Baibul a cikin shekara guda Agusta 19Ayuba 29:1-251. Ayuba ya ci gaba da jawabinsa,2. “Da ma ina nan lokacin da ya wuce baya can, kwanakin da Allah yake lura da ni,3. lokacin da fitilarsa take haske a kaina na yi tafiya cikin duhu tare da haskensa.4. Kwanakin da nake tasowa, lokacin da abokantakar Allah ta sa wa gidana albarka,5. lokacin da Maɗaukaki yana tare da ni, kuma ’ya’yana suna kewaye da ni,6. lokacin da ake zuba madara a inda nake takawa, duwatsu kuma suna ɓulɓulo mini man zaitun.7. “Sa’ad da na je ƙofar birni na zauna a bainin jama’a,8. matasan da suka gan ni sukan ja gefe tsofaffi kuma suka tashi tsaye;9. sarakuna suka yi shiru suka rufe bakunansu da hannuwansu;10. Muryar manya ta yi tsit harshensu ya manne a rufin bakunansu.11. Duk wanda ya ji ni ya yaba mini waɗanda suka gan ni kuma sun amince da ni,12. domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.13. Mutumin da yake bakin mutuwa ya sa mini albarka. Na faranta wa gwauruwa zuciya.14. Na yafa adalci ya zama suturata; gaskiya ita ce rigata da rawanina.15. Ni ne idon makafi kuma ƙafa ga guragu.16. Ni mahaifi ne ga masu bukata; na tsaya wa baƙo.17. Na karya ƙarfin mugaye na ƙwato waɗanda suke riƙe da haƙoransu.18. “Na yi tunani cewa, ‘Zan mutu a cikin gidana, kwanakina da yawa kamar turɓayar ƙasa.19. Jijiyoyina za su kai cikin ruwa, kuma raɓa za tă kwanta a rassana dukan dare.20. Ɗaukakata za tă kasance tare da ni garau, bakana koyaushe sabo ne a hannuna.’21. “Mutane suna mai da hankali su saurare ni, suna yin shiru don su ji shawarata.22. Bayan da na yi magana, ba su ƙara ce kome ba. Maganata ta shige su.23. Sukan jira ni kamar yadda ake jiran ruwan sama. Sukan sha daga cikin maganganuna kamar mai shan ruwan bazara.24. Sa’ad da na yi musu murmushi da ƙyar sukan yarda; hasken fuskata yana da daraja a gare su.25. Na zaɓar masu inda za su bi na kuma zauna kamar sarkinsu; na zauna kamar sarki a cikin rundunansu; ina nan kamar mai yi wa masu makoki ta’aziyya.Ayuba 30:1-311. “Amma yanzu suna yi mini ba’a waɗanda na girme su, waɗanda iyayensu maza ba su isa su zama karnukan kiwon garken tumakina ba.2. Ina amfani ƙarfin hannuwansu gare ni, tun da ba su da sauran kuzari?3. Duk sun rame don rashi da yunwa, suna yawo a gaigayar ƙasa a kufai da dare.4. A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi, jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.5. An kore su daga cikin mutanensu, aka yi musu ihu kamar ɓarayi.6. An sa dole su zauna a kwazazzabai da kuma cikin kogunan duwatsu da kuma cikin ramummuka cikin ƙasa.7. Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji, suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.8. Mutane marasa hankali marasa suna, an kore su daga ƙasar.9. “Yanzu kuma ’ya’yansu maza su suke yi mini ba’a cikin waƙa na zama abin banza a gare su.10. Suna ƙyamata suna guduna; suna tofa mini miyau a fuska.11. Yanzu da Allah ya kunce bakana ya ba ni wahala sun raba ni da mutuncina.12. A hannun damana ’yan tā-da-na-zaune-tsaye sun tayar; sun sa tarko a ƙafafuna, sun yi shirin hallaka ni.13. Sun ɓata mini hanyata; sun yi nasara cikin hallaka ni, ba tare da wani ya taimake su ba.14. Suka nufo ni daga kowane gefe; suka auko mini da dukan ƙarfinsu.15. Tsoro ya rufe ni; an kawar mini mutuncina kamar da iska, dukiyata ta watse kamar girgije.16. “Yanzu raina yana ƙarewa; kwanakin wahala sun kama ni.17. Dare ya huda ƙasusuwana; ina ta shan azaba ba hutawa.18. A cikin girman ikonsa Allah ya zama kamar riga a jikina; ya shaƙe ni kamar wuyan rigata.19. Ya jefa ni cikin laka, na zama ba kome ba sai ƙura da toka.20. “Na yi kuka gare ka ya Allah, amma ba ka amsa mini ba. Na tashi tsaye, amma sai ka dube ni kawai.21. Ka dube ni ba tausayi; Ka kai mini hari da ƙarfin hannunka.22. Ka ɗaga ni sama ka ɗora ni a kan iska; ka jujjuya ni cikin hadari.23. Na san za ka sauko da ni ga mutuwa zuwa wurin da kowane mai rai zai je.24. “Ba shakka ba mai ɗora hannu a kan mutumin da yake cikin wahala. Lokacin da ya yi kukan neman taimako a cikin wahalarsa.25. Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?26. Duk da haka sa’ad da nake begen abu mai kyau, mugun abu ne ya zo; Sa’ad da nake neman haske, sai duhu ya zo.27. Zuciyata ba tă daina ƙuna ba; ina fuskantar kwanakin wahala.28. Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba. Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako.29. Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi.30. Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa; jikina yana ƙuna da zazzaɓi.31. Garayata ta zama ta makoki, sarewata kuma ta zama ta kuka.Zabura 97:7-127. Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli!8. Sihiyona ta ji ta kuma yi farin ciki kuma dukan ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukunce-hukuncenka, ya Ubangiji.9. Gama kai, ya Ubangiji, kai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya; ana darjanta ka fiye da dukan alloli.10. Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.11. An haskaka haske a kan masu adalci da kuma farin ciki a kan masu gaskiya a zuciya.12. Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji, ku da kuke masu adalci, ku kuma yabi sunansa mai tsarki.Karin Magana 23:15-1615. Ɗana, in zuciyarka mai hikima ce, to, zuciyata za tă yi murna;16. cikin cikina zai yi farin ciki in leɓunanka suna maganar abin da yake daidai.1 Korintiyawa 1:1-311. Bulus, wanda aka kira domin yă zama manzon Kiristi Yesu, bisa ga nufin Allah, da kuma ɗan’uwanmu Sostenes,2. Zuwa ga ikkilisiyar Allah da take a Korint, da waɗanda aka tsarkake cikin Kiristi Yesu, aka kuma kira domin su zama masu tsarki, tare da dukan waɗanda suke ko’ina da suke kiran sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, Ubangijinsu da kuma namu.3. Alheri da salama daga Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.4. Ina gode wa Allah kullum dominku, saboda alherinsa da aka ba ku a cikin Kiristi Yesu.5. Gama a cikinsa kuka sami wadata ta kowace hanya, a cikin dukan maganarku, da kuma cikin dukan saninku6. gama shaidarmu game da Kiristi ta tabbata a cikinku.7. Saboda haka, ba ku rasa kowace baiwa ta ruhaniya ba, yayinda kuke jira da marmari, saboda bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi.8. Zai ƙarfafa ku har zuwa ƙarshe, domin ku zama marasa aibi a ranar Ubangijinmu Yesu Kiristi.9. Allah, wanda ya kira ku zuwa ga zumunci tare da Ɗansa Yesu Kiristi Ubangijinmu, shi mai aminci ne.10. Ina roƙonku ’yan’uwa, a cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, dukanku ku yarda da juna, domin kada a sami tsattsaguwa a cikinku, domin kuma ku zama ɗaya, cikakku a cikin halinku da tunaninku.11. ’Yan’uwana, waɗansu daga iyalin gidan Kulos sun gaya mini cewa, akwai faɗa a cikinku.12. Abin da nake nufi shi ne, ɗaya daga cikinku na cewa, “Ni ina bin Bulus,” wani na cewa, “Ni ina bin Afollos,” wani kuma, “Ni ina bin Kefas,” har wa yau wani kuma, “Ni ina bin Kiristi.”13. Kiristi a rabe ne? Bulus ne aka gicciye dominku? An yi muku baftisma a cikin sunan Bulus ne?14. Ina godiya domin ban yi wa wani baftisma a cikinku ba, sai dai Kirisbus da Gayus kaɗai.15. Don haka, ba wanda na iya cewa an yi muku baftisma a cikin sunana.16. (I, na kuma yi wa iyalin gidan Istifanas baftisma, ban da wannan, ban tuna da wani da na yi masa baftisma ba.)17. Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa.18. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.19. Gama a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”20. Ina mai hikima? Ina mai zurfin bincike? Ina masana na wannan zamani? Ashe, Allah bai wofinta hikimar duniya ba?21. Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara.22. Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima,23. amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai,24. amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah.25. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.26. ’Yan’uwa, ku tuna yadda kuke sa’ad da aka kira ku. Babu masu hikima da yawa a cikinku, bisa ga ganin mutum; babu masu iko da yawa, babu masu martaba da yawa bisa ga haihuwa.27. Amma Allah ya zaɓi abubuwa masu wautata duniya, don yă kunyata masu hikima. Allah ya zaɓi abubuwa marasa ƙarfi na duniya, domin ya ba wa masu ƙarfi kunya.28. Ya zaɓi abubuwa marasa martaba na wannan duniya da kuma abubuwan da aka rena da abubuwan da ba a ɗauka a bakin kome ba, domin a wofinta abubuwan da ake ganinsu da daraja,29. domin kada wani ya yi taƙama a gabansa.30. Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.31. Saboda haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Duk wanda yake taƙama, ya yi taƙama a cikin Ubangiji.” Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide.