Baibul a cikin shekara guda Agusta 13Ayuba 17:1-161. Na karaya, kwanakina sun kusa ƙarewa, kabari yana jirana.2. Ba shakka masu yi mini ba’a suna kewaye da ni; idanuna suna ganin tsokanar da suke yi mini.3. “Ya Allah, ka ba ni abin da ka yi mini alkawari. Wane ne zai kāre ni?4. Ka rufe zuciyarsu yadda ba za su iya ganewa ba, saboda haka ba za ka bari su yi nasara ba.5. In mutum ya juya wa abokansa baya don a ba shi wata lada ’ya’yansa za su makance.6. “Allah ya sa na zama abin da kowa yake magana a kai wanda kowa yake tofa wa miyau a fuska.7. Idanuna ba sa gani sosai don baƙin ciki; jikina ya zama kamar inuwa kawai8. Mutanen da suke masu adalci wannan abu ya ba su tsoro; marasa laifi sun tayar wa marasa tsoron Allah.9. Duk da haka, masu adalci za su ci gaba da tafiya a kan hanyarsu, waɗanda hannuwansu suke da tsabta kuma za su ƙara ƙarfi.10. “Amma ku zo dukanku, ku sāke gwadawa! Ba zan sami mutum ɗaya mai hikima ba a cikinku.11. Kwanakina sun wuce, shirye-shiryena sun ɓaci haka kuma abubuwan da zuciyata take so.12. Mutanen nan sun juya rana ta zama dare. A tsakiyar duhu suka ce, ‘Haske yana kusa.’13. In kabari ne begen da nake da shi kaɗai, in na shimfiɗa gadona a cikin duhu,14. In na ce wa kabari, ‘Kai ne mahaifina,’ tsutsa kuma ke ce, ‘Mahaifiyata’ ko ‘’yar’uwata,’15. To, ina begena yake? Wane ne zai iya ganin wani bege domina?16. Ko begena zai tafi tare da ni zuwa kabari ne? Ko tare za a bizne mu cikin ƙura?”Ayuba 18:1-211. Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,2. “Yaushe za ka gama maganganun nan? Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.3. Don me muke kamar shanu a wurinka, ka ɗauke mu mutanen wofi?4. Kai da ka yayyage kanka don haushi, za a yashe duniya saboda kai ne? Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?5. “An kashe fitilar mugu; harshen wutarsa ya daina ci.6. Wutar cikin tentinsa ta zama duhu; fitilar da take kusa da shi ta mutu.7. Ƙarfin takawarsa ya ragu; dabararsa ta ja fāɗuwarsa.8. Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.9. Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam.10. An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.11. Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je.12. Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.13. Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.14. An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai.15. Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama.16. Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama.17. An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi.18. An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya.19. Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.20. Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas.21. Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”Zabura 95:1-51. Ku zo, bari mu rera don farin ciki ga Ubangiji; bari mu yi sowa da ƙarfi ga Dutsen cetonmu.2. Bari mu zo gabansa da godiya mu rera gare shi da kiɗi da waƙa.3. Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli.4. A hannunsa ne zurfafan duniya suke, ƙwanƙolin dutse kuma nasa ne.5. Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa.Karin Magana 23:1-31. Sa’ad da ka zauna domin cin abinci da mai mulki, ka lura sosai da abin da yake gabanka,2. ka kuma sa wuƙa a maƙogwaronka in kai mai ci da yawa ne.3. Kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi gama wannan abinci ruɗu ne.Romawa 12:1-211. Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.2. Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.3. Gama ta wurin alherin nan da aka yi mini ne ina ce wa kowannenku. Kada yă ɗauki kansa fiye da yadda ya kamata, a maimakon haka bari yă auna kansa cikin natsuwa, gwargwadon baiwar bangaskiyar da Allah yi masa.4. Kamar dai yadda kowannenmu yake da jiki ɗaya da gaɓoɓi da yawa, gaɓoɓin nan kuwa ba aiki iri ɗaya suke yi ba,5. haka ma a cikin Kiristi mu da muke da yawa mun zama jiki ɗaya, kuma kowace gaɓar ɗan’uwan sauran ne.6. Muna da baye-baye dabam-dabam, gwargwadon alherin da aka yi mana. In baiwar mutum ta yin annabci ce, sai yă yi amfani da ita gwargwadon bangaskiyarsa.7. In ta hidima ce; sai yă yi hidima. In kuma ta koyarwa ce, sai yă koyar;8. in ta ƙarfafawa ce, sai yă ƙarfafa; in kuma ta ba da taimako ce don biyan bukatun waɗansu, sai yă yi haka hannu sake; in ta shugabanci ce, sai yă yi shugabanci da himma; in ta nuna jinƙai ce, sai yă yi haka da fara’a.9. Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.10. Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.11. Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.12. Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a.13. Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi.14. Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.15. Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.16. Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna girman kai, sai ma ku riƙa cuɗanya da talakawa. Kada ku zama masu ɗaga kai.17. Idan kowa ya yi muku mugunta, kada ku sāka masa da mugunta. Ku lura don ku aikata abin da kowa zai iya gani cewa daidai ne.18. Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa.19. Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.20. A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”21. Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.