al’ummai masu bi a Antiyok, Suriya da Silisiya. Gaisuwa.24. Mun ji cewa, waɗansu da sun fita daga cikinmu ba tare da izininmu ba suka kuma dame ku, suna tā da hankalinku ta wurin abin da suka ce.25. Saboda haka dukanmu mun yarda mu zaɓi waɗansu mutane mu kuma aike su wurinku tare da ƙaunatattun abokanmu Barnabas da Bulus 26. mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.27. Saboda haka muna aika Yahuda da Sila don su tabbatar muku da baki abin da muka rubuta.28. Ya gamshe Ruhu Mai Tsarki da mu ma kada a ɗora muku nauyi fiye da na waɗannan abubuwa.29. Ku guji abincin da aka yi wa alloli hadaya, da jini, da naman dabbar da aka murɗe da kuma fasikanci. Za ku kyauta in kun kiyaye waɗannan abubuwa. Ku huta lafiya.30. Aka sallami mutanen sai suka gangara zuwa Antiyok, inda suka tara ikkilisiya wuri ɗaya suka ba da wasiƙar.31. Mutanen suka karantata suka kuma yi farin ciki saboda saƙonta mai ƙarfafawa.32. Yahuda da Sila, waɗanda su kansu annabawa ne, suka yi magana sosai don su gina su kuma ƙarfafa ’yan’uwa.33. Bayan suka yi ’yan kwanaki a can, sai ’yan’uwa suka sallame su da albarkar salama su dawo wurin waɗanda suka aike su. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.