Baibul a cikin shekara guda Agusta 15Ayuba 21:1-341. Sai Ayuba ya amsa,2. “Ku saurare ni da kyau; bari wannan yă zama ta’aziyyar da za ku ba ni.3. Ku ba ni zarafi in yi magana, bayan na gama sai ku yi ba’arku.4. “A wurin mutum ne na kawo kukana? Don me ba zan kāsa haƙuri ba?5. Ku dube ni, ku kuma yi mamaki; ku rufe bakina da hannunku.6. Lokacin da na yi tunanin wannan, sai in ji tsoro; jikina yă fara rawa.7. Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa, suna kuma ƙaruwa da iko?8. Suna ganin ’ya’yansu suna girma, suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.9. Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo.10. Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari.11. Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.12. Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.13. Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.14. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.15. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?16. Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.17. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?18. Sau nawa suke zama kamar tattaka a iska, ko kuma kamar ƙura da iskar hadari take kwashewa?19. An ce ‘Allah yana tara wa ’ya’yan mutum horon da zai ba mutumin.’ Bari yă ba mutumin horo don yă san ya yi haka!20. Bari idanunsa su ga yadda zai hallaka; bari yă sha daga fushin Maɗaukaki.21. Ko zai damu da iyalin da ya bari a baya sa’ad da kwanakinsa suka ƙare?22. “Wani zai iya koya wa Allah ilimi tun da yana shari’anta har da waɗanda suke manya masu iko?23. Wani mutum zai mutu cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,24. jikinsa ɓulɓul, ƙasusuwansa da alamar ƙarfi.25. Wani kuma zai mutu cikin ɗacin rai, bai taɓa jin daɗin wani abu mai kyau ba.26. Dukansu kuwa za a bizne su a ƙasa, kuma tsutsotsi za su cinye su.27. “Na san duk abin da kuke tunani, yadda za ku saɓa mini.28. Kuna cewa, ‘Yanzu ina gidan babban mutumin nan, tenti wurin da mugaye suke zama?’29. Ba ku taɓa tambayar waɗanda suke tafiya ba? Ba ku kula da labaransu,30. cewa an kāre mugu daga ranar bala’i, an kāre shi daga ranar fushi?31. Wane ne yake gaya masa abin da ya yi? Wane ne yake rama abin da ya yi?32. Za a bizne shi a kabari, a kuma yi tsaron kabarinsa.33. Akan mai da ƙasa a kan gawarsa a hankali; dukan jama’a suna binsa, da yawa kuma suna gabansa.34. “Saboda haka ta yaya za ku iya yi mini ta’aziyya da surutan banzan nan naku? Babu wani abu cikin amsarku sai ƙarya!”Ayuba 22:1-301. Sai Elifaz mutumin Teman ya amsa,2. “Mutum yana iya zama da amfani a wurin Allah? Mai hikima ma zai iya zama da amfani a wurin shi?3. Wane daɗi Allah zai ji in kai mai adalci ne? Wace riba zai samu in rayuwarka marar laifi ce?4. “Ko don kana tsoron Allah shi ya sa ya kwaɓe ka ya kuma bari haka yă same ka?5. Ba muguntarka ce ta yi yawa ba? Ba zunubanka ne ba iyaka ba?6. Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara.7. Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.8. Ko da yake kai mai ƙarfi ne, ka mallaki ƙasa, mutum mai martaba kuma, kana zama cikin ƙasarka.9. Ka kori gwauraye hannu wofi, ka kuma karya ƙarfin marayu.10. Shi ya sa kake kewaye da tarkuna, shi ya sa ka cika da tsoron mugun abin da zai auko maka.11. An yi duhu ƙwarai, har ba ka iya gani, shi ya sa ambaliyar ruwa ta rufe ka.12. “Ba Allah ne a can sama ba? Dubi yadda taurarin sama suke can nesa a sama!13. Duk da haka ka ce, ‘Me Allah ya sani? A cikin duhu ne yake shari’a?14. Gajimare ya rufe shi, saboda haka ba ya ganinmu lokacin da yake takawa a cikin sammai.’15. Za ka ci gaba da bin tsohuwar hanyar da mugayen mutane suka bi?16. An ɗauke su kafin lokacinsu yă cika, ruwa ya share tushensu.17. Suka ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu! Me Maɗaukaki zai yi mana?’18. Duk da haka kuwa shi ne ya cika gidajensu da abubuwa masu kyau, saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.19. “Masu adalci suna gani ana hallaka mugaye, suna jin daɗi; marasa laifi suna yi musu ba’a, suna cewa,20. ‘Ba shakka an hallaka maƙiyanmu, wuta kuma ta ƙona dukiyarsu.’21. “Ka miƙa kanka ga Allah ka samu salamarsa; ta haka ne arziki zai zo maka.22. Ka bi umarnin da zai fito daga bakinsa kuma ka riƙe maganarsa a cikin zuciyarka.23. In ka komo ga Maɗaukaki, za ka warke. In ka kawar da mugunta daga cikin gidanka.24. Ka jefar da zinariyarka a ƙasa, ka jefar da zinariyar Ofir da ka fi so a cikin duwatsu,25. sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.26. Ba shakka a lokacin ne za ka sami farin ciki daga wurin Maɗaukaki, ku kuma ɗaga idanunku ga Allah27. Za ka yi addu’a zuwa gare shi, zai kuwa ji ka, kuma za ka cika alkawuranka.28. Abin da ka zaɓa za ka yi za ka yi nasara a ciki, haske kuma zai haskaka hanyarka.29. Sa’ad da aka ƙasƙantar da mutane ka kuma ce, ‘A ɗaga su!’ Sa’an nan zai ceci masu tawali’u.30. Zai ceci wanda ma yake mai laifi, wanda zai tsirar da shi ta wurin tsabtar hannuwanka.”Zabura 96:1-61. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji; ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka.2. Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana.3. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.4. Gama da girma Ubangiji yake, ya kuma cancanci yabo; tilas a ji tsoronsa fiye da dukan alloli.5. Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne, amma Ubangiji ne ya yi sammai.6. Daraja da ɗaukaka suna a gabansa; ƙarfi da ɗaukaka suna a cikin tsarkakar wurinsa.Karin Magana 23:6-86. Kada ka ci abincin mai rowa, kada ka yi marmarin abincinsa mai daɗi;7. gama shi wani irin mutum ne wanda kullum yana tunani game da tsadar abincin. Zai ce maka, “Ci ka sha,” amma zuciyarsa ba ta tare da kai.8. Za ka yi amai ɗan abin da ka ci dukan daɗin bakinka kuwa zai tafi a banza.Romawa 14:1-231. Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba.2. Bangaskiyar mutum ta yarda masa yă ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai.3. Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada yă rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada yă ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi.4. Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yă yi aiki mai kyau, ko yă kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.5. Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa yă kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa.6. Wannan mai ɗaukan rana ɗaya da muhimmanci fiye da sauran, yana yin haka ne ga Ubangiji. Wannan mai cin nama, yana yin haka ne ga Ubangiji, gama yakan yi godiya ga Allah; wannan da ba ya ci kuwa, yana yin haka ne ga Ubangiji yana kuwa yin godiya ga Allah.7. Gama ba waninmu da yake rayuwa wa kansa kaɗai, kuma ba waninmu da kan mutu don kansa kaɗai.8. In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne.9. Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai.10. Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah.11. A rubuce yake cewa, “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ”12. Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.13. Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yă yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.14. A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne.15. In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa.16. Kada ka bar abin da ka ɗauka a matsayi kyakkyawa yă zama abin zargi ga waɗansu.17. Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,18. duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.19. Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.20. Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe.21. Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.22. Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba.23. Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.