Baibul a cikin shekara guda Agusta 18Ayuba 27:1-231. Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,2. “Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.3. Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,4. bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.5. Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.6. Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.7. “Bari maƙiyana su zama kamar mugaye, masu gāba da ni kuma su zama kamar marasa adalci.8. Gama wane bege marar tsoron Allah yake da shi, lokacin da aka datse shi, lokacin da Allah ya ɗauke ransa?9. Ko Allah yana sauraron kukansa lokacin da ƙunci ya auko masa?10. Ko zai sami farin ciki daga Maɗaukaki? Ko zai yi kira ga Allah a kowane lokaci?11. “Zan koya muku game da ikon Allah; ba zan ɓoye hanyoyin Maɗaukaki ba.12. Duk kun ga wannan ku da kanku saboda haka me ya sa kuke maganganun nan marasa ma’ana?13. “Ga abin da mugaye za su samu gādon da azzalumi zai samu daga Maɗaukaki.14. Kome yawan ’ya’yansa, takobi za tă gama da su; zuriyarsa ba za su taɓa samun isashen abinci ba.15. Waɗanda suka tsira annoba za tă kashe su, kuma gwaurayensu ba za su yi kukan mutuwarsu ba.16. Ko da yake ya tara azurfa kamar ƙasa, tufafi kuma kamar tarin ƙasa,17. abin da ya tara masu adalci za su sa marasa laifi za su raba azurfarsa.18. Gidan da ya gina kamar gidan gizo-gizo, kamar bukkar mai tsaro.19. Attajiri zai kwanta, amma daga wannan shi ke nan; lokacin da zai buɗe idanunsa, kome ya tafi.20. Tsoro zai kwashe shi kamar ambaliyar ruwa; Da dare iska za tă tafi da shi.21. Iskar gabas za tă tafi da shi; shi ke nan ya ƙare; za tă share shi daga wurinsa.22. Za tă murɗe shi ba tausayi, lokacin da yake guje wa ikon iskar.23. Zai tafa hannu yă yi tsaki yă kawar da shi daga wurinsa.”Ayuba 28:1-281. Akwai ramin azurfa akwai kuma wurin da ake tace zinariya.2. Daga cikin ƙasa ake ciro ƙarfe, ana kuma narkar da tagulla daga cikin dutse.3. Mutum ya kawo ƙarshen duhu; yakan bincike zuzzurfar iyaka, yana neman duwatsu a wuri mafi duhu.4. Nesa da inda mutane suke zama, yakan huda rami yă yi abin lilo, a wurin da mutane ba sa bi.5. Cikin ƙasa inda ake samun abinci, a ƙarƙashinta kuwa zafi ne kamar wuta;6. akwai duwatsu masu daraja a cikin duwatsunta, akwai kuma zinariya a cikin ƙurarta.7. Tsuntsu mai farauta bai san hanyarta ba, ba shahon da ya taɓa ganin ta.8. Manyan namun jeji ba su taɓa binta ba, ba zakin da ya taɓa binta.9. Hannun mutum ya iya sarrafa ƙanƙarar duwatsu, yă kuma tumɓuke tushen duwatsu.10. Yana tona rami a cikin duwatsu idanunsa suna ganin dukan dukiyar da ke cikin duwatsun.11. Yana nema daga ina ruwan rafi yake ɓulɓulowa yana kuma binciko abubuwan da suke a ɓoye yă kawo su cikin haske.12. Amma a ina ne za a iya samun hikima? Ina fahimta take zama?13. Mutum bai gane muhimmancinta ba, ba a samunta a ƙasar masu rai.14. Zurfi ya ce, “Ba ta wurina”; teku ya ce, “Ba ta wurina.”15. Ba irin zinariyar da za tă iya sayenta, ko kuma a iya auna nauyinta da azurfa.16. Ba za a iya sayenta da zinariyar Ofir, ko sauran duwatsu masu daraja ba.17. Zinariya da madubi ba za su iya gwada kansu da ita ba, ba kuwa za a iya musayarta da abubuwan da aka yi da zinariya ba.18. Kada ma a ce murjani da duwatsu masu walƙiya; farashin hikima ya fi na lu’ulu’ai.19. Ba za a iya daidaita darajarta da duwatsun Tofaz na Kush ba, zallar zinariya ma ba tă isa ta saye ta ba.20. “To, daga ina ke nan hikima ta fito? Ina fahimta take zama?21. An ɓoye ta daga idanun kowane abu mai rai, har tsuntsayen sararin sama ma an ɓoye masu ita.22. Hallaka da mutuwa suna cewa, ‘Jita-jitarta kaɗai muke ji.’23. Allah ya gane hanyar zuwa wurinta. Shi ne kaɗai ya san inda take zama,24. Gama yana ganin iyakar duniya kuma yana ganin duk abin da yake ƙarƙashin sama.25. Lokacin da ya yi iska ya sa ta hura, ya kuma auna ruwaye.26. Lokacin da ya yi wa ruwan sama doka da kuma hanya domin walƙiya,27. sai ya dubi hikima ya auna ta; ya tabbatar da ita, ya gwada ta.28. Ya kuma ce wa mutum, ‘Tsoron Ubangiji shi ne hikima, kuma guje wa mugunta shi ne fahimi.’ ”Zabura 97:1-61. Ubangiji yana mulki, bari duniya tă yi murna; bari tsibirai masu nesa su yi farin ciki.2. Gizagizai da baƙin duhu sun kewaye shi; adalci da gaskiya su ne tushen kursiyinsa.3. Wuta tana tafiya a gabansa tana kuma cinye maƙiyansa a kowane gefe.4. Walƙiyarsa ta haskaka duniya; duniya ta gani ta kuma yi rawar jiki.5. Duwatsu sun narke kamar kakin zuma a gaban Ubangiji, a gaban Ubangijin dukan duniya.6. Sammai sun yi shelar adalcinsa, dukan mutane kuma suka ga ɗaukakarsa.Karin Magana 23:13-1413. Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.14. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.Romawa 16:1-271. Ina gabatar muku da ’yar’uwarmu Fibi, baranyar ikkilisiya a Kenkireya.2. Ina roƙonku ku karɓe ta a cikin Ubangiji yadda ya dace a karɓi tsarkaka a kuma ba ta kowane irin taimakon da take bukata daga wurinku, gama ta zama mai taimako ƙwarai ga mutane masu yawa, haɗe da ni ma.3. Ku gai da Firiskila da Akwila, abokan aikina cikin Kiristi Yesu.4. Sun yi kasai da ransu saboda ni. Ba ni kaɗai nake musu godiya ba amma har ma da dukan ikkilisiyoyin Al’ummai.5. Ku kuma gai da ikkilisiyar da take haɗuwa a gidansu. Ku gai da ƙaunataccen abokina Efenetus, wanda ya zama na farko a karɓar Kiristi a lardin Asiya.6. Ku gai da Maryamu wadda ta yi muku aiki tuƙuru.7. Ku gai da Anduronikus da Yuniyas, dangina waɗanda aka daure a kurkuku tare da ni. Su fitattu ne sosai a cikin manzanni, sun riga ni zama masu bin Kiristi.8. Ku gai da Amfiliyatus, ƙaunataccena a cikin Ubangiji.9. Ku gai da Urbanus, abokin aikinmu cikin Kiristi, da kuma ƙaunataccen abokina Sitakis.10. Ku gai da Afelles wanda amincinsa cikin Kiristi tabbatacce ne. Ku gai da iyalin gidan Aristobulus.11. Ku gai da ɗan’uwana, Hirodiyon. Ku gai da iyalin gidan Narkissus da suke cikin Ubangiji.12. Ku gai da Tiryifena da Tiryifosa, matan nan da suke aiki tuƙuru cikin Ubangiji. Ku gai da ƙaunatacciyata Fersis, wata matan da ta yi aiki tuƙuru cikin Ubangiji.13. Ku gai da Rufus zaɓaɓɓe cikin Ubangiji, da kuma mahaifiyarsa, wadda ta zama kamar mahaifiya a gare ni.14. Ku gai da Asinkiritus, Filegon, Hermes, Faturobas, Hermas da kuma ’yan’uwan da suke tare da su.15. Ku gai da Filologus, Yuliya, Nereyus da ’yar’uwarsa, da kuma Olimfas da dukan tsarkakan da suke tare da su.16. Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki. Dukan ikkilisiyoyin Kiristi suna gaishe ku.17. Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.18. Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.19. Kowa ya riga ya ji game da biyayyarku, don haka ina cike da farin ciki game da ku; amma ina so ku zama masu hikima game da abin da yake nagari, ku kuma zama marasa laifi ga abin da yake mugu.20. Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.21. Timoti, abokin aikina, yana gai da ku, haka ma Lusiyus, Yason, da Sosifater, dangina.22. Ni, Tertiyus, wanda ya rubuta wannan wasiƙa, ina gai da ku cikin Ubangiji.23. Gayus, mai masauƙina, mai kuma saukar da dukan ’yan Ikkilisiya, yana gaishe ku. Erastus, mai bi da ayyukan jama’ar gari, da kuma ɗan’uwanmu Kwartus, suna gaishe ku. Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.