Baibul a cikin shekara guda Agusta 17Ayuba 26:1-141. Sai Ayuba ya amsa,2. “Yadda ka taimaki marar ƙarfi! Yadda ka ceci marar ƙarfi!3. Ka ba marar hikima shawara! Ka nuna kana da ilimi sosai.4. Wane ne ya taimake ka ka yi waɗannan maganganu? Kuma ruhun wane ne ya yi magana ta bakinka?5. “Matattu suna cikin azaba, waɗanda suke ƙarƙashin ruwaye da dukan mazauna cikin ruwaye.6. Mutuwa tsirara take a gaban Allah; haka kuma hallaka take a buɗe.7. Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba.8. Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba.9. Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi,10. ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske.11. Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.12. Da ikonsa ya kwantar da teku; da hikimarsa ya hallaka dodon ruwan nan Rahab.13. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.14. Waɗannan kaɗan ke nan daga cikin ayyukansa masu yawa. Kaɗan kawai muke ji game da shi! Wane ne kuwa yake iya gane tsawar ikonsa?”Zabura 96:11-1311. Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna; bari teku tă yi ruri, da kuma dukan abin da yake cikinsa;12. bari gonaki su yi tsalle da murna, da kuma kome da yake cikinsu. Ta haka dukan itatuwan kurmi za su rera don farin ciki;13. za su rera a gaban Ubangiji, gama yana zuwa, yana zuwa don yă hukunta duniya. Zai hukunta duniya cikin adalci mutane kuma cikin amincinsa.Karin Magana 23:10-1210. Kada ka kawar da shaidar iyaka ta dā ko ka ɗiba gonar marayu,11. gama mai Kāriyarsu yana da ƙarfi; zai kuwa yi magana dominsu.12. Ka mai da hankali ga umarni ka kuma kasa kunne ga kalmomin sani.Romawa 15:25-3325. Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudummawa ga tsarkaka a can.26. Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudummawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima.27. Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Al’ummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya.28. Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata.29. Na san cewa sa’ad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.30. Ina roƙonku ’yan’uwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin addu’a ga Allah saboda ni.31. Ku yi addu’a don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudummawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can,32. don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku.33. Allah na salama yă kasance tare da ku duka. Amin. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.