Baibul a cikin shekara guda Agusta 14Ayuba 19:1-291. Sai Ayuba ya amsa,2. “Har yaushe za ku yi ta ba ni azaba ku kuma murƙushe ni da maganganunku?3. Yanzu sau goma ke nan kuna wulaƙanta ni, kuna kai mini hari na rashin kunya.4. In gaskiya ne na yi laifi, kuskurena ya rage nawa.5. In kuwa za ku ɗaukaka kanku a kaina kuna ɗauka wahalar da nake sha domin na yi laifi ne,6. sai ku san cewa Allah ya yi mini ba daidai ba ya kewaye ni da ragarsa.7. “Ko da yake na yi kuka cewa, ‘An yi mini ba daidai ba!’ Ba a amsa mini ba; ko da yake na nemi taimako, ba a yi adalci ba.8. Ya tare mini hanya yadda ba zan iya wucewa ba; ya rufe hanyata da duhu.9. Ya cire darajar da nake da ita, ya kuma cire rawani daga kaina.10. Ya yi kaca-kaca da ni har sai da na ƙare; ya tuge begen da nake da shi kamar itace.11. Yana jin haushina ya lissafta ni cikin maƙiyansa.12. Rundunarsa ta zo da ƙarfi; suka kafa sansani kewaye da ni, suka zagaye tentina.13. “Ya raba ni da ’yan’uwana maza; abokaina sun zama baƙi gare ni.14. Dangina sun tafi; abokaina na kurkusa sun manta da ni.15. Waɗanda sukan ziyarce ni, da masu yi mini aiki mata sun ɗauke ni baƙo.16. Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.17. Numfashina yana ɓata wa matata rai; ’yan’uwana sun ƙi ni.18. Har ’yan yara suna rena ni; in sun gan ni sai su fara yi mini riyar reni.19. Duk abokaina sun yashe ni; waɗanda nake ƙauna sun zama ba sa ƙaunata.20. Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira.21. “Ku tausaya mini, abokaina, ku ji tausayina, gama hannun Allah ya sauko a kaina.22. Don me kuke fafarata kamar yadda Allah yake yi? Ba ku gaji da yagar fatata ba?23. “Kash, da ma a ce ana rubuta maganganuna, da an rubuta su a littafi,24. a rubuta su da ƙarfe a kan dutse don su dawwama har abada!25. Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.26. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.27. Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!28. “In kuka ce, ‘Za ku ci gaba da matsa mini, tun da shi ne tushen damuwa,’29. sai ku ma ku ji tsoron takobin; gama fushi yakan kawo hukunci ta wurin takobi, sa’an nan za ku san cewa akwai shari’a.”Ayuba 20:1-291. Sai Zofar mutumin Na’ama ya amsa,2. “Tunanin da ya dame ni ya sa dole in amsa domin abin ya dame ni sosai.3. Na ji wani zargin da ka yi mini na reni, kuma yadda na gane, shi ya sa zan ba da amsa.4. “Ba shakka ka san yadda abin yake tuntuni, tun da aka sa mutum cikin duniya,5. mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.6. Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama, kansa kuma yana taɓa gizagizai.7. Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa; waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’8. Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba zai ɓace kamar wahayi da dare.9. Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba; wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.10. Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.11. Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura.12. “Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa,13. ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa,14. duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.15. Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.16. Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.17. Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.18. Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.19. Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.20. “Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba.21. Ba abin da ya ragu da zai ɗauka; arzikinsa ba zai dawwama ba.22. Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa; ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.23. Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi.24. Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe, kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.25. Zai zāre ta daga bayansa, tsinin zai fita daga hantarsa; tsoro zai cika shi;26. duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.27. Sammai za su fallasa laifinsa; duniya za tă yi gāba da shi.28. Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.29. Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.”Zabura 95:6-116. Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;7. gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,8. “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,9. inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.10. Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’11. Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”Karin Magana 23:4-54. Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa.5. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.Romawa 13:1-141. Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne.2. Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci.3. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka.4. Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.5. Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku.6. Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci.7. Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.8. Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.9. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”10. Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.11. Ku yi wannan domin kun san irin zamanin da kuke ciki. Lokaci ya yi da za ku farka daga barcinku, don cetonmu ya yi kusa yanzu fiye da lokacin da muka fara ba da gaskiya.12. Dare fa ya kusan ƙarewa; gari kuma yana gab da wayewa. Saboda haka bari mu kawar da ayyukan duhu mu kuma yafa kayan yaƙi na haske.13. Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba.14. A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.