Baibul a cikin shekara guda Agusta 12Ayuba 15:1-351. Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,2. “Mutum mai hikima zai amsa da surutai marasa kan gado ko yă cika cikinsa da iskar gabas?3. Ko zai yi gardama da maganganun wofi maganganu marasa amfani?4. Amma ka ma rena Allah ka hana a yi addu’a gare shi.5. Zunubanka ne suke gaya maka abin da za ka ce; kana magana kamar mai wayo.6. Bakinka zai kai ka yă baro, ba nawa ba; maganar bakinka za tă juya a kanka.7. “Kai ne mutum na farko da aka fara haihuwa? Ko kai ne aka fara halitta kafin tuddai?8. Kana sauraron shawarar Allah? Ko kana gani kai kaɗai ne mai hikima?9. Me ka sani da ba mu sani ba? Wane fahimi kake da shi da ba mu da shi?10. Masu furfura da tsofaffi suna gefenmu mutanen da sun girme babanka.11. Ta’aziyyar Allah ba tă ishe ka ba. Maganarsa mai laushi ba tă ishe ka ba?12. Don me ka bar zuciyarka ta kwashe ka, kuma don me idanunka suke haske,13. har kake fushi da Allah kake kuma faɗar waɗannan maganganu daga bakinka?14. “Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki, ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?15. In Allah bai nuna amincewa ga tsarkakansa ba, in har sammai ba su da tsarki a idonsa,16. mutum fa, wanda yake da mugunta da lalacewa, wanda yake shan mugunta kamar ruwa!17. “Ka saurare ni, zan kuma yi maka bayani; bari in gaya maka abin da na gani,18. abin da masu hikima suka ce, ba tare da sun ɓoye wani abu da suka samu daga wurin iyayensu ba19. (waɗanda su ne masu ƙasar kafin baƙi su shigo ƙasar).20. Dukan kwanakin ransa mugu yana shan wahala, wahala kaɗai zai yi ta sha.21. Ƙara mai bantsoro za tă cika kunnuwansa ’yan fashi za su kai masa hari.22. Yana jin tsoron duhu domin za a kashe shi da takobi.23. Yana ta yawo, abinci don ungulaye; ya san ranar duhu tana kusa.24. Ɓacin rai da baƙin ciki sun cika shi, kamar sarkin da yake shirin yaƙi,25. domin ya nuna wa Allah yatsa ya rena Allah Maɗaukaki,26. ya tasar masa da faɗa da garkuwa mai kauri da kuma ƙarfi.27. “Ko da yake fuskarsa ta cika da kumatu kuma yana da tsoka ko’ina,28. zai yi gādon garuruwan da suka lalace, da kuma gidajen da ba wanda yake zama a ciki, gidajen da sun zama tarkace.29. Ba zai sāke zama mai arziki ba, dukiyarsa ba za tă dawwama ba, abin da ya mallaka kuma ba zai bazu a ƙasar ba.30. Ba zai tsere wa duhu ba; wuta za tă ƙona rassansa, kuma numfashi daga bakin Allah zai hallaka shi.31. Kada yă ruɗi kansa ta wurin dogara ga abin da ba shi da amfani domin ba zai samu wani abu ba daga ciki.32. Kafin lokacinsa yă cika, za a gama biyansa duka, kuma rassansa ba za su ba da amfani ba.33. Zai zama kamar itacen inabi wanda ’ya’yansa suka kakkaɓe kafin su nuna, kamar itacen zaitun zai zubar da furensa.34. Gama marasa tsoron Allah za su zama marasa ba da ’ya’ya, wuta kuma za tă ƙona tenti na masu son cin hanci.35. Suna yin cikin rikici su kuma haifi mugunta; cikinsu yana cike da ruɗami.”Ayuba 16:1-221. Sai Ayuba ya amsa,2. “Na ji abubuwa da yawa kamar waɗannan; dukanku ba ku iya ta’aziyya ba!3. Dogayen surutanku ba sa ƙare ne? Me yake sa kuke ta yin waɗannan surutai har kuke cin gaba da yin gardama?4. Ni ma zan iya yin maganganu kamar yadda kuke yi in da kuna cikin halin da nake; zan iya faɗar duk abubuwan da kuke faɗi, in kaɗa muku kaina.5. Amma bakina zai ƙarfafa ku; ta’aziyyar da za tă fito daga bakina za tă kawar muku da ɓacin zuciyarku.6. “Duk da haka in na yi magana, ba na samun sauƙi; in ma na yi shiru zafin ba ya tafiya.7. Ba shakka ya Allah ka gajiyar da ni; ka ɓata gidana gaba ɗaya.8. Ka daure ni, ya kuma zama shaida; yadda na rame sai ƙasusuwa, wannan ya sa ake gani kamar don ni mai zunubi ne shi ya sa.9. Allah ya kai mini hari ya yi kaca-kaca da ni cikin fushinsa yana cizon haƙoransa don fushin da yake yi da ni; ya zura mini ido.10. Mutane suka buɗe baki suka yi mini riyar reni; suka yi mini ba’a suka haɗu suka tayar mini.11. Allah ya bashe ni ga mugayen mutane, ya jefa ni hannun mugaye.12. Dā ina zamana lafiya kome yana tafiya daidai; amma ya ragargaza ni; ya shaƙe ni a wuya; ya murƙushe ni na zama abin barata gare shi;13. maharbansa sun kewaye ni. Ba tausayi, ya soke ni a ƙodata har jini ya zuba a ƙasa.14. Ya ji mini rauni a kai a kai ya auko mini kamar mai yaƙi.15. “Ina makoki saye da tsummoki na ɓoye fuskata a cikin ƙura.16. Fuskata ta yi ja don kuka idanuna sun kukumbura;17. duk da haka hannuwana ba su aikata ɓarna ba kuma addu’ata mai tsabta ce.18. “Ya duniya, kada ki ɓoye jinina; bari yă yi kuka a madadina!19. Ko yanzu haka shaidata tana sama; wanda zai tsaya mini yana sama.20. Shi mai yin roƙo a madadina abokina ne yayinda nake kuka ga Allah;21. a madadin mutum ya yi roƙo ga Allah kamar yadda mutum yakan yi roƙo domin abokinsa.22. “Shekaru kaɗan suka rage in kama hanyar da ba a komawa.Zabura 94:20-2320. Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar?21. Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa.22. Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.23. Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.Karin Magana 22:28-2928. Kada ka matsar da shaidar kan iyakar da kakanninka suka kafa.29. Kana ganin mutumin da yake da gwaninta a cikin aikinsa? Zai yi wa sarakuna hidima; ba zai yi hidima wa mutanen da ba su iya ba.Romawa 11:19-3619. To, kana iya cewa, “An sassare rassan ne don a ɗaura aure da ni.”20. Haka yake. Amma an sassare su ne saboda rashin bangaskiya, kai kuma kana tsaye ta wurin bangaskiya. Kada ka yi taƙama, sai dai ka ji tsoro.21. Gama in har Allah bai bar rassan nan na asali ba, kai ma ba zai bar ka ba.22. Ka lura fa da alheri da kuma tsananin Allah, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, amma alheri a gare ka, da fata za ka ci gaba cikin alherinsa. In ba haka ba, kai ma za a sare ka.23. In kuwa ba su nace cikin rashin bangaskiya ba, za a sāke ɗaura aure da su, domin Allah yana iya sāke haɗa su.24. Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?25. Ba na so ku kasance cikin rashin sani game da wannan asirin ’yan’uwa, domin kada ku ɗaga kai. Isra’ila sun ɗanɗana sashe na taurarewa har sai da shigowar Al’ummai masu yawa ya cika.26. Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.27. Wannan kuwa shi ne alkawarina da su sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”28. Game da zancen nan na bishara kuwa, su abokan gāba ne saboda ku; amma game da zaɓen kuwa, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu,29. gama kyautar Allah da kiransa ba a sokewa.30. Kamar yadda a dā can ku da kuke marasa biyayya ga Allah kuka sami jinƙai yanzu ta dalilin rashin biyayyarsu,31. haka su ma suka zama marasa biyayya a yanzu domin su ma su sami jinƙai ta dalilin jinƙan da Allah ya yi muku.32. Gama Allah ya daure dukan mutane ga rashin biyayya don yă nuna jinƙai ga kowa.33. Kai, zurfin yalwar hikima da kuma sanin Allah yana nan a yalwace! Hukunce-hukuncensa kuma su fi gaban bincike, hanyoyinsa kuwa sun wuce gaban ganewa!34. “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji? Ko kuwa yă ba shi shawara?”35. “Wa ya taɓa ba wa Allah wani abu, da Allah zai sāka masa?”36. Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.