Baibul a cikin shekara guda Agusta 11Ayuba 13:1-281. “Idanuna sun ga waɗannan duka, kunnuwana sun ji sun kuma gane.2. Abin da kuka sani, ni ma na sani; ba ku fi ni ba.3. Amma ina so in yi magana da Maɗaukaki, in kai kukana wurin Allah kai tsaye.4. Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!5. In da za ku yi shiru gaba ɗaya! Zai zama muku hikima.6. Ku ji gardamata yanzu; ku ji roƙon da zai fito daga bakina.7. Za ku iya yin muguwar magana a madadin Allah? Ko za ku yi ƙarya a madadinsa?8. Ko za ku nuna masa sonkai? Ko za ku yi gardama a madadinsa?9. In ya bincike ku zai tarar ba ku da laifi? Ko za ku iya ruɗe shi yadda za ku ruɗi mutane?10. Ba shakka zai kwaɓe ku in kun nuna sonkai a ɓoye.11. Ko ikonsa ba ya ba ku tsoro? Tsoronsa ba zai auka muku ba?12. Duk surutanku kamar toka suke; kāriyarku na yimɓu ne.13. “Ku yi shiru zan yi magana; sa’an nan abin da zai same ni yă same ni.14. Don me na sa kaina cikin hatsari na yi kasada da raina?15. Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa16. lalle wannan zai kawo mini kuɓuta gama ba wani marar tsoron Allah da zai iya zuwa wurinsa!17. Ku saurara da kyau ku ji abin da zan faɗa; bari kunnuwanku su ji abin da zan ce.18. Yanzu da na shirya ƙarata, na san za a ce ba ni da laifi.19. Ko wani zai ce ga laifin da na yi? In an same ni da laifi, zan yi shiru in mutu.20. “Kai dai biya mini waɗannan bukatu biyu kawai ya Allah, ba zan kuwa ɓoye daga gare ka ba;21. Ka janye hannunka nesa da ni, ka daina ba ni tsoro da bantsoronka.22. Sa’an nan ka kira ni, zan kuwa amsa, ko kuma ka bar ni in yi magana sai ka amsa mini.23. Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina.24. Don me ka ɓoye mini fuskarka; ka kuma sa na zama kamar maƙiyinka?25. Ko za a wahalar da ganye wanda iska take hurawa? Ko za ka bi busasshiyar ciyawa?26. Gama ka rubuta abubuwa marasa daɗi game da ni; ka sa na yi gādon zunuban ƙuruciyata.27. Ka daure ƙafafuna da sarƙa; kana kallon duk inda na taka ta wurin sa shaida a tafin ƙafafuna.28. “Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye.Ayuba 14:1-221. “Mutum haihuwar mace kwanakinsa kaɗan ne, kuma cike da wahala.2. Yana tasowa kamar fure yana kuma shuɗewa; kamar inuwa, ba ya daɗewa.3. Za ka zura ido a kan irin wannan ne? Za ka kawo shi gaba don ka yi masa shari’a?4. Wane ne zai iya kawo abin da yake da tsarki daga cikin abu marar tsarki? Babu!5. An lissafta kwanakin mutum; ka riga ka ɗibar masa watanni, ka yi masa iyaka, ba zai iya wuce iyakar ba.6. Saboda haka ka kawar da kanka daga gare shi, ka rabu da shi har sai ya cika lokacinsa kamar mutumin da aka ɗauki hayarsa.7. “Aƙalla itace yana da bege. In an sare shi, zai sāke tsira, zai tohu da kyau.8. Ko da jijiyoyin itacen sun tsufa a cikin ƙasa kuma kututturensa ya mutu a cikin ƙasa.9. Daga ya ji ƙanshin ruwa zai tohu yă yi tsiro kamar shuka.10. Amma mutum yana mutuwa a bizne shi; daga ya ja numfashinsa na ƙarshe, shi ke nan.11. Kamar yadda ruwa yake bushewa a teku ko a gaɓar rafi sai wurin yă bushe,12. haka mutum zai kwanta ba zai tashi ba; har sai duniya ta shuɗe mutane ba za su farka ba, ba za su tashi daga barcinsu ba.13. “Da ma za ka ɓoye ni a cikin kabari ka ɓoye ni har sai fushinka ya wuce! In da za ka keɓe mini lokaci sa’an nan ka tuna da ni!14. In mutum ya mutu, ko zai sāke rayuwa? In haka ne zan daure kwanakin da nake shan wahala har su wuce.15. Za ka kira zan kuwa amsa maka; za ka yi marmarin abin da hannunka ya halitta.16. Ba shakka a lokacin ne za ka lura da matakaina amma ba za ka kula da zunubaina ba.17. Za a daure laifofina a cikin jaka; za ka rufe zunubaina.18. “Amma kamar yadda manyan duwatsu suke fāɗuwa su farfashe su kuma gusa daga wurarensu,19. yadda ruwa yakan zaizaye duwatsu ruwa mai ƙarfi kuma yă kwashe turɓayar ƙasa, haka kake barin mutum ba bege.20. Ka sha ƙarfinsa gaba ɗaya, sai ya ɓace, ka sauya yanayinsa ka kuma kore shi.21. Ko an martaba ’ya’yansa maza, ba zai sani ba; Ko an wulaƙanta su, ba zai gani ba.22. Zafin jikinsa kaɗai yake ji yana kuka wa kansa ne kaɗai.”Zabura 94:12-1912. Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;13. kana ba shi sauƙi a lokacin wahala, sai har an haƙa rami wa mugaye.14. Gama Ubangiji ba zai ƙi mutanensa ba; ba zai taɓa yashe gādonsa ba.15. Za a sāke kafa hukunci a kan adalci, kuma dukan masu adalci a zuciya za su bi shi.16. Wane ne zai yi gāba da mugaye domina? Wane ne zai ɗauki matsayi ya yi gāba da masu aikata mugunta domina?17. Da ba don Ubangiji ya yi mini taimako ba, da tuni na zauna shiru a wurin mutuwa.18. Sa’ad da na ce, “Ƙafata na santsi,” ƙaunarka, ya Ubangiji, ta riƙe ni.19. Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.Karin Magana 22:26-2726. Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi;27. gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.Romawa 11:1-181. To, ina da tambaya. Allah ya ƙi mutanensa ne? Sam, ko kaɗan! Ni mutumin Isra’ila ne kaina, zuriyar Ibrahim kuwa, daga kabilar Benyamin.2. Allah bai ƙi mutanensa da ya rigya sani ba. Ba ku san abin da Nassi ya faɗa game da Iliya ba, yadda ya kawo kuka ga Allah a kan Isra’ila ya ce,3. “Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”?4. Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.”5. Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri.6. In kuwa na alheri ne, ba sauran cewa ya dogara ga ayyuka ke nan. In ba haka ba, ashe, alheri ba alheri ba ne kuma.7. To, sai me? Abin da Isra’ila suka nema da himma ba su samu ba, amma zaɓaɓɓun suka samu. Sauran suka taurare,8. kamar yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yă zuwa yau.”9. Dawuda kuma ya ce, “Bari teburin cin abincinsu yă zama musu tarko, sanadin fāɗuwa da dutsen sa tuntuɓe da kuma ramuwa a kansu.10. Bari idanunsu su duhunta don kada su iya gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.”11. Har yanzu ina da tambaya. Sun yi tuntuɓe har ya kai ga fāɗuwar da ba za su iya tashi ba ne? Sam, ko kaɗan! A maimako, saboda laifinsu ne ceto ya zo ga Al’ummai don a sa mutanen Isra’ila su ji kishi.12. Amma in laifinsu yana nufin albarka ga duniya, hasararsu kuma albarka ga Al’ummai, ina misalin yalwar da albarkunsu za su kawo!13. Ina magana da ku ne fa Al’ummai. Tun da yake ni manzo ne ga Al’ummai, ina taƙama da aikin nan nawa,14. da fata zan rura kabilata a ta kowace hanya su ji kishi har ma yă sa in ceci waɗansunsu.15. Gama in ƙinsu da aka yi ya zama sulhu ga duniya, me karɓarsu za tă zama in ba rai daga matattu ba?16. In sashen da aka miƙa a matsayin nunan fari tsattsarka ne, to, sauran ma tsattsarka ne; in saiwar tsattsarka ce, to, sauran rassan ma tsattsarka ne.17. In an sassare waɗansu rassa, kai kuwa da kake kai zaitun jeji, aka ɗauke ka aka kuma yi muku aure, a yanzu kuwa kana shan ni’imar saiwar zaitun ɗin nan tare da sauran rassan,18. kada ka yi taƙama cewa ka fi waɗancan rassan da aka sassare. In kuwa ka yi haka, to, ka yi la’akari da wannan. Ba kai ne kake taimakon saiwar ba, saiwar ce take taimakonka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.